Wani lokaci ne ake yi wa mamaci sadaka da kuma abubuwan da ake yi a waɗannan lokutan bisa ga al’adar Hausawa ta gargajiya?
Mutuwa wani al’amari ne na dindindin, wanda ba a iya maido shi baya har abada lokacin da rayuwa ta tsaya (ƙare), ga duk wata halitta wadda ke rayuwa. Ana amfani da kalmar mutuwa da kuma rashin iya yin aiki na ƙwaƙwalwa na dindindin a matsayin ma’anar mutuwa a hukunce. Mutuwa aba ce da babu makawa, tsari ne na rayuwar duniya wanda daga ƙarshe yake faruwa ga dukkan wani abu mai rai.
Sai dai me yake biyo bayan mutuwa ga mamaci a fannin sadakar da za a yi masa?
A musulunci ba a ware wani lokaci da ya kamata a ce an yi wa mamaci sadaka ba, saboda yadda ake yin sadakar uku, da bakwai, da arba’in, duk ba su da tushe a addini da hadisan Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama.
Wannan al’ada ce ba ibada ba, idan za a yi sadaka sai an tara jama’a ba.
Shi mamaci duk abin da ka yi masa ladan zai isa gare shi, ko addu’a ko sadaka.
Za ka iya yin abinci ka raba sadaka da niyyar Allah Ya kai wa mamacin ladan, ko kuma idan kana da gona ka bayar da ita ga miskinai su kwashe abincin ciki a matsayin sadaka ga mamaci, ko kuma ka yi sadaqatul jariya ka gina rijiyoyin burtsatsai ko masallacin da za a dinga sallah, ko gida da baƙi za su dinga sauka. Sai dai a yi hankali ba a taɓa dukiyar marayu ƙanana a yayin yin sadaka. Don haka kowace rana ana iya yin sadaka ba a ware wasu ranaku na uku da bakwai da arba’in a matsayin lallai su ne ranakun da za a yi wa mamaci sadaka ba.
Sai dai kuma akwai wasu ayyukan Ibada guda biyar da ka iya amfanar mamaci a musulunci, har su zame masa kamar sadaka.
Hadisan Manzon Allah (SAW) sun bayyana cewa akwai wasu ayyukan da ka iya amfanar musulmi har bayan mutuwarsa.
1. Sallar jana’izar da ake yi masa: Ɗaya daga cikin abubuwan da ke amfanar mamaci shi ne sallar jana’izar da ake masa. Abdullahi Ibn Abbas ya ruwaito cewa: “Na ji Manzon Allah (SAW) ya ce: Idan musulmi ya mutu kuma mutane 40 marasa shirka ga Allah suka tsaya a kan gawarsa. Allah zai ba su cetonsa.” [Sunan Abu Dawud 3170]
2. Sadaqatul Jariyar da ya gabatar lokacin rayuwarsa: Daga cikin abubuwa masu muhimmanci da za su amfani mamaci musulmi shi ne Sadaqatul Jariya da ya gabatar lokacin da yake rayuwa. Misalan Sadaqatul Jariyan da musulmi zai iya amfana da su su ne, ginin masallaci, makarantar addini, gidan marayu, rijiya ko burtsatsan ruwan sha ga mabuƙata, da sauran su. Abdullah bin Abu Qatadah ya ruwaito cewa, mahaifinsa ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, abu mafi kyawu da mutum zai barin ma kansa uku ne: Dan kirkin da ke yi masa addu’a, Sadaqatul Jariya da ke gudana, da ilmin da ya amfanar da mutane da shi.” [Sunan Ibn Majah, 1/242]
3. Sadaqah da addu’oin da yaran mamacin suka yi masa: Addu’o’in yaran da mutum ya bari a baya na isar masa saboda irin tarbiyyar da ya yi musu na samun ilmi. Ummuna Aisha ta ce: Wani mutum ya fada wa Manzon Allah (SAW) cewa, “Mahaifiyata ta mutu, kuma ina tunanin da za ta iya magana, da ta yi sadaqa, shin zan iya Sadaqa a madadinta?” Manzon Allah (SAW) ya ce “Na’am, yi sadaqa a madadin ta.” [Sahih al-Bukhari 2760]
4. Biyan basukan mamaci da cika alƙawuran da mamacin ya yi. Hadisin Abdullahi ibn Abbas ya ce: Wata mata daga kabilar Juhaina ta zo wajen Manzon Allah (SAW) kuma ta ce, “Mahaifiyata ta yi alwashin yin aikin Hajji, amma ta mutu kafin yi, shin zan iya yi a madadin ta?” Manzon Allah (SAW) ya ce, “Yi Hajji a madadin ta, shin da akwai ba shi a kanta, za ka biya ko ba za ka biya ba? Saboda haka, bashin Allah ya fi cancanta a biya.” [Sahih Bukhari 1852]
5. Ilmin da ya azurta mutane da shi lokacin da yake rayuwa.
WALLAHI TA’ALA A’ALAM.