Tsakanin marubuci da darakta wanne ya fi yin kokari wajen samar da fim?
Kafin in bayyana ra’ayina a kan wanda ya kamata a jinjina mawa a tsakanin Marubuci da kuma Director, yana da kyau mu fara sanin matsayin kowannen su:
MARUBUCI: Shi ne wanda yake ƙirƙirar labari, ya kuma tsara shi ta fuskar da labarin zai bada ma’ana a ƙarƙashin jigon da aka gina labarin.
DIRECTOR: Shi ne wanda ya ke ɗora jaruman film a kan tsarin da zasu aiwatar da wasan kwaikwayon da aka gina a ƙarƙashin wani jigo, ta yadda wasan zai fito a kan tsarin da zai ƙayatar da masu kallo.
Dukkanin waɗannan haziƙan mutane suna bada gudummawa wurin samuwar Film, toh amma dole ɗaya ya fi ɗaya. A iya fahimtata, ina ganin marubuci ya fi Director ƙoƙari wurin samar da Film, domin marubuci shi ne ya fara gina foundation na film ɗin, zan iya cewa idan marubuci bai rubuta labari ba, toh Director ma ba zai iya directing ɗin ba, sannan kowane marubuci zai iya zama Director, amma ba kowane Director ne zai iya zama marubucin ba. Don haka marubuci ya fi Director taka rawa a harkar Film.
Duk da shima Director ɗin yana ƙoƙari, toh amma ba za a haɗa shi ba da na marubuci. Wannan shi ne ra’ayina.