Ina bukatar a fayyace mini banbanci tsakanin hukumar NITDA da kuma NCC
BAMBANCI TSAKANIN HUKUMAR NITDA DA KUMA NCC:
Rubutawa: Hassana Labaran Ɗanlarabawa.
Idan muka yi duba da cewa waɗannan hukumomi an yanke musu cibiya ne daga Federal Ministry Of Communication, Innovation and Digital Economy, wato hukumar National Information Technology Development Agency (NITDA), da Nigeria Communications Commission (NCC). Sai dai akwai bambanci a tsakanin ayyukan da hukumomin suke gudanarwa kamar haka;
GAME DA NITDA:
Mu sani cewa gwamnatin Nigeria ta ƙirƙiri NITDA ne don taimakawa wajen bincike, da ƙirƙira, da kuma ba da shawararwari ga gwamnati ta yadda za ta samarwa da ƙasa cigaba, amfani da na’ura mai ƙwaƙwalwa domin ci gaba a kowane ɓangare na rayuwar yau da kullum. Haka nan; hukumar NITDA tana yin wasu ayyuka domin horar da wasu al’umma kan wasu abubuwa masu muhimmanci. Misali, A jihar Jigawa, hukumar NITDA ta taɓa horar da ‘yan jarida su hamsin ilimin da za su dinga gano sahihancin labarai. Hakan ya samu a ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi.
Mahangar Arewa ta ruwaito cewar horon na tsawon yini biyu, wanda hukumar NITDA ta ɗauki nauyi, wasu kamfanonin sadarwa ne suka gabatar da horon, waɗanda suka haɗa da;
a) Image Marchant Promotions Limited (IMPR) Masu wallafa mujallar PRNigeria.
b) Economic Confidential Magazine.
c) Penlight Centre for New Media Innovation.
Wannan kaɗan ne daga cikin ayyukan da hukumar NITDA take gudanarwa.
GAME DA NCC:
Idan muka mayar da kallonmu kan hukumar NCC za mu ga cewar an ƙirƙire ta ne domin kula da duk wasu abubuwa da suka shafi sadarwa a Nigeria, kamar misalin kamfanonin telephone, gidaje, radio, da abin da ya danganci hakan. Haka nan kuma, NCC ce ke kula da yadda suke tafiyar da ayyukansu ta yadda zai yi kafaɗa da ƙuduri ko manufofin gwamnatin Nigeria har ma ya amfani al’ummar ƙasar Nigeria ɗin. Dangane da haka akwai ayyuka da hukumar NCC take gudanarwa, wasu na ƙashin kanta wasu kuma haɗin gwiwa. Idan muka yi duba da dokar aikata miyagun laifuffuka ta hanyar yanar gizo-gizo, da kuma abubuwan da dokar ta wajabta a kan ma’aikatun hada-hadar kuɗaɗe da masu samar da sabis. A ranar Litinin, 4 Ga watan Janairu, 2021. Bashir Abdullahi El-bash ya rubuta maƙala game da miyagun laifuffukan da ake aikatawa ta hanyar yin amfani da kimiyyar fasahar na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer) wato (Cyber Crime). Inda ake yin kutse cikin bayanan sirri na wani mutum ko wasu mutane ko wasu ma’aikatu da hukumomim gwamnati da ‘yan kasuwa ko ƙungiyoyi domin kwashe musu kuɗaɗe ko naɗar wasu muhimman bayanansu na sirri. Matsalar da ta addabi duniya a wannan zamani. Har a ƙarshen maƙalar ya kawo ayyukan da suke kan masu samar da sabis shi ne bibiya da naɗar bayanan ayyukan da aka yi da sabis din da suka samar, wanda hakan ya samu ne haɗe da haɗin gwiwar hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) da kuma tabbatar da yi wa layukan wayar salula rijista, kamar yadda hakan yake ƙunshe cikin dokar ta (NCC). Duba da yadda ake cigaba da samun ƙaruwar matsalolin aikata laifuffuka ta computer, haƙiƙa wannan tsarin doka ne mai matuƙar muhimmanci wanda zai taimaka wajen samun tsaron dukiya da na rayukan al’umma a ƙasa gaba ɗaya. Tun da farko wannan doka ta tanadar da cewa wajibi ne kamfanonin da ke samar da sabis ɗin yin amfani da computer su dinga kiyaye bayanan masu amfani da sabis ɗin ta yadda hakan zai taimaka ƙwarai da gaske wajen gano masu aikata laifin kutse cikin bayanan sirrin al’umma da kamfanoni, da sassan ma’aikatu da hukumomin gwamnati da wuraren cinikayya.
Wannan kaɗan ne daga cikin ayyukan da hukumar NCC take gudanarwa.
ƊAURAYA:
A taƙaicen taƙaitawa, wannan shi ne bambancin da yake tsakanin waɗannan hukumomi guda biyu da wasu suke wa kallon abu guda, har ma da tagomashin kaɗan daga cikin irin ayyukan da suke gudanarwa. Muna fatan kwalliya za ta biya kuɗin sabulu dangane da fuskantar waɗannan bayanan daki-daki.
Mun gode.