Ina bukatar a fayyace mini banbanci tsakanin hukumar NITDA da kuma NCC
Da farko dai, dukka NCC (Nigeria Communications Commission) da NITDA (National Information Technology Development Agency), wasu bangarori ne, wato agencies na Federal Ministry of Communication, Innovation and Digital Economy. An kirki NCC ne a shekarar 1992, ita kuma NITDA an samar da ita ne a 2001.
Wasu daga cikin agencies na ministry din sun hada da NDPC (Nigeria Data Protection Commission), NIPOST (Nigeria Postal Service), NIGCOMSAT (Nigeria Communications Satellite Limited) da kuma Galaxy Backbone.
An kirkiri NCC ne kacokam don kula da duk wani abu da ya shafi sadarwa, wato telecommunications, a Nigeria, misali gidaje da kamfanonin telephone, radiyo da makamantansu. NCC ce ke kula da yadda suke gudanar da aikinsu ta yadda zai yi daidai da kudurorin gwamnatin Nigeria, kuma ya amfani yan kasa.
Ci gaba da duniya ke ta samu a bangarorin information technology, wato IT, ya sa gwamnatin Nigeria ta kirkiri NITDA don taimakawa wajen bincike, kirkire-kirkire da bada shawarwari ga gwamnati ta yadda za ta samarwa kasa ci gaba ta hanyar IT, kamar su e-government, amfani da na’ura mai kwakwalwa a kowane sashe na rayuwa da ci gaba.
Kasancewar IT ya shafi duk wani na’urar technology shi ya sa ayyukan hukumar NITDA ke shiga ayyukan hukumar NCC. Misali babu ruwan NCC da abinda ya shfi amfani da na’ura mai kwakwalwa a bankuna don inganta aiki, to amma ya shafi NITDA saboda zai taimaka wajen inganta ci gaban kasa ta hanyar amfani da technology.
Wannan shi ne dan takaitaccen bayani da muka samo game da banbancin NCC da NITDA.
Watakila wani member a nan ya kara samo maka karin bayani.
Yauwa madalla, muma mun gode.
Madalla. Ni ma na gamsu da wannan amsa sosai. Fatan alheri.
Na gamsu sosai, ina mai matukar godiya.