Cikakkiyar ma’anar iba da ce “Dukkan abin da Allah yake so, kuma ya yarda da shi, na daga magana ko aiki, kamar sallah da Zakka…”
Ma’ana, Ibada Umurni ne na Ubangiji Madaukakin Sarki, aiwatar da ita kuma biyayya ce ga a gare Shi. Sannan Ibada bata ingantuwa har sai bawa ya san Allahn da ya ke yi ma ita, kamar yadda Allah ya faɗa a cikin Hadisul Ƙudusi, inda ya ce “Ku san nni, kafin ku bauta Mani. Idan baku san Ni ba, ta ya za ku bauta Mani.?”
Don haka sanin Ubangiji wajibi ne ga mai yin bauta, bauta kuma ita ce ibadar.
Misalan Ibada suna da yawa, Manya-manya daga ciki akwai Sallah, Zakka, azumi, aikin Hajji, dukkaninsu Manyan Ibadu ne.
Sannan daga cikin nau’ukan ibada akwai:
Farilla:- ita ce Ibadar da Allah ya sanya ta zama dole ga bayinsa, wadda babu fashi a cikinta, sai idan wani uzuri ya zo, kuma duk da wannan uzurin akwai abin da zai zo a madadinta. Misalinta akwai Sallah, azumi, Zakka, aikin hajji.
Sunna:- Ita ce Ibadar da ba wajibi ba, amma tana da ɗimbin lada tare da ƙara darajar mai yawan yin ta. A wani ɓangaren ma har taimakon bawa take a cikin farillarsa, yayin da ya samu naƙasu. Misalanta akwai azumin Litinin da Alhamis, sallolin nafila, sadaƙa d.s.
Sannan Salatin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama Ibada ce, karatun Alkur’ani Ibada ce, ambaton Allah ibada ce, biyayya ga iyaye ibada ce, nisantar haram Ibada ce. A taƙaice dai duk wani abu da Allah ke so, na magana ko aiki sunansa Ibada.
Sannan Ibada bata yiwuwa da ka, dole sai mutum ya yi koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama gwargwadon iyawarsa.
Idan mutum ya ce zai yi ibada da ka, toh kuwa tamkar yana wahalar da kansa ne.
Don haka neman ilimin yadda zamu yi Ibada yake wajibi, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce “Neman ilimi farilla ne, ko da a birnin ɗin ne.”
Ingata Ibada tare da yawaita ta na sa bawa ya samu kusanci da Ubangijinsa, wanda yake kusa da Ubangiji kuma haƙiƙa ya na tare da dukkan Alkhairi.
Wulakanta Ibada kuwa yana sa bawa yin asara tare da taɓewar duniya da lahira, don haka sai mu dage, domin musababbin halittar mu kenan, kamar yadda Allah ya faɗa a cikin Littafinsa Mai Tsarki “Ban halicci Mutum da Aljani ba sai don su bauta Mani.”
Da fatan Allah ya datar da mu Amiin.