Hukumomin lafiya a kowane mataki sun duƙufa haiƙan wajen ganin iyaye mata sun karɓi tsarin ba wa jarirai zallar nono har tsawon watanni shida, shin me ya sa ake son hakan kuma wane alfanu hakan ke da shi ga yaran da kuma iyayen?
MUHIMMANCIN SHAYAR DA YARO NONON UWA ZALLA (Exclusive Breast Feeding)
Yayin da mace ta haihu an fi so ta shayar da jaririnta zallar nonon har na tsawon watanni shida na farko daga haihuwar jaririn, ba tare da an haɗa da komai ba. Sannan za a ci gaba da bada nonon haɗe da abinci har zuwa jaririn ya kai shekaru biyu a duniya.
Dalilin masana kiwon lafiya dangane da wannan tsarin shi ne: Nonon uwa na ɗauke da ruwa, har ana ganin ruwan ma na da rinjaye sosai a cikin Nonon, wanda baya buƙatar a ƙara masa wasu ruwan na daban. Sannan akwai ingantaccen abinci mai gina jiki a cikinsa, da kuma abinci mai ƙara kuzari. Sannan har ila yau a cikin nonon akwai sinadarai masu kare jiki daga kamuwa da cutuka, waɗanda suka haɗa da Vitamins da Minerals.
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) da sauran kungiyoyin lafiya, da ma dukkanin ma’aikatan lafiya na duniya sun tabbatar nonon uwa shi kaɗai ne zai iya rike jariri har zuwa watanni shida tare da gadar masa da duk wasu matakan girman jiki da lafiya, don haka a tsawon wannan lokacin babu buƙatar shayar da shi ko ciyar da shi wani nau’in abinci.
Kadan daga cikin amfanin shayar da jariri nonon uwa zalla :
1- Yana Kara musu basira.
2- Yana Kara musu garkuwan jiki.
3- Yana kare su daga cututtuka.
4- Yana Kara musu Ilmi.
5- Yana Hana yaro mummunar Kiba da mummunar ramewa.
6- Yana Kara soyayya tsakanin uwa da da.
7- Yana dauke da dukkan nau’in abinci da jariri sabuwar haihuwa yake bukata.
8- Yana kare uwa daga kamuwa da ciwon jeji da kuma raunin ƙashi a karshen rayuwar ta.
9- Yana taimakawa wajan tsaida jinin haihuwa.
10- Yana taimakawa wajan hana ɗaukar ciki. Don haka duk mai buƙatar ɗanta ya samu ingantacciyar lafiya, sai ta gwada wan
nan tsarin.