Shin karatun ɗa namiji ne ya fi muhimmanci ko karatun ‘ya mace?
MUHIMMANCIN ILIMI GA MATA YA FI NA MAZA
Hakika ilimin ‘ya mace na da muhimmanci kwarai. Don haka ne a ke cewa idan ka ilmantar da ya mace to ka ilmantar da al’umma. A wannan takaitaccen makala zan dan tattauna ne akan muhimmancin karatun diya mace, kuma karatu mai zurfi na boko da na islamiyya.
Duba fa’idar ilimi wajen samun nagartacciyar al’umma .
Yana da matukar muhimmanci mata mu yi karatu. Ya zama wajibi kuma farilla ne a kanmu mu dalilin kuwa Hadithin nan na Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi wanda ya ke cewa,
‘Dalabul ilmu faridatun ala kulli muslimin wa muslimatin,’ wato neman ilimi farilla ne ga dukkan musulmi na miji ne ko mace.
Sai kuma har’ila yau, Hadithin da yake cewa, “Idlubul ilma walau fissin,’ watau a nemi ilimi ko da a kasar Sin ne. Dubi tazaran da ke tsakanin Makka da Sin, amma a ka wajabta wa mutum. Wannan lallai ya nu nuni ne da muhimmancin ilimi. Har’ila yau kuma a dubu muhimmancinsa ga ya mace.
1. Mace mai ilimi itace za ta san yadda zata tafiyar da gidanta da kyau in tana da hankali
Ilimi haske ne rashin ilimi, watau jahilci kuma, duhu ne
2. In mace jahila ce ba na addinin ba na boko yaya ake tunanin zata tada yaranta da kyau a zamanin mu na yanzu?
3. Mace itace uwa, ita zata sa yaranta akan hanya, har shi mijinta dakansa ita ta kan koya masa dabi’u masu kyau.fiye da ɗa na miji In kuwa bata da ilimi, bata san abinda yakamata ta na iya zama masa da yayansu makauniyar jagora.
4. Turawa ma sun ce duk namijin da ka ga ya yi nasara a rayuwarsa, to akwai mace bayansa – ko uwarsa ko matarsa.
5. Ilimi ke sanya mace ta san yadda za ta tafiyar da kanta a kowane irin hali. Za ta zama wayayyiya mai basira.
Saboda haka yanzu kowani namiji ya gane bai son auren jahila.Kowa yana son yaga yaransa sun zame masa abin alfakhari. Haka kuma zai samu ne idan mace na da ilimi.
Kuma karatu baya tsufa, ko kuwa mutum baya tsufa ya ce ya wuce lokacin karatu. Karatu na farawa ne daga haihuwa har zuwa mutuwa.