Da aboki da ɗan uwa wanne yafi muhimmanci a rayuwa?
Ya danganta da yadda halayensu suke, da kuma mu’amalarsu, kowanne yana iya zama mafi muhimmanci ko akasin haka. Akwai abokin da zai kasance mafi muhimmanci a kan ɗan’uwa musamman idan ya kasance na kirki ne mai taimakon ka da ɗora ka a turbar daidai, wanda zamanka da shi zai sa ka ƙaru a addininka, ko ka ƙaru da ilimi, ko aikin ƙwarai da ake yi, ko a rayuwar yau da kullum. Irin wannan abokin ya kan zarta ɗan’uwan da bai mu’amalance ka da hakan ba.
Akwai kuma ɗan’uwan da zai iya zarta aboki muhimmanci, musamman idan ya kasance ya ɗamfaru da irin waɗancan sifofi na abokin ƙwarai, to yakan fi mugun aboki muhimmanci, wanda a kullum ya kamata ka nisance shi, ka datse igiyar alaƙa da shi, idan kuwa babu yadda ka iya da shi, to sai ka san dabarar zama da shi.
Ɗan uwa daban, aboki daban, kowane da irin role ɗin da yake playing, sannan a hakan kowane zai iya hawa role ɗin ɗayan
Hausawa na cewa ‘Ɗan’uwa rigar ƙaya’ wanda hakan ke nufin in babu shi sai dai ka tafi tsirara kenan, in kuma ka saka shi to ya dinga sukarka kenan. Shi aboki dama yake baka na ka rayu cikin farincikin da ba lallai bane ɗan’uwan ya ba ka shi, shi kuwa ɗan’uwa jininka ne ko ka so yadda shi ba zai yadu ba.