Tsakanin exchangers na cryptocurrency wato Bybit, Binance da Bitget wanne ya fi daɗin mu’amala?
Binance, Bybit da kuma Bitget dukkansu (Centralise Exchangers) ne, wato Exchangers da ake hada-hadar kasunwanci na crypto currency a fili, ba kamar Decentralise Exchangers ba, waɗanda su mutum zai yi kasuwancinsa na crypto ba tare da mai saye da sayarwa sun san juna ko kuma alaƙa da juna ba.
Duka waɗannan Exchangers guda uku suna da Higher Trading Volume, wanda yake nufin yawan cinikayya a kasuwar Crypto currency.
Sannan suna da tsaro sosai, kasantuwar kasunwaci ne da ake a bainar jama’a. Tun kafin ka shigo kasuwa sai an tantace ka, an san waye kai da kuma inda ka fito (KYC), shi ya sa ba a cika samun matsala a waɗannan Exchangers ɗin ba, saɓanin Decentralise Exchangers, waɗanda ba wanda ya san wani, ko a wurin registration kai kaɗai ke da security phrases ɗinka, da zaran ka rasa su, toh ka rasa dukiyarka.
Wadda ta fi a cikin waɗannan Exchangers ɗin kuma ita ce Binance, ta fi su Security, sannan ta fi su Higher Trading volume, domin ita world wide Exchanger ce. Sannan Binance ba kowane coin ne take listing ba, a can baya bata yin listing na memecoins marasa usecase kamar irin su (Dogs, Notcoin , Hamster), sai dai masu Usecase irin su (Bitcoin, Ethereum d.s), yanzu ne ma suke ɗan yi, saboda sun fahimci da Memecoins ɗin ne ake samun kuɗi a kasuwar crypto, shi ma ba kowanne ne suke yi ba, saboda manyan Traders na duniya sun fi yawa a can, kuma su ba irin waɗannan shitcoins ɗin ne a gabansu ba.
Sannan ta fi su sauƙin mu’ala a wurin cire kuɗi, internal ko external transfer ne mutum zai yi, sannan da wahala mutum ya yi asarar kuɗinsa a nan.
A matsayina na wadda ta ke amfani da dukkansu, zan iya cewa Bybit ce Number ta biyu, duk da tana da matsaloli masu yawa. Sai kuma Bitget zata zo a Number ta uku.
Amma dukkansu Centralise Exchangers ne masu daɗin mu’amala ga wanda yake hulɗa da su.