A cikin al’adun aure Akwai wani aure da ake kira auren sadaka, yaya ake gudanar da shi?
Auren sadaka na cikin nau’aukan aurarrakin da hausawa ke yi, wanda suka haɗa da auren soyayya, auren dole, auren kisan wuta da sauransu. Sannan aure ne da salonsa ya sha banban da waɗancan aurarrakin na hausawa, domin kuwa amarya da angon basu taɓa sanin junansu ba, idan ma sun san juna, toh ba sa taɓa sa ran zasu zama ma’aurata. Yadda yake kasancewa kuma shi ne:
A lokacin da yarinya ta kai minzalin aure, mahaifinta zai fara shiri ne tare da sanar da ita da duk wani mai haƙƙi, amma ba zata san waye zata aura ba, kamar yadda shi ma angon ba lallai ne ya san za a ba shi mata ba bare ya shirya. Idan an gama duk wani shiri da ya kamata, sai a fidda ranar ɗaurin aure, idan ta zo, a wurin ɗaurin auren ne Mahaifin amarya zai ce toh ya ba da ƴarshi wance ga wane, wani angon a matsayin wanda aka gayyata ya zo, amma ƙarshe ya tafi da aure a kansa. Ita kuma amarya ya rage nata, ko tana so, ko bata so, an dai riga an ɗaura.
Irin wannan auren ya faru ne a can baya kafin wayewar ilimin addini ta cika mutane, duk da a yanzu ma ba a rasa waɗanda basa yi ba, amma ba sosai ba.
Sannan gaskiya yana da matuƙar illah, domin ni dai duk wanda na ga an yi, ba a ƙare lafiya ba, don kuwa saki ne ya biyo baya, don haka yin sa bai cika fa’ida ba. Wasu kuma a kan yi dace idan an yi a zauna lafiya.
Muna fatan Allah ya yi mana zaɓin aure na gari Amiiiiin.