Ruwa ne ya fi muhimmanci a rayuwar ɗan’adam ko wuta?
Kacokam rayuwar ɗan adam ta ta’allaƙe ne a ƙarƙashin wuta da ruwa, domin idan babu ɗaya daga cikinsu, da wahala rayuwar ta yi masa daɗi yadda ya kamata, don haka idan so samu ne, toh ace ya mallake su duka.
Sai dai duk da muhimmancinsu, toh ba za a rasa wanda ya fi a cikinsu ba, domin zai iya yin aikin da ko da ba ɗayan, toh rayuwa zata yi sauƙi ga ɗan adam.
Hausawa suka ce “Ra’ayi riga, kowa da irin ta sa”, don haka a ra’ayina shi ne, ruwa ya fi muhimmanci fiye da wuta ga rayuwar ɗan adam, dalilina na faɗin haka kuwa, kaf rayuwa ma baza yiyu ba idan ba ruwa, tunda daga buƙatuwar gangar jiki, da sauran mu’amaloli.
Bari in fara buga misalina na farko da ƙishirwa, duk abu mai rai ya san irin zafin da ƙishirwa take da shi, wanda duk rintsi ruwa ne kaɗai zai iya maganinta, ruwan kuma wand baya da sirki da wuta, ma’ana ba mai zafi ba, kun ga kuwa duk da muhimmancin wuta, akwai inda idan ta haɗu da ruwa zata yi illa ga amfanin da ruwan zai yi, domin ruwa mai zafi baya maganin ƙishirwa.
Sannan ta ɓangarori da dama ita kanta wutar ba zata yi amfani ita kaɗai ba, sai da ruwa, domin har idan ta kama za’a yi girki, toh ba za ‘a ɗauko abinci a bushe a ɗaura a wuta ba, don zai ƙone, har sai idan an sanya ruwa ne wutar zata iya yin aikinta yadda ya kamata, kun ga ta nan ruwa ya zama babban mataimaki ga wuta.
Idan mutum na rashin lafiya, babu inda ake cewa ya rasa wutar jikinshi, sai dai a ce ya rasa ruwan jikinsa, ba zai samu lafiya ba kuma har sai ya maida wannan ruwa da ya rasa, domin rayuwar ɗan adam bata tafiya sai da ruwa.
Idan muka dawo a ɓangaren noma, idan ba ruwa ta ina zamu yi noma da kiwon dabbobinmu? Wuta dai idan ba illa ba, babu abin da zata iya yi ma wannan ɓangaren. Sannan akwai nau ukan abincin da ko ba wuta zamu iya cinsu, kuma mu rayu, kamar ƴaƴan itace da sauransu.
Don haka ruwa ya fi wuta muhimmanci ta kowane ɓangare, duk da itama tana da nata muhimmancin, kuma idan so samu ne, toh mutum ya mallaki wuta da ruwa, idan kuma an ce ya zaɓi ɗaya, toh ni dai ruwa na zaɓa.
Ma sha Allah! Amsa ta fita fes.