Ma’anar taimama a harshen Larabci, shi ne: Nufi da dogara.
Ma’anar ta a Shari’ah kuma: Shafar fuska da hannuwa da turbaya mai tsarki akan a siffa kebantacciya. Kuma yana daga cikin abin da Allah ya kebanci wannan al’umma da shi, wato madadin amfani da ruwa.
YADDA AKE YIN TAIMAMA:
1. Yin Niyya.
2. Dukan (bugun) Kasa da tafunan hannaye; na farko.
3. Shafar fuska da tafukan hannayen, faruwa daga maɓuɓɓugar gashi (saman goshi), zuwa karshen hanci.
4. Dukan (bugun) Kasa da tafukan hannaye; na biyu.
5. Shafar wajen hannun dama da cikin hannun hagu.
6. Shafar wajen hannun hagu da cikin hannun dama.
ABIN DA AKE TAIMAMA DA SHI:
1. Fuskar Kasa (Turbaya, Dutse.)
2. Simenti, Bulo.
3. Ba a yin Taimama da Ƙanƙara (ta ruwa)
4. Dole abin da za a taimama da shi ya zama mai tsarki.
ABIN DA KE SA A YI TAIMAMA:
1. Rashin ruwa.
2. Ka sa amfani da ruwa; saboda rashin lafiya.
3. Ƙarancin ruwan da zai kai, misali a dinga jin tsoron fada wa cikin ƙishi idan an yi Al-wala da ruwan.
4. Ƙarancin ruwan da zai sa; sai dai a zaba tsakanin kawar da najasa ko Al-wala.
5. Ƙarancin lokacin zai sa; kafin a yi Al-wala lokacin Sallah zai iya fita.
HUKUNCE-HUKUNCEN TAIMAMA:
1. Taimama a madadin Al-wala iri daya ce da Taimama a madadin Wanka.
2. Abin da ke ɓata Al-wala da Wanka yana ɓata Taimama (misali: Fitsari, Janaba.)
3. Taimama ba ta inganta sai akwai uzurin da ke sa a yi ta.
4. Wanda ya yi Taimama a madadin Wankan Janaba; zai iya yin Sallah da ita, amma wanda ya yi Taimama a madadin wani wankan da ba na Janaba ba; to sai ya yi Al-wala ko ya yi Taimama biyu.
5. Wajibi ne Jerantawa da Gaggautawa.
FARILLAN TAIMAMA:
1. Niyya.
2. Wuri mai tsarki.
3. Bugu na farko.
4. Shafar fuska da tafukan hannuwa.
SUNNONIN TAIMAMA:
1. Bismillah. ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ
2. Fuskantar alkibila.
3. Ta kasance a yi ta a lokacin da za a yi sallah.
4. Bugun kasa na biyu.
5. Jerantawa.
6. Tsattsefe yatsun hannu.
ABUBUWAN DA KE WARWARE TAIMAMA:
1. Samun ruwa.
2. Abubuwan da ke warware alwala da wanka to suna warware taimama, domin ita taimama abar musanyawar su ce, kuma abin da ya warware na asali (wato alwala da wanka) to yana warware na biye da shi.
TAIMAMA GA MAI ƊAURI KO CIWO:
Duk wanda akwai karaya ko ciwo ko ƙurji a jikinsa, kuma yana tsoron cutuwa idan ya wanke wajen da ruwa, ko kuma zai sa shi damuwa idan ya shafa, to sai ya yi taimama bayan haka sai ya wanke sauran. Duk wanda ya rasa ruwa ko turbaya a kowane hali to sai ya yi sallah gwargwadon halin kuma ba zai sake ta ba.
WALLAHU TA’ALA A’ALAM.