A ba mu misalan hanyoyin gane masoyi nagari.
Ganen masoyin gaskiya, ko masoyi na gari sai Allah, domin sau da yawa wanda muke ma kallon masoyi, ya kan rikiɗe ya zama babban maƙiyi, har mukan yi mamakin ya hakan take kasancewa.
Sai dai siffofin da suke sa a kyautata ma mutum zaton masoyin gaskiya ne suna da yawa, amma ga kaɗan daga ciki:
Masoyin gaskiya na son masoyinsa a duk yadda yake, ma’ana ko da yana da wata siffa wadda ta sha banban da ta game-garin mutane, toh zai so shi a wannan siffar. An sha samun mutum mai lalurar kurumta, ko makanta, ko kuma wata naƙasa dai, amma a samu wata ta ce idan ba shi ba sai rijiya.
Masoyin gaskiya ba ruwansa da arziki ko talauci, zai so masoyinsa a halin akwai da kuma halin rashi, don kuwa an sha samun ƴar ko ɗan masu kuɗi sun liƙe ma talaka, har mutane su riƙa faɗin me wane zai yi da wance? Shi ya ko ita sun san me zasu yi da juna, tunda shi so gamon jini ne.
Masoyin gaskiya yana kula masoyinsa, duk rintsi ya kan samu lokacin da yake ba masoyinsa kulawa ko da kaɗan ce. Masoyin gaskiya baya rowar kulawa ga masoyinsa.
Kyauta ko kuma in ce Ihsani, suna cikin jerin abubuwan da ke jaddada soyayyar gaskiya, tunda an ce “Sadakin so, tukuici.” Duk da ita kyauta hali ce, wani ko ba soyayya a tsakaninku zai iya yi maka kayauta. Toh amma dai masoyin gaskiya ko yaya ne yana yin kyauta ga wanda yake so, ko da bai da halin kyauta.
Aure: Babban burin masoyin gaskiya shi ne ya mallaki wanda yake so a matsayin abokin rayuwa ta har abada, domin da wannan ne zai samu damar nuna soyayyar sa yadda ya kamata, don haka duk wanda bai son ka ba zai so mallakar ka ba, bare har ya iya rayuwa da kai.
Ƙaɗan kenan daga cikin siffofin masoyi na gaskiya, da fatan Allah ya haɗa mu da masoya na gari, masu ƙaunar mu domin Allah Amiiiin.