Zuciya da ƙoda gaɓoɓi ne masu muhimmanci guda biyu a jikin ɗan’adam. Suna aiki tare don kiyayewa da tabbatar da lafiyar jiki. Lokacin da ɗaya ya kamu da cuta, ɗayan ma zai iya harbuwa.
Babban aikin zuciya shi ne aikawa da jini mai cike da iskar oxygen zuwa ga dukkan sassan jikinka, wanda da jinin ne suke iya aiki. Wannan yana nuna cewa idan ba tare da zuciya ba, ƙoda ba za ta sami jinin da ke cike da iskar oxygen ɗin da ake buƙata don yin aikace-aikace masu mahimmanci ba. Ita ko ƙoda aikinta shi ne tsaftace jini, cire datti da ruwa gurɓatacce. Idan ba tare da ƙoda ba, jini ba zai sami tatuwa ba. Zuciya za ta kasance tana aiki haiƙan mai yawa wanda hakan zai iya haifar da matsalolin lafiya.
Duba da yadda jini ya jibanci muhimman sassan na ɗan’adam guda biyu, shin ko yaya dangantakarsu za ta kasance a ɓangarorin aikinsu, lafiyarsu da kuma yadda ya shafi rayuwar ɗan’adam? Wadannan sune tambayoyin da za mu yi ƙoƙarin amsawa a wannan maƙalar in Allah Ya so.
Mene ne ciwon zuciya?
Ciwon zuciya, wanda ake kira da Turanci, heart disease ko cardiovascular disease, yana faruwa ne a lokacin da wani ɓangare na tsokar zuciya bai sami wadataccen jini ba. Yawanci hakan kan afku ne saboda toshewar arteries, wato jijiyoyin jini. Waɗannan arteries su ne jijiyoyin da ke jigilar isar da iskar oxygen da jini da abubuwan inganta jiki zuwa tsokar zuciya. Lokacin da suka toshe, wani yanki na tsokar zuciya zai iya lalacewa ko ya mutu saboda rashin iskar oxygen, wanda ke zama silar bugawar zuciya. A yayinda haka ta kasance, masu fama da ciwon kan yi laushi, wannan kuma zai iya kai su ga mutuwa.
Ciwon zuciya ya kasance babban ƙalubale na kiwon lafiya a cikin al’ummar yau, domin kuwa yana ɗaya daga cikin mafi tsananin nau’ikan cutukan da ke haɗiye rayuka a duk faɗin duniya. Kowace shekara, miliyoyin rayuka ake rasawa bayan kamuwa da cutar. Ciwon zuciya shi ne kan gaba wajen kawo ajalin mutane da dama a ƙasashe masu arziki, domin an yi kiyasin cewa a kowane rabin minti mutum guda na mutuwa a sanadiyar ciwon zuciya a ƙasashen Yamma, duk da ci gaban da suka samu wajen wayewa da fahimtar cututtukan zuciya da aikin tiyatar zuciya.
Alamomin ciwon zuciya
Kamar yadda Ogunlabi (2017) ya kawo, akwai alamomin ciwon zuciya da dama waɗanda suke bayyana gabanin ciwon ya kai mummunan mataki, ga wasu daga cikin alamomin.
• Rashin kuzari
Jin kasala ko rashin kuzari na ɗaya daga cikin alamomin bugun zuciya musamman ga mata. Jin kasala na daga cikin alamomin bugun zuciya wanda zai iya kai mutum ga kasa yin wani aikin. A cewar masana, hakan ya sanya a lokacin bugun zuciya jinin da ke zagayawa a zuciya yakan ragu tare da sanya jin gajiya a damtse.
• Raguwar numfashi
Wata alamar ciwon zuciyar kuma ita ce ta raguwar yin numfashi. Za a riƙa jin raguwar numfashi, misali idan aka hau bene za a riƙa yin haki. In har ana jin wannan yanayi na yin numfashi da kyar da jin gajiya bayan an yi ‘yar tafiya, to hakan alama ce da ke nuni da rashin lafiyar zuciya.
• Jin zafi mai radadi a zuciya
Za kuma a riƙa jin zafi mai raɗaɗi a zuciya, wanda kuma ba lallai ne ya cika damun mutane ba, don haka a tabbatar da an tuntuɓi masana kiwon lafiya domin wannan alama ce ta ciwon zuciya kuma hakan yana hana jini yawo zuwa zuciya.
• Ciwon ciki
Ciwon zuciya wani lokacin yakan janyo lalacewar ciki kamar jin amai, saboda hakan yakan faru ne dalilin wani irin nau’in abinci da aka ci.
• Fesowar ƙuraje a baya ko a ƙirji ko damtsen hannu
Fesowar kuraje a wurin y ana haddasa raɗaɗi. Jin raɗaɗi a waɗannan wurare sakamakon fesowar ƙurajen alamomi ne na an kamu da ciwon zuciya, kuma hakan yana janyo rashin fitar iska saboda jijiyoyin jini sun toshe. Idan aka fara ji ko ganin waɗannan alamomin to a tabbatar an nemi agajin likita.
• Rashin jin daɗin makogoro ko wuya ko mukamuki
Yana daga cikin alamomin ciwon zuciya ko bugun zuciya a dinga jin rashin daɗi a maƙogwaro ko a wuya ko kuma a muƙamuƙi, wanda kuma ba a saba jin irin sa a baya ba. Saboda haka mutane masu fama da ciwon zuciya sukan mayar da hankali a dukkan wani canji da suka ji a jikinsu.
Nau’ikan ciwon zuciya
• Ciwon zuciya na jarirai
Akwai ciwon zuciya wanda ake haifar jarirai da shi, kuma yana da nau’ika guda biyu; mai tsanani da marar tsanani. Mai tsanani shi ne wanda wasu jariran ma ba sa kwana, da zarar an haife su suke komawa. Nau’i marar tsanani kuma shi ne wanda jariri zai rayu har ya girma da shi ba tare da ma an gane ba.
Alamomin da za a fahimta jariri na da wannan ciwo ya danganta da tsanani ko rashin tsananin ciwon. Wani lokaci ba wata alama da ake gani, kuma hakan na nufin yaro zai iya rayuwarsa lafiya ba tare da matsala ba. Wani lokaci kuma, akan ga wasu alamomi waɗanda suka haɗa da yawan haki, ko kuma ya kasance jariri ba ya iya shan nono sosai, idan ya sha kaɗan sai ya huta sannan ya ƙara sha, ko a ga leɓensa yana yin duhu ko baƙi-baƙi maimakon launin hoda.
A wasu lokutan kuma za a iya ganin ƙirjin yaro yana harbawa ɓal-ɓal, saboda saurin da zuciyar ke yi wajen bugawa. Idan yaro ya fara magana, yakan iya cewa yana jin ciwon ƙirji, kuma bai cika samun sukunin shiga wasannin yara ba, ko ya shiga yana saurin gajiya.
• Ciwon zuciyar hawan jini
Hawan jini na kawo ciwon zuciya, sai dai hakan na faruwa ne idan hawan jinin ya ɗaɗe a jikin mutum ba a sauko da shi ba ta hanyar shan magunguna waɗanda za a iya samu a asibiti.
Mai ɗauke da wannan ciwo zai iya jin numfashi sama-sama, musamman idan ya kwanta, wanda hakan kan sa mutum kwanciya da matashi biyu ko uku. Numfashi sama-sama zai iya sa mutum ya kasa barci, domin da ya kwanta sai ya ji kamar an shaƙe shi. Sai kuma a fara tari, da kumburin ƙafafuwa. Wani lokaci akwai ciwon ƙirji.
• Ƙiba
Kiba tana lahani ga zuciya idan daskararren mai ya toshe magudanan jini da suke zagaye da zuciyar, don su ne suke ba ta nata kason na jini. Idan hakan ta faru ɓangaren da abin ya shafa a jikin zuciyar zai iya mutuwa, ya kuma jawo matsala ga zuciyar bakiɗaya. Yawancin masu ƙiba kuma suna da hawan jini, wanda hakan kan haɗu ya ƙara wa zuciya ciwo.
Babbar alamar da ake ji idan irin wannan ciwon ya kama mutum shi ne ciwon tsakiyar ƙirji, daidai saitin da zuciya take. Ciwon ya fi tashi idan aka ɗan yi wani kazar-kazar, ko aka ji mummunan labari.
Yakan lafa idan aka ɗan zauna aka huta. Za a iya ganin mutum yana zufa ko gumi idan ciwon ya yi tsanani, wanda hakan alama ce ta cewa dole a kai mutum asibiti cikin gaggawa kada zuciya ta buga.
• Ƙwayoyin cuta
Ƙwayoyin cuta daba-daban kan samu damar shiga cikin zuciya su samu wurin zama idan jini ya kwaso su daga wasu sassan jiki musamman waɗanda suke daga baki da maƙogwaro, su sa wa zuciya. Akwai irin wannan ciwon zuciya da ƙwayoyin cuta kan kawo har iri biyu, wato ‘Rheumatic Valvular Heart Disease’ mai kama murafan zuciya da ‘Infective Endocarditis’ mai kama tsokar naman zuciyar.
Ƙwayar cutar bakteriya ita ta fi samun sukuni a jikin zuciya, duk da cewa ƙwayoyin irin su virus da fungus sukan iya sa wa zuciya ciwo.
• Ciwon hunhu
Akwai kuma nau’in ciwon zuciya wanda ciwo a hunhu ne kan haifar, wato idan aka samu matsala a hunhu matsalar takan iya shafar zuciya. Cututtukan hunhu da za su iya sa ciwon zuciya sun haɗa da ciwon tarin fuka, da ciwon daji na hunhu, wanda ya fi kama masu shan taba sigari.
Abubuwa masu haɗari game da ciwon zuciya
1. Shekaru: Maza masu shekaru 45 da mata sama da 55 sun fi shiga haɗarin kamuwa da ciwon zuciya.
2. Taba sigari: Wannan ya haɗa da shan tabar da kuma shaƙar hayaƙinta na dogon lokaci.
3. Hawan jini: Wannan na iya lalata jijiyoyin bugun jini da ke kaiwa ga zuciya a kan lokaci. Hawan jini da sauran cututtuka, irin su ƙiba, yawan kitse ko ciwon sukari, suna ƙara haɗarin sosai.
4. Ciwon suga: Yawan sukarin jini yana tashi lokacin da jiki ba ya samarwa ko amfani da sinadarin insulin na hormone yadda yakamata. Yawan sukarin jinin yana janyo samuwar bugun zuciya.
5. Abinci marar inganci: Abincin mai yawan sinadarin suga da kitsen dabba, abinci mai maiƙo da gishiri suna hura wutar haɗarin cututtukan zuciya.
6. Damuwa: Matsananciyar damuwa, kamar fishi, na iya haifar da cutar bugun zuciya.
Shima Garba (2024) ya kara da cewa hawan jini, kiba da ta wuce kima, yawan shan giya, tu’ammuli da guba, cin abinci mara tsafta, gadon ciwon, kwayoyin cuta da karanci sinadarai a jiki duk suna iya jefa mutum cikin hadarin kamuwa da ciwon zuciya.
Hanyoyin gwaje-gwaje
Ana gano ciwon zuciya ta hanyar lura da hawan jini, bugun jini, da zazzabi. Ana yin gwaje-gwaje don tantance yadda zuciya ke bugawa da kuma tantance lafiyar zuciya gabaɗaya. Gwaje-gwajen na’urori da ake yi don gano ciwon zuciya sun haɗa da:
• Electrocardiogram (ECG)
Wannan gwaji ne da ake yi don gano ciwon zuciya da kuma lura da na’urorin da ke aiki a cikinta. Ana sanya na’urar (electrodes) a ƙirjin marar lafiya, a wasu lokutan kuma hannaye da ƙafafu.
• Gwajin jini
Bayan bugun zuciya, wasu sinadaran zuciya suna ci gaba da sauka cikin jini. Ana iya gano waɗannan sinadaran ta amfani da gwajin jini.
• X-ray (Hoton ƙirji)
Ɗaukar hoton kirji yana nuna yanayi da girman zuciya da huhu.
Magungunan ciwon zuciya
Akwai wasu nau’in magungunan ciwon zuciya na asibiti da kafar Hesperian Health Guides ta wallafa a shafinta yanar gizo wanda suka haɗa da:
- Aspirin magani ne da ake ba wa wanda ciwon zuciya ya buge nan take, kafin a kai shi zuwa ga asibiti.
- Morphine magani ne domin magance raɗaɗi da kuma sauƙaƙa wa zuciyar wajen turo jini.
- Nitroglycerine (glyceryl trinitrate)
- Ana amfani da nitroglycerine wajen magance zafin ƙirji na ciwon zuciya. Yana kuma taimakawa wajen ƙara faɗin hanyoyin jini wanda zai sa zuciya ta sami sauƙi wurin turo jini.
Magungunan gargajiya
Ahmad (2024) ya bayyana wasu hanyoyi na gargajiya da za a iya amfani da su a matsayin magungunan ciwon zuciya na gargajiya, ga su kamar haka;
- Shan ruwan zafi ko shayi. Sai dai masana sun fi bayar da shawarar shan ruwa zoɓo mai ɗumi.
- A wasu binciken da yawa sun bayyana tafarnuwa cewa tana maganin ciwon zuciya. Ana iya haɗa ta da kanumfari ko da madara.
- Hodar kurkur ma ana haɗawa da ruwan madara mai ɗumi a sha. Ana sha ne kafin a kwanta barci, yana taimakawa sosai wajen maganin ciwon zuciya.
- Ana iya shan ruwan citta ko shayinta, shi ma masana sun yi amannar yana taimakawa sosai wajen magance matsalar zuciya.
Mene ne ciwon ƙoda
Ciwon ƙoda na nufin rashin jin daɗi ko lalacewa ko gazawa a aiwatar da ayyukan ƙoda. Waɗannan gaɓoɓi biyu masu siffar wake suna maƙale a ƙasan haƙarƙari, ɗaya a kowane gefen ƙashin baya. Ciwon ƙoda sau da yawa yana nuna alamar matsala a cikin yanayin fitsari.
Ƙoda na da mahimmanci don samun lafiyayyen jiki. Su ne ke aiwatar da aikin tace abubuwa marasa kyau, ruwan da ba shi da kyau, da sauran ƙazanta daga cikin jini. Ana tura waɗannan gurɓatattun abubuwa cikin mafitsara sannan a fitar da su yayin fitsari.
Ƙoda na daidaita matakan pH, gishiri, da potassium a cikin jiki. Tana samar da hormones waɗanda ke daidaita hawan jini da sarrafa samar da jajayen ƙwayoyin jini (red blood cells). Ƙoda na taimakawa wajen samar da wani nau’i na bitamin D, wanda ke taimaka wa jiki da sinadarin calcium.
Cututtukan ƙoda na iya haifar da wasu matsalolin lafiya, ciki har da raunin ƙasusuwa, lalacewar jijiya, da rashin abinci mai gina jiki. Idan cutar ta yi ƙamari, ƙoda na iya daina aiki gabaɗaya. Wannan yana nufin cewa za a buƙaci dialysis don yin aikin koda. Dialysis magani ne da ke tacewa da tsarkake jini ta amfani da na’ura. Ba zai iya magance cutar koda ba, amma yana iya tsawaita rayuwar mai ɗauke da cutar.
Alamomin cutar ƙoda
Yawancin ciwon koda bai cika bayyana da wuri ba sai ya kai matakin da ya ta’azzara. Shafin Medicover Hospital sun bayyana alamomin ciwon koda dake bayyana da farko idan mutum na dauke da cutar koda, kamar haka;
- Gajiya
- Rashin nutsuwa
- Rashin barci
- Rashin sha’awar cin abinci
- Wani sashe na jiki ya rika motsi haka nan
- Kumburin ƙafa da gwiwa
- Kumburin idanu da safe
- Bushewar fata
- Yawan fitsari musamman da dare
Idan kuma cutar ta yi tsanani sosai, ana ganin alamomi kamar:
- Tashin zuciya
- Amai
- Rashin jin sha’awar jima’i
- Canjin fitsari
Ciwon ƙoda na saka lalacewar jijiyoyi, da raguwar karfin ƙashi, da kuma saka rama. Idan cutar ta yi muni, hanta tana daina aiki kwata-kwata, sai dai a koma inji ya riƙa wanke ƙoda.
Abubuwan da ke kawo cutar ƙoda
Abubuwan dake kawo cutar ƙoda sun hada da:
- Ciwon hawan jini
- Ciwon suga
- Yawan fitsari
- Rashin fitsari
- Gado daga iyaye
- Tsufa ko yawan shekaru
Sai dai bincike ya nuna cewa, yawanci ciwon hawan jini da ciwon suga ne ke kan gaba wajen kawo cutar ƙoda.
Nau’ikan cutar ƙoda
• Cutar ƙoda mai tsanani
Wannan ita ce cutar ƙodar da hawan jini yake haddasawa wadda kuma ita ce aka fi fama da ita. Takan daɗe a jikin mutum kuma za a ga kullun lamarin ƙara munana yake. Hawan jini kan janyo tura wa ƙoda jini da yawa wanda hakan ke sa ta riƙa aiki fiye da yadda ya kamata wanda a ƙarshe har ta kai dakatawa da aiki. Ciwon sukari ma yana kan gaba wajen taimakawa sosai da kamuwa da irin wannan cutar ƙodar.
• Kidney stones
Wannan cutar ƙoda ce wacce wasu abubuwa masu ƙarfi ke taruwa, yawanci ana fitsarar da su ne. Sukan sa mutum ya ji zafin fitsarinsa sosai. Ita ma wannan cuta ana yawan fama da ita.
• Glomerulonephritis
Wannan nau’in cutar yakan sa ƙodar mutum ta kumbura ne kuma ana samun hakan daga shan ƙwayoyi, kafin ko bayan haihuwa, ko kuma wata karamar cuta, yawanci kodar kan koma daidai da kanta.
• Polycystic kidney disease
Ita wannan nau’in cutar ƙoda takan sa wani abu ya kumbura a kan ƙodar mutum wanda a ƙarshe yakan hana kodar aikinta yadda ya kamata. Sai dai wasu lokutan wannan kumburi bai cika yi wa ƙodar illa ba.
• Urinary tract infections
Wannan kuma cutar fitsari ce wadda ke da alaka da ƙoda. Idan aka yi maganinta da wuri babu wata illa. Idan kuwa aka yi sakaci, ba shakka za ta iya zama illa sosai har ta kai ga lalata ƙoda.
Nau’ikan abincin mai cutar ƙoda
Abinci mai gina jiki na da matuƙar muhimmaci wajen magance ciwon ƙoda, kusan ɗaya yake da shan magani, abincin mai ciwon ƙoda kamar yadda masana suka bayyana su ne:
- ‘Ya’yan itatuwa, lemo, ayaba, abarba, da sauran su
- Kifi
- Ganye irin su alayyahu, kabeji, zogale da sauran su
- Gero, Alkalama, Dawa, Masara, da sauran hatsi
- A riƙa motsa jiki kuma akai-akai
Riga-kafin ciwon ƙoda
- A rika shan ruwa akai-akai
- Idan akwai ciwon sukari, kada a bari jini ya hau
- A Rage shan gishiri
- A daina shan giya
- A daina shan taba
- A rage cin jan nama da kaji
- A daina shan magani ba tare da umarnin likita ba don kuwa wasu magungunan na lalata ƙoda.
Maganin ciwon ƙoda na gargajiya
Zuma na maganin ciwon koda wanda ake kira da kidney stones. Ya danganta da irin ciwon ƙodar da ake fama da shi.
Yadda ake amfani da zumar shibne, ana haɗa ta da lemon tsami ne, wannan haɗi yana tarwatsa kidney stones kuma a warke, amma ba a tabbatar cewa ko zuma na maganin cutar ƙoda mai tsanani ba.
Wasu muhimman bayanai game da ciwon ƙoda
• Ba a warkewa daga cutar ƙoda mai tsanani, sai dai akwai magunguna da hanyoyi da ake bi wajen rage radadinta musamman idan ba ta kai matakin gargara ba.
• Mai cutar wanda bai samu kulawa ba, tana kisa farat ɗaya. Cikin kwanaki kaɗan mutum na iya mutuwa. Amma idan aka samu kulawa mai kyau, masana sun ce ana iya rayuwa har tsawon shekaru goma ko fiye da haka.
• Idan cutar ƙoda ta yi tsanani sosai tana hana haihuwa.
Kammalawa
Kamar yadda ya gabata a bayanai, zuciya da koda suna da matukar muhimmanci a jikin ɗan’adam, kuma dukkansu sun jibanci amfani da jini inda zuciya ke aikin sarrafa jinin zuwa dukkan sassan jikin ɗan’adam, a yayinda ita kuma koda ke aikin tace jinin. Wannan yana nuna cewa illa ga daya yana iya shafar dayan kaistaye. Kowannensu idan ya tabu yana iya haifar da cututtuka daban-daban, sai dai idan aka kiyaye akan lokaci kuma aka ziyarci ma’aikatan lafiya ana iya gujewa fadawa mummunar yanayi.
Manazarta
Ahmed, B. (2024, June 15). Maganin ciwon zuciya na Gargajiya. Hutudole
Garba, A. (2024, May 13). Ciwon zuciya. Bakandamiya
Hospitals, M. (n.d.-b). Kidney pain: causes, symptoms, and effective treatments
Medicines for heart Attack – Hesperian Health Guides. (n.d.).
Ogunlami, Y. (2017, February 7). Alamun ciwon zuciya ga jikin Mata. Pulse Nigeria
Sulaiman, H. (2024, April 17). Zuciya. Bakandamiya