Skip to content

Yadda ake samarwa da rarraba wutan lantarki a Nigeria

Wutan lantarki a Nigeria

Tun daga shekarar 1896, wato lokacin da aka samar da wutar lantarki a Najeriya, kawo wannan lokacin, ana ci gaba da fuskantar ƙalubale a fannin lantarkin da suka haɗa da samarwa da rarrabawa. Shin waɗanne manyan matsaloli ne suke haifar da wannan tarnaƙi, kuma ta yaya za a magance su? Wannan maƙala ta yi ƙoƙarin fayyace yadda ake samarwa da rarraba wutar lantarkin har ta isa gidaje da masana’antu. Haka nan maƙalar ta yi duba kan ƙalubalen da ke kawo cikas wajen samar da wutar lantarki mai inganci da rahusa kuma abar dogaro ga al’ummar ƙasa Najeriya. Wutar lantarki na taka muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum ta kowane ɗan Najeriya, tana samar da haske ga gidaje, tana tallafa wa harkokin sadarwa da ci gaban kasuwanci da masana’antu. Fahimtar yadda samarwa da rarraba wutar lantarki yake abu ne mai rikitarwa; ya ƙunshi ɓangarori daban-daban. Mun yi nazarin yadda kowane ɓangare ke aikinsa don samar da wutar lantarki.

Me ake nufi da wutar lantarki?

A cewar ƙamus ɗin Merriam-Webster, ‘wutar lantarki wani nau’i ce na makamashi da ake iya samu ta fuskoki daban-daban, kamar hasken lantarki da kan samu ta hanyoyin asali, ko kuma ta na’urar janareta. Wanda ya fara gano makamashin lantarki a duniya shi ne Benjamin Franklin, wani masani ɗan ƙasar Amurka a shekarar 1752.

Wutar lantarki wani nau’i ce na makamashi wanda ya samo asali daga abubuwan da ke da makamashin subatomic kamar su; electrons, protons, da dai sauransu. Wutar lantarki na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da suke da tasiri a duniyar ɗan’adam tare da kawo cigaba. A dukkan faɗin duniya, ana amfani da wutar lantarki don aiwatar da ayyuka da yawa, saboda haka ta zama wani ɓangare na rayuwar yau da kullun.

A fannin ilimin kimiyya, a matakin farko, mun san cewa abubuwan da ke cikin sararin samaniya sun haɗa da ƙwayoyin halitta da sinadarai da makamashi masu yawa, kuma kowanne makamashi ko sinadari yana da adadin ƙwayoyin sinadarai a ƙarƙashinsa, kamar makamashin electrons, protons, da neutrons. A yayin da electrons ke samar da ɓangare marar caji, protons kuma su ne ɓangarorin da ke samar da makamashin caji, neutrons su ne tsaka-tsaki.

Yadda ake samar da wutar lantarki?

Samar makamashin lantarki wato (generation) shi ne mataki na farko a tsarin samar da wutar lantarki. Ana yin hakan ne ta hanyar amfani da tashoshin wutar lantarki, waɗanda ke canja nau’ikan makamashi daban-daban zuwa wutar lantarki. Mafi yawan hanyoyin samar da wutar lantarki su ne ta amfani da albarkatun ɗanyen mai (kamar gawayi, iskar gas, da man fetur), makamashin nukiliya, da sauran hanyoyin samar da makamashi, kamar hasken rana, iska, da ruwa da sauran su.

A wani ɓangaren kuma, samar da makamashin lantarki wata fasaha ce ta tsarin samar da wutar lantarki. Wannan aiki na samar da makamashin shi ne mataki na farko kuma mafi mahimmanci a cikin matakan samar da wutar lantarki. Ya ƙunshi canja asalin makamashin farko kamar gawayi, iskar gas, makamashin nukiliya, makamashin hasken rana, ruwa zuwa makamashin lantarki. Zaɓin asalin makamashi ya dogara ne a kan yanayin ƙasa, tattalin arziki, da kuma muhalli.

Kowace hanya daga cikin waɗannan hanyoyi na da nata tsarin fasaha da abubuwan more rayuwa. Misali, tsarin amfani da hasken rana wato photovoltaic na canja hasken rana kai tsaye zuwa makamashin wutar lantarki.

Wuraren sarrafa makamashin wutar lantarki yawanci manya ne kuma suna nesa da birane, saboda yanayin tsarin aikinsu. Girman waɗannan wurare da abubuwan da suke samarwa ya bambanta sosai, daga manyan tashoshi da ke samar da dubban megawatts zuwa ƙanana da ke samar da kilowatt kaɗan.

Yadda ake watsawa da rarraba lantarki

Watsawa da rarrabawa hanyoyi ne daban-daban waɗanda ake jigilar wutar lantarki daga injinan da ke tashoshin lantarki zuwa ga abokan ciniki. Da zarar an samar da makamashi, ana rarraba shi zuwa gidaje, kasuwanni, da masana’antu ta hanyar tsarin wayoyin lantarki da aka sani da grid. Watsawa da rarraba matakai ne daban-daban guda biyu da ke a kan tsarin grid.

Yadda ake dakon lantarki

Dakon makamashi lantarki shi ne tsarin da ake bi wajen jigilar wutar lantarki daga cibiyar samarwa, kamar tashoshin wutar lantarki, zuwa tashoshin da ke kusa da jama’a. Hanyoyin turawar suna da nisa, kuma suna ɗauke da adadi mai yawa na makamashi mai ƙarfi. Ƙarfin da ke cikin hanyoyin turawar yana gudana da ƙarfin lantarki wanda ya yi tsayi sosai, saboda ba za a iya isar da shi ga masu amfani kai tsaye ba. Sakamakon haka, masu rarraba makamashin sukan rage yawan wutar lantarki da ake turawa kafin isar da ita zuwa gidaje da masana’antu. Ana iya gano hanyoyin watsawa ta yanayin girmansu da tsarinsu. Waɗannan hanyoyin suna da tsayi, yawanci ƙafa 30 daga ƙasa, suna ɗauke da wayoyi da yawa kuma suna da nisa sosai.

Yadda ake rarraba lantarki

Tsarin rarraba makamashin lantarki yana nufin mataki na ƙarshe na tsarin  samar da makamashin zuwa ga masu amfani. Wutar lantarki tana tafiya a kan tsarin rarrabawa wanda ya dace da muhallan gidaje da na kamfanoni. Masu amfani da lantarki za su iya gane hanyoyin rarrabawa cikin sauƙi yayin da suke tafiya a kan titunan unguwanni. Ana amfani da wutar lantarkin da ake bayarwa ta hanyoyin rarrabawa da na’urori da sauran su.

Wutar lantarki a Najeriya kafin samun yancin kai

An gina tashar wutar lantarki ta farko a Najeriya a shekarar 1896, wadda ta ƙunshi 30KW, 1000 volt, da ƙarin da aka yi a shekarar 1902, sannan kuma kawo shekarar 1909, an ƙara ƙarfin wutar inda ya kai 120KW. A cikin shekarar 1920, ƙarfin tashar wutar lantarki ta Legas Marina ya kai 420KW. An gina tashar wutar lantarki ta farko da aka yi amfani da gawayi a ranar 1 ga Yunin 1923 tana samar da jimullar wutar lantarki mai ƙarfin 3.6MW. Sakamakon rufe tashar Marina a ranar 28 Nuwamba 1923, an ƙara wa sabuwar tashar wutar lantarkin ƙarfin da ya kai 13.75MW.

Duk da wannan ci gaban da aka samu a tsakanin shekarar 1944 zuwa 1948, Najeriya ta fara fuskantar koma baya wajen amfani da gawayi don samar da wutar lantarki, sakamakon raguwar ayyukan haƙar ma’adinai, da kuma samuwar ɗanyen mai da yawaitarsa a shekarar 1956.

Tsarin wutar lantarki bayan samun ‘yancin kai

Bayan samun ‘yancin kan ƙasa Najeriya, an ci gaba da rarraba wutar lantarki a Najeriya tare da haɗa tashoshin wutar lantarki a Kainji, Jebba, Shiroro, Afam, Delta (Ughelli), Sapele (Ogorode), da kuma Egbin (Lagos) a farkon shekarar 1960. A wancan lokacin, 330KV ya ƙaru zuwa bangarorin ashirin da takwas da hanyoyin rarrabawa talatin da biyu. Hanyoyin rarrabawar da ake da su sun ƙaru daga talatin da biyu (32) zuwa sittin da huɗu (64) da kuma ɓangarori ashirin da takwas (28) zuwa hamsin da biyu (52) tsakanin shekarun 1998 da 2012.  Wayoyin lantarkin sun haɗa waɗannan tashoshi da ɓangarori hamsin da biyu da hanyoyin rarrabawa sittin da huɗu wanda suka ƙunshi cibiyoyin sarrafawa guda huɗu (cibiya ɗaya a Oshogbo da cibiyoyi uku a Benin, Shiroro, da Egbin).

Sauyin da aka samu a fannin makamashin lantarki a Najeriya ya samu ne ta hanyar rarraba wutar lantarki na kai tsaye, wanda ya haifar da kamfanoni shida masu samar da wutar lantarki da IPPs, wadanda ake kira Gencos. Sauyin ya fara ne da kafa hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya wato (ECN) a shekarar 1951 da kuma hukumar kula da madatsar ruwa ta Neja (NDA) a shekarar 1962. An hade ECN da NDA ƙarƙashin doka mai lamba ta 24 ta shekarar 1972 aka kafa hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya wato (NEPA), daga baya ta koma Power Holding Company of Nigeria (PHCN). A shekara ta 2001, aka fara yin garambawul a fannin wutar lantarki tare da fitar da manufar samar da wutar lantarki ta ƙasa, abin da wannan manufa ta ƙunsa shi ne samar da ingantacciyar wutar lantarki a Najeriya. Babbar manufar wannan ƙudiri shi ne hannanta ikon gudanarwa da sarrafa kadarorin ma’aikatar wutar lantarki ga kamfanoni masu zaman kansu, tare da samar da duk wasu tsare-tsare da ake bukata don ci gaban harkokin wutar lantarki a Najeriya.

A shekarar 2005, aka ƙirƙiri dokar sake fasalin ɓangaren wutar lantarki (EPSR), sannan aka kafa hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya wato (NERC) a matsayin wata hukuma mai zaman kanta mai kula da harkar wutar lantarki a Najeriya. Bugu da kari, an kafa kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (PHCN) a matsayin kamfani na riƙon ƙwarya wanda ya ƙunshi kamfanoni 18 da suka gada (kamfanonin tsarawa guda 6, kamfanonin rarrabawa guda 11, da kamfanin watsawa guda 1) da aka ƙirƙira ƙarkashin NEPA.

A shekarar 2005, jimillar ma’aunin wutar lantarkin da aka samu a dukkan tashoshin samar da wutar lantarki na kamfanin Power Holding Company of Nigeria (PHCN) ya kai 6656.40MW, tare da matsakaicin karfin da ya kai 3736.55MW, wanda ya samar da kashi 56.13%. A watan Yulin shekarar 2009, jimullar ƙarfin samar da wutar lantarkin na PHCN ya kai MW 9,914.4, yayin da megawatt 1,115 yake fitowa daga IPPs.

A cikin 2O10, aka kafa kamfanin Nigerian Bulk Electricity Trading Plc (NBET) a matsayin amintaccen kamfani mai karɓar wutar lantarki daga kamfanonin da ke samarwa. Kawo Nuwambar 2013, aka kammala cefanar da dukkan cibiyoyin sarrafa makamashin lantarki. Har ila yau, a watan Yulin 2014, jimullar ƙarfin tashar samar da wutar lantarki ya ƙaru zuwa 8,876MW, sai dai ana iya samar da makamashin mai karfin 3,795MW ne kawai.

A halin yanzu grids guda 23 ne suke aiki tare da tashoshin Samar da Wutar Lantarki ta Najeriya (NESI) waɗanda ke da jimullar 11,165.4MW kuma suke iya samar da 7,139.6MW. Yawancin tashoshin na tushen zafi ne, suna da jimullar ƙarfin 9,044MW (81%) wanda sukan iya samar da 6,079.6MW. Wutar lantarki daga manyan tashohi uku na da jimullar ƙarfin 1,938.4MW, da kuma ƙarfin da suke iya samarwa da ya kai 1,060MW.

Yawan wutar lantarkin da ake samarwa ya ragu sosai fiye da buƙata da ake da ita; Misali, a cikin shekarar 2014 da 2016, adadin da ake samarwa ya ragu da 21,639MW da 23,401MW, wanda ke wakiltar kusan kashi 15% da 17% na samar da wutar lantarki. Don haka, ba a samu ƙaruwar wutar lantarki daidai da yadda yawan jama’a ke ƙaruwa ba, kamar yadda aka samu a shekarar 2014, lokacin da yawan al’ummar ƙasa ya ƙaru zuwa miliyan 165 amma jimillar wutar da aka samu 3,795MW ce kawai.

Kamfanin dakon wutar lantarki na Najeriya wato (TCN) ne ke kula da hanyoyin tunkuɗa wutar lantarki a ƙasar. Yana ɗaya daga cikin kamfanoni 18 da suka kasance ƙarƙashin kamfanin Power Holding Company of Nigeria (PHCN) a watan Afrilun 2004 kuma ya samo asali ne daga hadewar sassan rarrabawa da tsarin aiki na PHCN. An kafa shi ne a watan Nuwamba 2005 kuma ya samu lasisin dakon lantarki a ranar 1 ga Yuli, 2006. A halin yanzu TCN mallakar gwamnati ne ita ke da alhakin gudanar da shi, kuma a wani ɓangare na shirin sake fasalin gwamnati, za a sake tsara shi tare da sake fasalinsa don ingantawa da faɗaɗa ayyukansa.

Kawo yanzu, tsarin dakon lantarki yana ɗaukar kusan kilomita 5,523.8 na hanyoyin 330KV, kilomita 6,801.49 na hanyoyin 132KV, da kuma 24,000 na hanyar rarrabawa (33KV). Cibiyar rarraba wutar lantarki a halin yanzu tana da kilomita 19,000 na hanyoyin 11KV da kusan tashoshin 22,500. Haka nan a yanzu, kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 ne suka mamaye ƙasa baki daya.

A shekarar 2013, aka kammala cefanar da kamfanonin rarraba wutar lantarki 10, yayin da gwamnatin tarayya ta ci gaba da riƙe ikon mallakar kamfanin dakon wutar wato TCN. An kuma kammala cefanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na 11 a watan Nuwamba 2014. A yanzu haka akwai jimullar kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 wato Distribution Companies (DisCos) a Najeriya.

A shekarar 1990, ƙarfin wutar lantarkin Najeriya ya gaza biyan buƙatun wutar lantarki ga ‘yan ƙasa, wanda ya haifar da ƙirƙirar manufar samar da wutar lantarki ta kasa ta shekarar 2001 da wasu gyare-gyare da dama. Kawo shekara ta 2000, hukumar kula da wutar lantarki ta ƙasa (NEPA), ce ke kula da samar da wutar lantarki, watsawa, da rarrabawa a Najeriya. Tana samar da jimillar ƙarfin lantarki kusan 6,200MW daga tashoshin ruwa guda 2 da kuma wasu tasoshin wutar lantarki guda 4. Wannan ya haifar da rashin jin daɗi da rashin dogaro da wutar lantarki a ƙasar, inda abokan ciniki ke fuskantar matsalar rashin wutar lantarki akai-akai da kuma katsewarta na tsawon lokaci da rashin kula da kayan aiki, tsofaffin na’urorin, ƙarancin kuɗaɗen shiga, da yawan asarar da ake samu, satar wutar lantarki, da kuma rashin tsarin jadawalin kuɗaɗen lantarkin.

A cikin shekarar 2001, aka kafa hukumomin samar da wutar lantarki masu zaman kansu wato (IPPs) da National Integrated Power Projects (NIPP) don magance matsalar ƙarancin wutar lantarki. A shekarar 2005, Najeriya na da kiyasin megawatt 6,861 na kuzarin wutar lantarki.

Hanyoyin makamashin lantarki a Najeriya

Akwai hanyoyin samar da wutar lantarki da yawa a Najeriya. Ƙasar na da kuzarin samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 16,384. Samar da wutar lantarki a Najeriya ya samo asali ne daga tashoshin wutar lantarki da ake fitarwa daga ruwa da iskar gas, inda kamfanonin ruwa ke samar da megawatt 2,062 da iskar gas mai karfin megawatt 11,972. Solar, iska, da sauran hanyoyin kamar dizal da man fetur mai nauyi (HFO) su ne ragowar hanyoyin da ke samar da megawatt 2,350.

A ranar 28 ga Fabrairu, 2021, Najeriya ta sami mafi girman ƙarfin lantarki wato megawatt 5,615.40, wato ƙarin megawatt 22 fiye da baya, kuma hakan ya zo kwanaki uku bayan da ƙarfin ya kai ƙololuwarsa wato megawatt 5,593.40 yadda ake iya samu a baya. Wannan ba wani abin yabawa ne duba da buƙatar ƙasar ta yawan makamashi sama da megawatt 98,000.

• Solar

A cewar Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya (NIMET), babban tattalin arzikin nahiyar Afirka yana cikin hasken rana a kowace shekara wanda ya kai sa’o’i 6.25 a kowace rana (Rahoton Makamashi na Najeriya, 2019). Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ke da zafi a duniya da ke tsakanin 40 zuwa 130, da faɗin ƙasar da ya kai 9.24 × 105 km2 kuma tana more matsakaicin sa’o’in hasken rana a kowace rana, daga sa’o’i 3.5 a yankunan bakin teku zuwa sa’o’i 9.0 a kan iyakokin arewa. Najeriya na samun kusan 4.851 × 1012 kWh na makamashi kowace rana daga hasken rana.

Dangane da faɗin ƙasar da matsakaicin 5.535 kWh/m2/rana, Najeriya tana da matsakaicin 1.804 × 1015 kWh na hasken rana a kowace shekara. Wannan  keɓantaccen makamashin rana na  shekara ɗaya ya kusan yin ninki 27 na yawan albarkatun makamashi na asali a Najeriya. Wannan yana nuna cewa Najeriya tana da dama mai dimbin yawa da za ta sarrafa hasken rana domin samar da makamashin lantarki.

A cewar IRENA, Najeriya ta yi alfahari da kusan megawatt 28 na makamashin da aka tara a shekarar 2019. Wannan ya yi daidai da ci gaban da ake samu a wutar lantarkin ƙasar daga megawatt 15 da aka samu a shekarar 2012 da kuma megawatt 19 a shekarar 2018 (Rahoton Solar Nigeria, 2021). Tsarin Makamashi Mai Sabuntuwa wato (The Renewable Energy Master Plan) na da ƙudirin  samar da megawatt 500 na makamashin lantarki mai amfani da hasken rana a cikin shekarar 2025. Ƙudirin da ake da shi na tattara ƙarfin hasken rana da samar da wutar lantarki ya tasar wa megawatt 427,000.

A ƙarshen shekarar 2019, an yi kiyasin cewa Najeriyar ta girka mini-grid kusan megawatt 2.8, tare da tsare-tsare 59 a yankunan karkara. Waɗannan alƙaluman tun daga lokacin sun canja tare da ƙarin ƙananan grids masu amfani da hasken rana da aka sanya a cikin shekarar 2020. Kasuwanci da masana’antu solar suna ƙaruwa yayin da kamfanoni da ‘yan kasuwa da yawa ke amfani da fasahar wajen gudanar ayyukansu.

• Renewable energy plan (Makamashi mai sabuntawa)

Ƙalubale kamar rashin isasshiyar iskar gas da abubuwan more rayuwa sun kawo cikas ga bunƙasar fannin samar da wutar lantarki na gargajiya, sun tilasta buƙatar makamashin lantarki ta wuce ta amfani da iskar gas zuwa amfani da tsarin makamashin da za a iya sabuntawa don ƙarin ƙarfin wutar lantarki da kuma sabbin hanyoyin sabunta wutar lantarki.

An yi hasashen fitar da hayaki mai gurbata muhalli a Najeriya zai ƙaru da kashi 114% zuwa kusan metric ton miliyan 900 nan da shekarar 2030, amma akwai manufofin ci gaban kasar na rage fitar da hayaki da kashi 20 cikin 100 ba tare da sharadi ba, da kashi 45 bisa 100 na sharadin kasuwanci kamar yadda aka saba (BAU) 2030.

Sakamakon haka, gwamnatin Najeriya ta tsara shirin faɗaɗa ƙarfin gigawatt 30 da aka girka a kan tsarin grid zuwa shekarar 2030, tare da samar da makamashin da ake amfani da shi na zamani wanda zai ba da gudummawar gigawatt 13.8 (45%) da kuma matsakaita da manyan tashohin wutar lantarki na ruwa da ƙarfin gigawatt 9.1 (30%)

• Biomass

Najeriya tana samun ɗimbin ƙwayoyin halittu daga dabbobi da tsarrai musamman matattu kusan ton miliyan 144 a kowace shekara. A cewar hukumar kula da makamashi ta Amurka, yawancin ‘yan Najeriya, musamman mazauna karkara, na amfani da ƙwayoyin halitta da sharar itace, da gawayi, da takin dabbobi domin biyan bukatunsu na makamashi. Wannan shi ne kusan kashi 80% na yawan makamashin da ake amfani da shi a Najeriya. Yawancin waɗannan abubuwa ana amfani da su wajen samar da dumi, samar da haske, da dafa abinci a yankunan karkara.

A watan Nuwambar shekarar 2016 ne gwamnatin jihar Ebonyi ta karbi ragamar hukumar kula da ci gaban masana’antu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNIDO) a cibiyar samar da wutar lantarki ta biomass gas da ke rukunin ƙananan masana’antu na UNIDO da ke Ekwashi Ngbo a ƙaramar hukumar Ohaukwu ta jihar. Kamfanin samar da wutar lantarkin zai samar da megawatts 5.5 na makamashi ta hanyar amfani da ɓuntun shinkafa.

• Hydro (Na ruwa)

Najeriya tana da manyan koguna da saukar ruwan sama, da kuma kiyasin 1,800 m3 a kowace shekara na albarkatun ruwa masu sabuntuwa. Manyan tafkunan da ke samar da wadataccen makamashin ruwa su ne kogin Neja, kogin Benue, da tafkin Chadi. Najeriya dai na da tashoshin samar da wutar lantarki guda shida, duk da cewa ba dukkaninsu ke aiki ba. Manyan tashohi uku suna aiki: Kainji (760MW), Jebba (578MW), da Shiroro (600MW). Akwai kuma aikin samar da wutar lantarki na Mambilla, wanda ake sa ran zai iya samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 3,050 idan an kammala shi.

A halin yanzu, jimullar  wutar lantarki ta kai megawatt 2,062. Bugu da ƙari kuma, ƙididdigar bincike ta nuna jimullar ƙarfin amfani da wutar lantarki ta ruwa ta kai sama da 14,120MW, wanda ya haura 50,800GWh na wutar lantarki a kowace shekara. Don haka, har yanzu akwai giɓin da za a cike na kusan kashi 85 cikin 100 na wutar lantarki da har yanzu ba a samar ba.

• Off-grid

A cewar REA ta Najeriya, idan aka inganta wannan hanyoyi na Off-grid, za a iya haifar da damar kasuwanci da za ta samar da dalar Amurka $9.2B daidai da (₦3.2T a shekara) don samar da ƙananan grid da tsarin amfani da hasken rana wanda zai samar da dalar Amurka $4.4B daidai da (₦1.5T a shekara) daga gidaje da kasuwannin Najeriya.

A halin yanzu, tsarin gidaje masu amfani da hasken rana, tsarin C&I mai amfani da hasken rana, minigrid na hasken rana, da sauran hanyoyin samar da iskar iskar gas sun mamaye sararin samaniya a Najeriya. Kawo shekarar 2019, jimullar ƙarfin samar da wutar lantarki a Najeriya da NERC ta amince da shi ya kai 500MW. Daga cikin wannan alƙaluma, ƙananan grid na hasken rana sun kai kusan 3MW.

• Wind (Na iska)

Ƙarfin samar da makamashi ta hanyar amfani da iska a halin yanzu ya kai megawatt 10. Tashar da ke jihar Katsina, an kammala samar da ita ne a farkon shekarar 2021. A cewar ECOWAS mai sa ido kan makamashi mai inganci, tashar iska ta Katsina za ta ƙunshi GEV MP 275 37KW a arewacin Najeriya. Kammala aikin, wanda aka fara a shekara ta 2005, ya haifar da  cigaba a fannin makamashin iska na Najeriya.

NERC a matsayin hukuma mai zaman kanta

Hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, wato (NERC) hukuma ce mai zaman kanta, wacce aka kafa a ƙarƙashin Dokar Wutar Lantarki ta 2005 (amma an soke ta), yanzu ita ce Dokar Lantarki ta 2023, don aiwatar da tsarin fasaha da tattalin arziki na ma’aikatar samar da wutar lantarki ta Najeriya. Hukumar ce ke da alhakin ba da lasisi, ƙayyade tsare-tsaren aiki da ƙa’idoji, kula da haƙƙin abokin ciniki da samar da wajibai, da tsara jadawalin kuɗaɗen lantarki. Hukumar tana da hedikwatarta a Abuja kuma a halin yanzu tana da rassan ofisoshi a mafi yawan jihohin ƙasar, waɗanda ke aiki a matsayin wuri na farko don gabatar da korafe-korafen abokan hulda da kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) ba su iya warwarewa ba.

Tun da aka kafa NERC ta sami nasarori masu mahimmanci, ciki har da faɗaɗa ƙarfin samar da makamashin ta hanyar ba da lasisi don samar da wutar lantarki, watsawa, rarrabawa, da kasuwancinta, da inganta ka’idojin ma’aikatar da dokokin kasuwanci, da jadawalin biyan kuɗin na shekaru-shekara. Bugu da ƙari, hukumar ta fitar da wasu ka’idoji da umarni da suka samar da kyakkyawan tsarin kasuwancin wutar lantarki a Najeriya.

Waɗannan nasarorin an same su ne ta hanyar tabbatar da cewa hada-hadar kasuwancin lantarki ta dogara ne a kan ƙa’ida da ingantattun hanyoyin tuntubar juna da masu ruwa da tsaki don tabbatar da gaskiya da riƙon amana. Waɗannan halaye na gaskiya, adalci, da kuma rikon amana suna da matuƙar muhimmanci ga hukumar NERC ta Najeriya mai zaman kanta. Dokar Lantarki ta yi taka-tsan-tsan wajen tabbatar da wannan ‘yancin kai. Dokar ta ba da izini kuma ta tanadi ƙa’idar ‘yancin kai ta hanyar:

1. Ƙirƙirar sashen ƙoli na gudanarwar NESI bisa dokar Majalisar Dokoki ta ƙasa maimakon ta wasu dokoki. Sashe na 33 (1) daga ciki yana cewa:

  • “An kafa hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (a cikin wannan dokar, ana kiranta da “Hukumar”), wacce za ta kasance mai zaman kanta kuma za ta iya kai ƙara ko a kai ta da sunanta, bisa ga wannan doka, za ta yi aiki, da duk ayyukan da hukumomi za su iya yi na doka.”
  • Sashe na 33 (3) ya ci gaba da cewa “Hukumar za ta zama matakin koli mai kula da NESI kuma za ta kasance hukuma mai zaman kanta wajen gudanar da ayyukanta da yin amfani da ikonta a ƙarƙashin wannan dokar.”
  • Kwamitin kwamishinonin ne za su ɗauki matakin da ya dace a ƙarƙashin sashe na 35(1) wanda ya ce, hukumar za ta ƙunshi kwamishinoni bakwai na cikakken lokaci da shugaban ƙasa zai naɗa sai majalisar dattawa ta tabbatar da hakan. Waɗannan kwamishinonin, a ƙarƙashin sashe na 226 na dokar, na iya tsara ƙa’idoji a kan duk al’amuran da hukumar ke da iko a kai.

2. Kuɗaɗe, daga kuɗaɗen shiga da ake samu a cikin gida da kuma abubuwan da gwamnati ke yi. Sashi na 53 na dokar ya yi magana ne game da kuɗaɗe ga Hukumar: “Kuɗaɗen Hukumar za su ƙunshi:

  • Kuɗaɗen caje-caje da sauran kuɗaɗen shiga da ke tattare da hukumar daga masu lasisi da sauran abubuwan da ta yi a cikin wannan dokar, ban da duk wani kuɗin tara ko hukuncin da aka samu a karkashin wannan dokar;
  • Kuɗaɗen da majalisa ta ware wa hukumar, a ƙarƙashin bukatar da hukumar ta nuna na neman ƙarin kuɗaɗen da ake buƙata don biyan kuɗaɗen da suka dace; kuma irin waɗannan kuɗaɗe za a iya ba wa hukumar, ko a lokacin gudanar da ayyukanta ko akasin haka.

A halin yanzu, hukumar tana karɓar kashi 1.5% na kuɗaɗen shiga na kasuwancin lantarki a matsayin caje-caje. Idan aka yi la’akari da kuɗaɗen gudanarwa da caje-caje, ya kamata a lura cewa:

  • Alhakin NERC shi ne tsara ka’idojin aiki ga duk masu lasisin wutar lantarki da kuma sa ido kan yadda ake gudanarwa don tabbatar da cewa waɗannan ƙa’idojin sun cika, an kiyaye su.
  • Ana amfani da cajin ƙa’ida ba kawai don ba da kuɗi aikin Hukumar ba, tare da sa ido da aiwatarwa, amma ana amfani da su don biyan kuɗin ayyukan sauran hukumomin aiki na kasuwanci da kwamitoci ta hanyar amfani da shawarwari, warware taƙaddama da kuma kare buƙatun jama’a (musamman haƙƙin abokan ciniki).

3. Hukumar tana da ikon ɗaukar irin ma’aikatan da take buƙata da biyansu albashi da alawus-alawus da iya rike su da karfafa su.

Sashi na 43 ya baiwa hukumar ikon biyan kwamishinoni irin waɗannan albashi da alawus kamar yadda suka tsara, tare da la’akari da shawarar hukumar albashi da ma’aikata ta ƙasa. A yayin bayar da shawarwari ga hukumar, hukumar kula da ma’aikata ta ƙasa, da tattalin arziki, da ma’aikata ta yi la’akari da ka’idoji kamar haka:

  • Yanayin aikin hukumar
  • Buƙatar dogaro da kai na kuɗi ga kwamishinonin
  • Albashin da aka biya ga ɗaiɗaikun mutane ƙwararru, masu gogewa, da ƙwarewa a cikin kamfanoni masu zaman kansu
  • Yanayin kashe kuɗin kwamishina
  • Irin waɗannan la’akari na iya zama dole don cimma daidaiton albashi da alawus-alawus ga kwamishinoni.

Ta hanyar tanadin doka, hukumar tana da hakkin amincewa da albashin da ya dace ga kwamishinonin bayan ta yi la’akari da shawarwarin da hukumar kula da ma’aikata ta ƙasa ta bayar na albashi da kuɗaɗen shiga. A bisa dokar ne kwamishinonin farko suka amince da albashi da alawus na ma’aikata da su kansu.

Hukumar ta yi imani da gaske game da darajar da tsarin gudanarwarta ya haifar ga kasuwancin wutar lantarki da za ta iya bunƙasa da kuma samun tabbacin hakan. Hukumar tana gudanar da ayyukanta yadda ya kamata tare da fa’idar dokokin ‘yancin kai da aka tanada a cikin dokarta. Yayin da kasuwancin lantarki ke ci gaba, ana fatan hukumar za ta iya cire kanta gabaɗaya daga kuɗaɗen tallafin da gwamnati ke bayarwa.

Kamfanin (TCN) na Najeriya

Kamfanin dakon lantarki na Najeriya (TCN) ne ke kula da hanyoyin dakon wutar lantarki a ƙasar. A halin yanzu TCN mallakar gwamnati ne kuma tana sarrafa shi, kuma ayyukan da aka ba shi lasisin aiwatarwa sun haɗa da watsa wutar lantarki, tsarin aiki, da kula da GenCos da kuma turawa zuwa kamfanonin rarrabawa wato DisCos.

TCN ya ƙunshi manyan tashoshin wutar lantarki tare da jimullar ƙarfin watsawa da ya kai megawatt 7,500 da sama da kilomita 20,000 na hanyoyin watsawa. A halin yanzu, ƙarfin isar da (megawatt 5,300) ya fi matsakaicin ƙarfin aiki na megawatt 3,879, amma ya yi ƙasa da jimillar ƙarfin da aka samar na megawatt 12,522.

Ayyukan hukumar TCN

Dangane da tarihin TCN, hukumar ta ƙunshi sassan aiki guda uku.

1. Transmission provider 

Sa ido, kulawa, da faɗaɗa kayan aikin watsawa. Ita ce ke da alhakin tsara hanyoyin rarraba wutar lantarki na ƙasa da matsakaitan layin wutar lantarki da samar da ayyukan rarrabawa.

2. System operations 

Ita ce hukumar da ke sarrafa ayyukan wutar lantarki tun daga tsarawa zuwa ga kamfanonin rarrabawa. Ayyukan wannan sashin sun haɗa da rarraba wutar lantarki, sarrafa alƙaluman grid, ƙarfin lantarki da sarrafa bangarori, jigilar tattalin arziƙi na kamfanonin tsarawa, da kula da ayyuka da sauransu.

3. Market operations

TCN ce ke gudanar da ka’idojin kasuwanci na NESI. Ita ce ke da alhakin aiwatar da kasuwancin wutar lantarki da kuma inganta kasuwar makamashin lantarki a Najeriya.

Kalubale da matsalolin wutar lantarki a Najeriya

Akwai ƙalubale da matsaloli da dama da suka dabaibaye samarwa da rarraba wutar lantarki tsawon shekaru a Najeriya; wasu daga cikin waɗannan ƙalubalen suna da alaƙa da samarwa, rarrabawa, da sauran matsalolin gama-gari.

Matsalolin da ke tattare da watsawa

Tsarin watsawa ko dakon wutar lantarki a Najeriya bai shafi dukkan ɓangarorin ƙasar ba. A halin yanzu ƙasar na da ƙarfin rarraba kusan megawatt 4,000, kuma tana da raunin amfani da fasaha, don haka akwai matukar damuwa da ƙalubale. A taƙaice, manyan matsalolin da aka gano su ne:

  • Fasahar da ake amfani da ita gabaɗaya tana da rauni da ƙarancin kuzari.
  • Akwai rashin isassun kayan aikin tunkuɗawa da watsa makamashin lantarki cikin inganci.
  • Gwamnatin tarayya ce ke tallafa wa fannin lantarki da kuɗaɗe, wanda kuma wannan kuɗi sun yi kaɗan wajen biyan buƙatun ma’aikatar lantarki ta ƙasa.
  • Har yanzu dai makamashin wutar lantarki bai kai ga sassa da dama na ƙasar ba.
  • Matsakaicin ƙarfin wutar lantarki a halin yanzu shi ne megawatt 4,000, wanda ya yi ƙasa da buƙatun al’ummar ƙasar.
  • Wasu ɓangarorin grid sun tsufa sosai kuma ba a sauya su ba.
  • Gwamnatin tarayya ba ta da kuɗin da ake buƙata wajen faɗaɗawa akai-akai da sabuntawa da kuma kula da hanyar rarrabawa.
  • Ana samun lalacewar hanyoyin rarraba lantarki akai-akai, wanda ke da alaƙa da rashin sa ido da tsaro a kan duk kayan lantarki.
  • Akwai rashin fasahar zamani da ake buƙata don sadarwa da sa ido.
  • Taransifomomin da aka girka a yawancin wuraren da ake amfani da makamashin lantarki sosai suna da cinkoso, lodi ya yi musu yawa, sun yi kaɗan.
  • Akwai rashin isassun kayayyakin gyarawa da kulawar gaggawa ga na’urori da sauran kayan aiki.
  • Rashin ɗaukar ƙwararrun ma’aikata, gine-gine mara inganci da rashin ba wa ma’aikatan bita horo su ma matsaloli ne da ke addabar fannin lantarkin Najeriya.

Matsalolin kasuwanci da rarrabawa

A mafi yawan wurare a Najeriya, hanyoyin rarraba wutar lantarki ba su da kyau, tsarin wutar lantarkin ba shi da inganci, kuma lissafin mita ko kuɗin wutar ba daidai ba ne. A matsayin wani sashen, wanda ke hulɗa da jama’a, akwai buƙatar tabbatar da isassun hanyoyin rarrabawa da samar da wutar lantarki mai inganci baya ga ingantaccen tsarin kasuwanci da kuma isar da buƙatun abokin ciniki. A taƙaice, wasu manyan matsalolin da aka gano sun haɗa da:

  • Rashin kyakkyawan tsarin biyan kuɗaɗen lantarki.
  • Munanan ayyuka da ɗabi’u daga ma’aikata da rashin kyakkyawar dangantaka da jama’a.
  • Rashin isassun kayayyakin buƙata na ma’aikatar, kamar kayan aiki da motocin zirga-zirga.
  • Rashin inganci da ƙarancin hanyoyin sadarwa.
  • Yawancin taransifomomi suna ɗauke da lodi mai yawa a kansu.
  • Gajiyayyun hanyoyin rarraba wutar lantarki.
  • Gurɓatattun halayen ma’aikata da rashin horo na musamman.
  • Rashin isassun kuɗaɗen don ayyukan kulawa da gyare-gyare na’urori.

Matsalolin wutar lantarki na gama-gari

Daga cikin matsalolin da aka ambata a baya, yanzu ga wasu daga cikin manyan ƙalubalen da fannin wutar lantarki ke fuskanta, da ke da nasaba da ƙarancin samar da wutar lantarki, da matsalolin rarraba wutar lantarki a Nijeriya gabaɗaya:

  • Rashin ɗorewar dangantaka da aiwatarwa tsakanin gwamnatin tarayya da sauran masu ruwa da tsaki, musamman kamfanonin mai na ƙasa da ƙasa na JV da masu samar da wutar lantarki (IPP).
  • Rashin amfani da kadarorin da ke akwai da kuma jinkirin kulawa da gyarawa.
  • Jinkiri wajen aiwatar da sabbin ayyuka.
  • Rashin isasshiyar wutar lantarki a sabbin tashohin da aka kammala ginawa.
  • Gwamnatin tarayya, kasancewar ita ce kaɗai ke samar da kuɗaɗe don faɗaɗa tsarin lantarkin ƙasa, ba ta iya samar da kuɗaɗen da ake buƙata na fadadawa, sabuntawa, zamanantarwa da kuma kula da fannin akai-akai.
  • Yawaitar lalata bututun iskar da layukan kebul yana da alaƙa da rashin sa ido da tsaro a kan duk kayayyakin lantarki.
  • Yawaitar ƙarancin kayan aiki, kamar motocin zirga-zirga, da kayayyakin gyaran wutar lantarki.
  • Rashin amfani da fasahar zamani da ake buƙata don sadarwa da sa ido kan samarwa, watsawa, da kayayyakin rarrabawa.
  • Rashin sarrafa albarkatun iskar gas na cikin gida don samar da wutar lantarki.
  • Har yanzu National Grid bai mamaye sassa da yawa na ƙasar ba.
  • Matsakaicin ƙarfin wutar lantarki a yanzu shi ne megawatt 4,000, wanda yayi ƙasa da yadda ake buƙata.
  • Wasu sassa na National Grid sun tsufa, kayan aiki ba su da inganci sannan babu kulawa da gyarawa

Mafita ga matsalolin wutar lantarki

Idan ana son magance ƙalubalen da aka ambata a sama, ana bukatar tsauraran dabaru masu inganci, musamman yadda samar da makamashi, watsawa, da rarrabawa a Najeriya zai samun ci gaban da ya dace. Ana buƙatar cikakken nazari game da aiki da tsarin gudanarwar fannin wutar lantarki don  inganta shi. A wannan yanayin, ya kamata a yi la’akari da:

  • Ya kamata a samar da cikakken tsarin samar da wutar lantarki, watsawa da rarrabawa ga ‘yan Nijeriya na tsawon shekaru 25 masu zuwa.
  • Ana buƙatar cikakken bayani game da inganta aikin tsarin samar da wutar lantarki bisa tsarin jiha-da-jiha.
  • Ya kamata a gudanar da cikakken nazarin buƙatun ƙasa da nufin samar da ingantattun bayanai kan abubuwan da ake buƙata na wutar lantarki a yanzu da cikakkun bayanai da kuma hasashen shekaru 25 masu zuwa.
  • Dole ne a samar da dabarar raba farashi ga dukkan matakan gwamnati don samun cikakkiyar damar bunƙasa samar da wutar lantarki a ƙasa.
  • Tsarin hukumomi kan yadda ɓangaren wutar lantarki zai yi aiki tare da gwamnatin tarayya a matsayin cibiyar aiwatarwa ta tsakiya, da aiki tare da jihohi da ƙananan hukumomi, ya kamata a inganta shi.
  • Ya kamata a fitar da tsarin rawar da jihohi ke takawa a fannin makamashin lantarki, musamman da ake buƙata don zama cibiyar sa ido kan gudummawar albarkatun ƙasa.

Kammalawa

Kamfanonin samarwa, watsawa, da rarrabawa suna aiki tare don samar da makamashin wutar lantarki ga gidaje, kasuwanni, da masana’antu na Najeriya, kodayake suna aiki mabanbanta. Kawo yanzu mun tabbata an fahimci bambance-bambancen da ke tsakaninsu da kuma yadda suke dogaro da juna, da fatan an samu kyakkyawar fahimtar yadda suke aiki don ci gaban ƙasa Najeriya.

Manazarta

Nigeria Electricity Sector – Energypedia. (n.d.).

Onuoha, K. (2016). The Electricity Industry in Nigeria: What are the Challenges and Options Available to Improve the Sector? SSRN Electron. J., no. May 2010, 2016.

Saunders, T. (2023). Who discovered electricity? Probably not who you’re thinking. BBC Science Focus

Simbi. (2023, May 30). Understanding the differences between transmission, distribution, and power generating companies in Nigeria. BuyPower.ng Blog. Retrieved December 6, 2024

Sule, A.H. (2010). Major Factors Affecting Electricity Generation, Transmission, and Distribution in Nigeria.

The Nigeria Electricity System operator. (n.d.).

Transmission Company of Nigeria. (n.d.).

Was this article helpful?
YesNo