Skip to content

Tarihi, alfanu da matsalolin tallafin man fetur a Nigeria

Tallafin man fetur a Nigeria

Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa samar da ɗanyen mai a Afirka; sai dai kuma duk da wannan yawan arzikin man fetur ɗin, ƙasar na shigo da kusan kashi 70% na tataccen mai daga waje har kawo wannan shekarar da muke ban-kwana da ita na 2024, sakamakon yawancin matatun man ƙasar sun durƙushe ba sa iya aikin tace man da zai wadatar da buƙatar ƙasar. Bayan haka ƙasar na fuskantar matsalar tattalin arzikin da ke da alaƙa da taƙaddamar cire tallafin mai. Masu sharhi kan al’amuran yau da kullum na alaƙanta waɗannan matsaloli da rashin gudanar da abin da ya dace a fannin man fetur da kuma illar rashin kyakkyawan shugabanci na tsawon shekaru da ke addabar ƙasar. Najeriya ta kwashe shekaru da yawa tana ba da tallafin man fetur domin tabbatar da cewa ‘yan ƙasar suna sayen man a farashi mai rahusa. Sai dai abin lura a nan shi ne; tallafin man fetur yana da alfanu da kuma naƙasu. To mene ne alfanun da naƙasun? Kuma ta ya ya suke shafar yanayi da walwalar al’ummar ƙasar? Waɗannan su ne wasu daga cikin tambayoyin da za mu yi ƙoƙarin amsawa a wannan maƙala.

Mene ne tallafin man fetur?

A sauƙaƙe tallafin man fetur na nufin wani taimakon kuɗi da gwamnati ke bayarwa don rage tsadar farashin mai ga masu amfani da shi. Ana saka tallafi ne don rage farashin man fetur da mayar da shi mafi araha da sauƙi ga al’umma.

A wata mahangar kuma, ana iya bayyana tallafin man fetur da cewa, tallafin kuɗi ne da gwamnati ke shigarww cikin harkar man fetur don rage farashin mai ga jama’a. Wannan tallafin yana sauƙaƙa farashin man fetur a gindin famfo fiye da yadda farashin yake a kasuwa. Wannan na faruwa dalilin gwamnati ta ɗauke nauyin wani kaso na farashin don man ya zama mai sauƙi ga kowa.

Tallafin man fetur wani rangwame ne da gwamnati kan ɗora a asalin farashin man fetur na kasuwanni domin mutane su saya a ƙasa da farashin kasuwanni. Yayin da aka samar da tallafi, masu amfani da man fetur za su saya ƙasa da farashin kasuwa a kowace litar man.

Me ake nufi da cire tallafin man fetur

Cire tallafin man fetur a sauƙaƙe shi ne wani tsari da gwamnati take ɗauka domin kawo ƙarshen bayarwa ko saka tallafin kuɗi ga man fetur, hakan na haifar da farashin man ya tashi zuwa ga asalin farashin kasuwa. Wannan mataki na yana haifar tasiri sosai ga tattalin arziki da walwalar al’umma.

Tallafin man fetur a Najeriya ya fara ne tun a cikin shekarun 1970 a sakamakon tashin farashin gwauron zabin da man fetur ya yi a shekarar 1973. Tallafin dai an aiwatar da shi ne don daidaita farashin man fetur ga ‘yan ƙasa, ya kasance ƙasa da farashin ƙasa da ƙasa, an yi amfani da dukiyar gwamnati ne wajen cike giɓin bambancin don rage tasirin hauhawar farashin man fetur a duniya ga ‘yan ƙasa Najeriya.

Tattalin arzikin Najeriya ya dogara da kaso mai yawa a kan ɗanyen mai. Sannan kuma, rashin samar da tsayayyar wutar lantarki a kodayaushe, ya tilasta wa  magidanta da masu ƙananan sana’o’i dogara da janareta, waɗanda ke kwankwaɗar makamshin mai sosai. An samar da manufar ba da tallafin man fetur a Najeriya a matsayin wata hanya ta daidaita farashin man fetur har sai masana’antun cikin gida sun inganta.

Tarihin cire tallafin man fetur a Najeriya

‘Yan Najeriya sun sha fuskantar tsadar man fetur a tsawon shekaru da dama, tun daga kan kobo 6 kacal a shekarar 1973 zuwa Naira 617 a kowace lita a shekarar 2023. A tsawo lokaci, gwamnatoci da dama sun ciccire tallafin man fetur a ƙasa Najeriya kamar yadda za a gani a bayanan da ke ƙasa;

• Shekarun 1973 zuwa 1999

Gowon (1973-1976): Farashin man fetur ya ƙaru daga kobo 6 zuwa kobo 9 saboda yawaitar buƙatar man fetur a duniya.

Obasanjo (1978-1982): Dalilan matsalolin tattalin arziki sun haifar da ƙarin farashin man fetur mai yawa daga kobo 9 zuwa kobo 20, wanda ya shafi harkar sufuri.

Babangida I & II (1986-1991): Canje-canje tsarin tattalin arziki don dacewa da yanayin duniya ya haifar da ƙarin kashi 97.5%, wannan ƙari ya shafi harkokin sufuri.

Shonekan da Abacha (1993–1999):  Taɓarɓarewar tattalin arziki a lokacin mulkin Shonekan ta haifar da ƙarin kashi 614.29 cikin 100 a tsawon wa’adinsa na kwanaki 82, yayin da Abacha ya fuskanci koma-baya, ciki har da faɗuwar farashin mai a shekarar 1993 da kuma ƙari mai yawa daga baya.

• Zamanin Obasanjo daga 2000 zuwa 2007

Obasanjo I (2000): An samu ƙarin tallafin kashi 50 cikin ɗari, wanda ya yi tasiri sosai ga sufuri; amma a cikin shekarar 2003, ya cire tallafin, wanda ya haifar da ƙarin farashin. Kazalika, a dai cikin shekarar 2003, a ƙarƙashin mulkin Obasanjo din, an sake cire tallafin da ya janyo ƙarin kashi 61.54%, wanda ya yi tasiri kai tsaye ga kuɗaɗen sufuri.

Haka nan kuma, a lokacin Obasanjo, a cikin shekarar 2004, ya maido da tallafin, amma karuwar kashi 30% ya nuna ma’auni mai zurfi tsakanin bukatun cikin gida da sauye-sauyen tattalin arziki na duniya, wanda ya shafi farashin sufuri.

• Shekarun 2007 zuwa 2015

Shugaba Yar’Adua (2007): Ya rage kashi 15.39%, wannan ya nuna ƙoƙarinsa na daidaita farashin wanda ya sauƙaƙa harkokin sufuri. Yar’adua ya ciri tuta saboda kasancewarsa shugaba ɗaya tilo da ya tabbatar da daidaiton farashin man fetur a lokacin gwamnatinsa.

Jonathan I (2012): Kuɗaɗen sufuri sun ƙaru sosai da matsin tattalin arziki, sakamakon ƙarin kashi 116.92 cikin 100 bisa cire tallafin da ya yi, wanda ya haifar da zanga-zanga a Najeriya.

Jonathan II (2012-2015): A wani abu da ake dangantawa da siyasa, Jonathan ya dawo da tallafin wanda ya haifar da sauyi, tare da raguwar farashin da kaso 10.31% a 2015, wanda ya taimaka wajen rage farashin sufuri.

• Zamanin mulkin Buhari 2015 zuwa 2023

Buhari (2016): An samu ƙarin kashi 66.67 cikin 100 ne sakamakon yadda kasuwar man fetur ta duniya ta yi tasiri, wanda ya shafi harkokin sufuri.

Wa’adin Buhari (2015-2023): Yayin da matsalolin tattalin arziki suka ci gaba da faruwa, a shekarun baya an samu ƙarin kashi 124% wanda ya shafi harkar sufuri.

• Zamanin Tinubu 2023

Tinubu (Mayu 2023): Farashin kuɗaɗen sufuri ya yi ƙaru sosai sakamakon cire tallafin nan take da shugaban ya yi, wanda ya sa farashin hawa sosai daga N195 zuwa N540 kowace a kan kowace lita a watan Yuni da kuma farashin da ba a taɓa gani ba wanda ya kai N617 a kowace lita a watan Yuli.

Sauye-sauyen farashin man fetur a Najeriya

Shekarun 1973 zuwa 1999

  • Gowon (1973): 6k zuwa 8.45k (40.83%)
  • Murtala (1976): 8.45k zuwa 9k (6.5%)
  • Obasanjo (1978): 9k zuwa 15.3k (70%)
  • Shagari (1982): 15.3k zuwa 20k (30.72%)
  • Babangida I (1986): 20k zuwa 39.5k (97.5%)
  • Babangida II (1988): 39.5k zuwa 42k (6.33%)
  • Babangida III (1989): 42k zuwa 60k (42.86%)
  • Babangida IV (1991): 60k zuwa 70k (16.67%)

Shekarun 1993 zuwa 2003

  • Shonekan (1993): 70k zuwa N5 (614.29%)
  • Abacha I (1993): N5 zuwa N3.25k (Farashin ya ragu 35%)
  • Abacha II (1994): N3.25k zuwa N15 (361.54%)
  • Abacha III (1994): N15 zuwa N11 (Farashin ya ragu 26.67%)
  • Abubakar I (1998): N11 zuwa N25 (127.27%)
  • Abubakar II (1999): N25 zuwa N20 (Farashin ya ragu 25%).

2000-2007: Sauye-sauyen Obasanjo

  • Obasanjo I (2000): N20 zuwa N30 (50%)
  • Obasanjo II (2000): N30 zuwa N22 (Farashin ya ragu 26.67%)
  • Obasanjo III (2002): N22 zuwa N26 (18.18%)
  • Obasanjo IV (2003): N26 zuwa N42 (61.54%)
  • Obasanjo V (2004): N42 zuwa N50 (19.05%)
  • Obasanjo VI (2004): N50 zuwa N65 (30%)
  • Obasanjo VII (2007): N65 zuwa N75 (15.39%)

2007-2015: Sauye-sauye da matakin ƙarshe

  • Yar’Adua (2007): Ya rage farashin zuwa N65 (Farashin ya ragu 15.39%)
  • Jonathan I (2012): N65 zuwa N141 (116.92%)
  • Jonathan II (2012): N141 zuwa N97 (Farashin ya ragu 31.21%)
  • Jonathan III (2015): N97 zuwa N87 (Farashin ya ragu 10.31%)

2015-2023: Zamanin Buhari

  • Buhari (2016): N87 zuwa N145 (66.67%)
  • Wa’adin Buhari na biyu (2015-2023): N87 zuwa N195 kowace lita (124%)

2023: Zamanin Tinubu

  • Tinubu (2023): N195 zuwa N557
  • Tinubu (2023): N557 zuwa N617

Sakamakon cire tallafin man fetur

Ana iya bayyana sakamakon cire tallafin-man fetur ga tattalin arzikin Najeriya ta ɓangarori biyu, wato alfanu da rashin alfanu.

Alfanun cire tallafin man fetur

Abuchi (2023) ya bayyana wasu kyawawan fa’idojin cire tallafin man fetur ga tattalin arzikin Najeriya.

1. Inganta ababen more rayuwa na jama’a

Muhimmin alfanun ga tattalin arziki da ke tattare da cire tallafin man fetur a Najeriya shi ne, kuɗaɗen da ake amfani da su wajen biyan tallafin man fetur za a iya juya su wajen bunƙasa muhimman ababen more rayuwa a Najeriya. Masana a fannin tattalin arziki sun yi ittifaƙin cewa za a iya amfani da kuɗaɗen da ake amfani da su don biyan tallafin wajen inganta ababen walwalar jama’a.

Rashin isassun kuɗaɗen yana sa gwamnati ta ciwo basussuka masu tarin yawa domin gudanar da kasafin kudin. Amma tare da cire tallafin man fetur a shekarar 2023, gwamnati na iya amfani da waɗannan kuɗaɗe yadda ya kamata don haɓaka muhimman ababen more rayuwa a Najeriya.

2. Cike gibin kasafin kudi da samar da rarar kuɗaɗe

Wani ingantacce alfanun cire tallafin man fetur ga tattalin arziki shi ne, za a yi amfani da kuɗaɗen don cike giɓin kasafin kuɗin da ake ciki. Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa tallafin man fetur na taimakawa wajen cike giɓin kasafin kudin Najeriya. A tarihi Najeriya ta cike giɓin kasafin kudi a cikin shekaru 10 da suka wuce.

A baya-bayan nan, an biya tallafin man fetur ɗin da ya laƙume Naira Tiriliyan 4 a shekarar 2022 da kuma Naira Tiriliyan 17 a shekarar 2023, yayin da kasafin kudin 2023 da aka amince da shi ya kasance Tiriliyan 21.83 kacal. Wannan yana nuna cewa tallafin man fetur zai cinye kusan kashi 77% na kasafin kudin, wanda tuni ya jefa Najeriya cikin gibin kasafin kudin da zai kai Najeriya ga shiga kunci da talauci. Baya ga haka, kashi 90% na kuɗaɗen shigar Najeriya ana amfani da su ne wajen biyan basussukan ƙasashen waje, wanda ya ƙara dagula al’amuran kuɗin Najeriya. Haƙiƙa cire tallafin man fetur na baya-bayan nan abu ne mai kyau ga tattalin arzikin Najeriya domin ya rage gibin kasafin kuɗi a halin yanzu ta yadda za a yi amfani da Naira Tiriliyan 17 wajen ƙara kasafin kuɗin ƙasar. Kuma bayan lokaci, Najeriya za ta iya samun rarar kasafin kuɗi.

3. Inganta sauran bangarori

Baya ga bunkasa muhimman ababen more rayuwa a Najeriya, cire tallafin man fetur na iya ‘yantar da albarkatun kuɗi don ci gaban sauran bangarorin da ke bukatar sa hannun gwamnati da kuɗaɗe masu yawa. Kuɗaɗen da za a yi amfani da su wajen biyan tallafin man fetur za a iya sanya su a sassa kamar su noma, kiwon lafiya, yawon bude ido, ilimi, da kuma samar da kuɗaɗen aiwatar da dokar lamuni ga dalibai.

4. Samun damar yin aiki

Wata manufa mai kyau ta cire tallafin man fetur ita ce, za a samar da ayyukan yi. Wannan tsari zai ba da dama ga kamfanoni da yawa su shigo da mai a farashi mabanbanta wanda zai haifar da gasa. Waɗannan kamfanoni za su ɗauki ma’aikata, ta yadda za su samar da ayyukan yi. Haka kuma, sake farfado da matatun mai na cikin gida Najeriya zai haifar da samar da ayyukan yi. Haka kuma, matatar mai ta Dangote da ta fara samar da man fetur, ta samar da ayyukan yi kai tsaye sama da 10,000 a Legas kadai da sama da 30,000 na ayyukan yi kai tsaye a faɗin Najeriya.

5. Rage rancen gwamnati

Tun lokacin da aka fara bayar da tallafin man fetur, gwamnatin Najeriya ke karɓo rance, kuma lamunin ya ƙara taɓarɓarewa a lokacin koma bayan tattalin arziki a shekarar 2016 da kuma annobar cutar COVID-19 ta shekarar 2020. Ba da jimawa ba, a cikin shekarar 2022, gwamnati ta ci gaba da karɓo rance daga Babban Bankin Najeriya (CBN) ta hanyoyi daban-daban don biyan tallafin man fetur. Gwamnati ba ta da wani zaɓi illa ta ƙara yawan rance daga babban bankin ƙasar. Gwamnatin tarayya ta karɓi bashin babban bankin kasar har dala tiriliyan 22.7, wanda a kwanakin baya majalisar dokokin kasar ta amince a shekarar 2023. Cire tallafin man fetur da aka yi a baya-bayan nan na nuni da cewa bashin da gwamnati ke karba daga babban bankin zai ragu ainun, saboda kuɗaɗen da aka ceto daga mai, cire tallafin zai zama hanyar samun kuɗi ga gwamnati.

6. Sauƙaƙa harkokin canjin kuɗaɗe

Sakamakon cire tallafin man fetur, ya kamata gwamnati ta bar matatun mai na cikin gida su ƙara samar da ɗanyen mai da sauran albarkatun man fetur. Hakan zai rage shigo da man fetur daga ƙasashen waje, zai kuma ƙara fitar da man da ake sarrafawa a cikin gida. Hakan kuma zai ƙara yawan kuɗaɗen ƙasashen waje daga man fetur da ake shigowa da su daga waje da kuma ƙara samun kuɗaɗen waje daga man fetur da ake fitarwa. Yawaitar kuɗaɗen ƙasashen waje zai ƙara samar da kuɗaɗen musaya a kasuwannin canji da kuma inganta Naira a kan dalar Amurka. Hakan kuma zai haifar da darajar Naira da kuma inganta canjin canji. Misali, matatar Ɗangote, mai ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana, za ta iya biyan buƙatun cikin gida na Najeriya da rage shigo da mai, da samar da rarar da za a iya fitarwa zuwa ƙasashen waje. Don haka gwamnati za ta iya ceto biliyoyin daloli da ake kashewa wajen shigo da man fetur daga ƙasashen waje, kuma za a iya amfani da irin waɗannan kuɗaɗen da aka tara wajen rage matsin tattalin arziki da kuma inganta harkokin ciniki.

7. Rage dogaro da man fetur da ake shigo da shi daga waje

Idan cire tallafin man fetur ya biyo bayan sake farfaɗo da matatun mai a cikin gida, hakan zai iya zaburar da matatun cikin gida don samar da ƙarin albarkatun man fetur da kuma rage dogaron da Najeriya ke yi kan man da ake shigo da shi daga waje. Idan aka yi la’akari da sabuwar matatar Ɗangote, tana da ƙarfin tace ganga 650,000 a kowace rana, wanda ya isa ya biya buƙatun cikin gida na Najeriya na albarkatun mai, da samar da rarar fitar da man zuwa ƙasashen waje, da kuma rage shigo da mai sosai. Baya ga matatar Ɗangote, sauran matatun man na cikin gida su za su ƙara inganta ayyukan tace man.

8. Ƙarancin iskar carbon

Kasancewar tallafin man fetur a cikin shekaru goma da suka gabata ya ƙarfafa ayyukan tattalin arziki masu alaƙa da man fetur wanda da ke ƙara gurbatar iska da hayakin Carbon a Najeriya. Lalacewar CO2 a Najeriya, ta wani ɓangare ya danganta da tallafin man fetur da ake bayarwa, ya tashi daga dalar Amurka biliyan 1.5 a shekarar 1998 zuwa dalar Amurka biliyan 5.23 a shekarar 2021. Cire tallafin man fetur a Najeriya zai taimaka wajen daƙile sauyin yanayi da ake ci gaba da samu da kuma rage gudumawar da Najeriya ke bayarwa ga gurbacewar iska da yanayi a duniya. Cire tallafin mai a Najeriya zai kuma rage bukatu da wadatar albarkatun mai, ta yadda za a rage hayakin carbon. a Najeriya.

9. Rage cin hanci da rashawa

Wani ƙarin alfanun da ke tattare da cire tallafin man fetur shi ne, zai iya kawo ƙarshen almundahana a cikin kuɗaɗen tallafin man fetur (Itumo & Onyejiuba (2019). Wani ra’ayi na cewa tallafin man fetur wani shiri ne na ci gaba da karkatar da kuɗaɗen ƙasashen waje da Najeriya ke samu zuwa wasu asusun masu zaman kansu a ketare. Bayanai na baya-bayan nan sun nuna cewa farashin ɗanyen mai a duniya bai tashi da yawa ba, amma yawan ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya karu, ana samar da ganga miliyan biyu a kowace rana. Amma duk da haka, ana ci gaba da samun rahoton raguwar kudaden asusun ajiyar Najeriya a waje. Shin mene ne ya haifar da wannan? Cin hanci da rashawa su amsa ga wannan tambaya. Misali, ɗan-kasuwa mai shigo da mai daga waje, zai shigo da metrik tan goma sha biyar kacal na man fetur, amma sai ya je hukumar kula da farashin man fetur da ke Abuja, ya bayar da rahoton cewa ya shigo da metrik tan saba’in da biyar. Masu shigo da man sukan haɗa baki da wasu jami’an hukumar ta PPPRA domin su samu nasu kason daga cikin metric ton sittin da aka ƙara a matsayin almundahana. Wannan cin hanci da rashawa gagarumi da ake tafkawa a harkokin man fetur. Saboda haka cire tallafin man fetur, irin wannan cin hanci da rashawa zai zamo tarihi.

Matsalolin cire tallafin man fetur

Naidoo (2023) ya bayyana wasu matsalolin cire tallafin mai ga tattalin arzikin ƙasa Najeriya.

1. Tashin farashin man fetur

Cire tallafin man fetur ya haifar da tashin farashin man fetur. Wannan ya janyo ƙarancin buƙatar man fetur da raguwar yawan man da ake sayarwa. Raguwar bukatun ta rage ribar ƙananan ‘yan kasuwa da ke dogaro da man fetur. Kowa zai jin raɗaɗin hakan, amma kodayaushe talaka shi ne ke fin shan wahala. Sai dai akwai ra’ayin da ke cewa cire tallafin man fetur a shekarar 2023 zai kawo gasa a tsakanin masu sayar da man fetur kuma gasar za ta sa farashin man ya sauka, amma wannan hasashen ilimi ne kawai kuma ba zai tabbata a kwana kusa ba saboda farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, shike tantance farashin man fetur a Najeriya. Abin nufi a nan shi ne, hauhawar farashin man fetur a halin yanzu za ta ci gaba da kasancewa a haka har tsawon lokaci.

2. Koma baya ga tattalin arziki

Wani mummunan tasirin tattalin arziki na cire tallafin man fetur shi ne, koma baya ga tattalin arziki. Cire tallafin man fetur zai haifar da tashin farashin kayayyaki da ayyuka masu mahimmanci. Sakamakon haka, za a samu raguwar kuɗin shiga da ake karɓa a hannun ɗaiɗaikun mutane da masu ƙananan sana’o’i saboda tashin farashin kayayyaki, ƙarancin albashi, da ƙayyade mafi karancin albashi na ƙasa. Wannan zai haifar da raguwar kashe kuɗaɗen amfanin yau da kullum, kuma zai haifar da ja baya ga buƙatun gabaɗaya.

3. Ƙarin talauci da fatara

Cire tallafin man fetur zai ƙara talauci cikin ƙanƙanin lokaci. Zai haifar da jin zafi da raɗaɗi da yunwa ga jama’a. A matakin mutum ɗaya, cire tallafin man fetur, ba tare da wani abin jin daɗi ba, zai haifar da ƙarancin kuɗaɗe da ƙarancin abinci a ƙasa da ƙarancin magunguna ga marasa lafiya da rashin samun ilimi ga sassa da dama, musamman a yankin arewacin Najeriya. Mutane da yawa za su shiga yunwa, yawancin yara. Talakawa da matsakaita za su rasa damar sayen abubuwan buƙatun rsuuwa, kuma ƙananan ’yan kasuwa za su fuskanci tawaya cikin ribarsu saboda tsadar kayayyaki. Kuma idan sun yi ƙoƙarin ƙara kuɗi ga masu sayen kaya, masu sayen za su ƙi saya ko kuma za su rage adadin da suke son saya, wanda hakan zai haifar da ƙarancin ciniki. Bugu da ƙari kuma, cire tallafin man fetur zai iya shafar matalauta, marasa galihu idan babu wani kyakkyawan tsarin tattalin arziki ko shirye-shiryen taimakawa jama’a wanda zai iya rage matsalolin tattalin arziki da kunci da cire tallafi kan haifar.

4. Tashin hankali da zanga-zanga

Wani mummunan tasirin cire tallafin man fetur shi ne, afkuwar zanga-zanga da tashin hankali a cikin al’umma. Tashin farashin man fetur na iya janyo zanga-zanga. Idan farashin ya ci gaba da hauhawa, za a kai magidanta masu ƙaramin ƙarfi bango, a wannan lokacin ba su da wata hanya face su shiga zanga-zangar tayar da zaune tsaye don ganin gwamnati ta sauya ƙudirin cire tallafin man fetur.

5. Hauhawar farashin kayan masarufi

Cire tallafin man fetur ya haifar da ƙaruwar farashin man fetur daga farashin da aka sa wa tallafi na ₦190 a watan Mayun 2023 zuwa farashin da ba a saka tallafi ba na ₦537 a watan Yunin 2023 da kuma ₦617 a watan Yulin 2023. A halin da ake ciki kuma farashin man fetur na iya hauhawa sama da ₦600 a wasu yankuna masu nisa a arewa, kamar jihar Borno, saboda tsadar sufuri. Wato farashin mafi yawan kayan masarufi da masana’antu, waɗanda ake samarwa ko jigilar su da man fetur, za su ƙaru sosai. Farashin biredi zai karu, haka nan kuma farashin sufurin cikin gida zai ƙaru, wanda hakan zai sa ya yi tsada ga talakawa da masu ƙaramin ƙarfi. Hakan zai shafi har  masu hannu da shuni, amma kamar kullum, talakawa za su fi shan wahala ta hanyar ƙarancin kuɗaɗe a hannunsu.

6. Fasa-ƙwaurin man fetur

Karin farashin man fetur bayan cire tallafin na iya haifar da fasa-ƙwaurin mai mai rahusa zuwa Najeriya daga ƙasashen makwabta, kamar yadda mutane suka riƙa yin fasa-ƙwaurin man fetur ɗin Najeriya cikin sauƙi zuwa jamhuriyar Nijar kafin cire tallafin. Idan aka cire tallafin man fetur, ana iya samun karuwar safarar man mai sauki zuwa yankunan karkarar Najeriya, saboda da yawa daga cikin mutanen karkara ba sa iya sayen mai kan kuɗi Naira 537.

7. Rashin ayyuka

Cire tallafin man fetur kan haifar da asarar ayyuka a fannin da ba na yau da kullun ba, wanda ya dogara da PMS ko mai. Ɓangaren yau da kullun na amfani da makamashin dizal don ayyukansu, yayin da ɓangaren da ba na yau da kullun ya dogara da man fetur. Tashin farashin mai zai kai ga rufe ƙananan sana’o’in da ba za su iya sayen man fetur da tsada ba, kuma ribar da suke samu gabaɗaya ta samu naƙasu dalilin cire tallafin man fetur a ɓangaren mu’amalar yau da kullum.

8. Yawaitar aikata laifuka

Akwai hasashen karuwar aikata laifuka. Ƙarin farashin man fetur bayan cire tallafi na iya haifar da wasu laifuka, kamar satar mai daga rumbunan ajiya na matatun mai, motocin mutane, gidajen mai, da na injinan janaretocin mutane. Aikata laifukan na iya ƙara taɓarɓarewa yayin da wasu ‘yan Najeriya ke fafutukar ganin sun samu biyan buƙatansu.

Kammalawa

Tallafin man fetur a Najeriya yana fa’idoji da matsalolin da ke da tasirin kai tsaye ta fuskar tattalin arziki, zamantakewa da siyasa. Yayin da cire tallafin kan ba da gudummawa ga bunƙasar kasafin kuɗi, a hannu guda kuma yana illata tattalin arzikin da walwalar al’umma. A maimakon cirewar, ya kamata gwamnati ta yi shi cikin kyakkyawan tsari don guje wa illolinsa da kan shafi mafi yawan ‘yan ƙasa. Tabbatuwar Najeriya a matsayinta na ƙasa da samun ɗorewar makamashi a nan gaba, na buƙatar kyawawan tsare-tsare da sadaukar da kai ga jin daɗi da walwalar dukkan ‘yan ƙasa.

Manazarta

Abuchi, J., (2023, June 1). 10 Benefits of petroleum subsidy removal. The Authority News

Itumo, A., & Onyejiuba, E. I. (2019). Oil subsidy and development of local refineries In Nigeria: A Critical Analysis. African Journal of Politics and Administrative Studies, 12 (1)

Naidoo, A. (2023, August 27). The impact of fuel subsidy removal in Nigeria. LinkedIn

Was this article helpful?
YesNo