A karshen wannan shekara ta 2024 babu abinda ya jawo cecekuce mai yawa irin sabon tsarin haraji da shugaban Nigeria, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a gaban majalisar kasar. Sabon tsarin karba da rabawar harajin kasar ya samu suka mai yawa, musamman daga arewacin kasar, a yayin da sauran yankunan kasar ke ganin canjin daidai ne, musamman yan yamma maso arewacin kasar, inda shugaba Tinibun ya fito. Shin me wannan sabon tsarin rabon harajin ya kunsa? Ta yaya ya banbanta da tsarin da ake amfani da shi a yanzu? Kuma ta yaya zai shafi tattalin arzikin kasar da kuma al’ummar yankuna daban-daban? Za mu yi kokarin amsa wadannan tambayoyi, har ma da kawo muku tarihin tsarin haraji a Nigeria, a cikin wannan makalar don warware muku zare da abawa dangane da wannan cecekuce akan haraji. Bari mu fara da tarihin haraji.
Tarihin haraji a Nigeria
Najeriya ta kasance ƙasa mai dadadden tarihi tun tale-tale, ta haɗa kabilu manya da kananan da yankuna daban-daban da masarautu da dauloli daban-daban da al’umominsu da tsarin mulkinsu da kasuwancinsu da sauran al’amuran rayuwa. Domin fahimtar yadda tarihin haraji ya kasance a Najeriya, masana sun kasa shi gida uku, kafin mulkin mallaka, lokacin mulkin mallaka da kuma bayan samun ‘yancin kai.
(A) Kafin mulkin mallaka
Kafin mulkin mallaka, Najeriya ta ƙunshi masarautu da yawa da kuma yankuna da dama waɗanda suke da tsarin mulki irin nasu daidai da al’adunsu. Kowanne yanki yana da nasa shugaban da kuma tsare-tsare dangane da yadda ake karɓar haraji don gudanar da ayyukan al’umma da tafiyar da sha’anin mulki. Za a iya rarraba waɗannan yankuna zuwa;
i) Ƙasar Hausa
A farkon karni na 11, aka kafa garuruwan Hausa guda bakwai masu cin gashin kansu a arewacin Najeriya (wato Rano, Biram, Daura, Gobir, Kano, Katsina da Zariya). Waɗannan garuruwa sun zama cibiyar kasuwanci mai ƙarfi, tare da kiwo har ma da cinikin bayi. Suna da nau’ikan haraji iri-iri da suka hada da;
- Gandu: Wato harajin noma a kan amfanin gona.
- Zakka: Wannan ta zo ne a addinin musulmi, kuma ta haɗa da sadaka, kamar yadda Al-ƙur’ani ya tsara.
- Kudin-ƙasa: Wannan haraji ne na amfani da ƙasa.
- Jangali: Wannan haraji ne na masu kiwon shanu.
- Shukka-shukka: Shi ma wannan haraji ne na shuka.
- Gado: Kuɗi ko dukiyar da mamaci ya bari kuma ba a san wanda zai gaje shi ba. Wannan kuɗi ana bayar da su ga masarauta ne.
- Kudin sarauta: Wani kuɗi ne da ake biya ga sarki ko masarauta yayin da aka yi nadin wata sarauta.
ii) Ƙasar Borno
An kafa daular gabas wato (Kanem Borno Empire) da yankin Tafkin Chadi a karni na 9. Daular da ke mulki, wato Saifawa, a wancan lokacin ta ƙara faɗaɗa yankin ta hanyar mamaye wasu yankuna. Sakamakon rikice-rikice a tsakanin ƙarni na 12 zuwa 14, sarakunan ba su da wani zaɓi illa su koma Borno a arewa maso gabashin Najeriya. Mazaunan Borno na asali makiyaya ne da manona na yau da kullun.
Har kawo ƙarni na 19 bayi ne ke aikin gonakin noma. Tsarin harajinsu mai ban sha’awa ne, domin ya samar da ingantaccen tushen samun kudin shiga ga masarauta. Akwai nau’ikan haraji wanda aka fi sani da sada’a, wajibi ne a kan dukkan musulmi. An sanya wannan haraji ga manoma a matsayin harajin hatsi. Ana kuma karɓo harajin kiwo daga makiyaya. Harajin ƙasa, dole ne waɗanda suka mallaki ƙasa su biya shi. Har ila yau kuma manoma suna biyan wani nau’in haraji da ake kira kaleram, wato kuɗi ne da ake biya don samun izinin yin noma a ƙasar. ‘Yan kasuwa kuwa suna biyan kafelo, wannan wata nau’in kyautar wajibi ce ga mai mulki. Hadiyya ta kasance harajin da ake biya a wasu bukukuwan musulmi.
iii) Ƙasar Yarbawa
– Masarautar Ife
Birnin Ile-Ife ya kasance cibiyar al’adu da addini. Tana da matsayi na musamman na tarihi da tsarin mulki, wanda sauran masarautun Yarbawa ke bi. Muhimman masarautu suna da tsari na cigaba. Sana’ar sassaƙa ta kasance babbar hanyar ci gaba a yankin. Suna sassaƙa abubuwa iri-iri na itace, dutse da tagulla.
Birnin ya samu damar tattara kuɗaɗen shiga ta hanyar haraji da kuma kuɗaɗen ciniki a sakamakon waɗannan ayyukan da ake aiwatarwa. Jama’a suna ba wa sarakuna kuɗin shiga ta hanyar tsarin haraji shekara-shekara da gudunmawa ta musamman a wajen bukukuwa.
– Masarautar Oyo
Ita wannan masarauta ta Oyo tana da tsarin siyasa mafi inganci da dakarun soja, ta tattara yanki mafi girma a dukkan masarautun Yarbawa kuma ta zama mafi iko a cikin duk waɗannan masarautun a tsakiyar ƙarni na 16. Ƙasa ce mai albarka a yankin da ta ba wa jama’a damar noman amfanin gona wanda hakan ya ba su damar yin kasuwanci da garuruwa makwabta. Daular Oyo ta yi mu’amala da sauran garuruwan Yarbawa da kuma daular Benin.
Oyo na da tsarin kasuwa mai ban sha’awa, wanda ke haɗe da ingantattun hanyoyi. ‘Yan kasuwa suna da tsarin ƙungiyoyi daban-daban. Kasuwancinsu ya ƙunshi sayar da amfanin gonaki mai yawa da kayayyakin da aka sassaƙa, wanda ya ba wa yankin damar samar da kuɗaɗen haraji masu yawa. ‘Yan kasuwa suna biyan haraji ga garuruwan da suke, a lokacin da suka zo fita da hajojinsu ta ƙofar garin. A lokacin biki, garuruwan sukan kawo wa sarki harajinsu da kyautuka.
– Masarautar Ibadan
Asalin garin Ibadan daga wani ƙaramin ƙauye ne a shekarar 1827 ya bunƙasa zuwa birni mai adadin mazauna 60 000 a shekarar 1852, da 150 000 a shekarar 1890. Ana ba da gonakin noma na kusa ga dukkan mazauna garin, waɗanda suke son shuka amfanin gona a filayen da ake da su. A ƙarni na 19 birnin ya fitar da amfanin gona zuwa Ijebu har ma da Legas.
Kasancewar Ibadan cibiyar kasuwanci ce ta yankin Yarbawa, an ba ‘yan kasuwar Ibadan kariya ta hanyoyi daban-daban. Jama’a suna biyan haraji ga Ibadan a matsayin harajin shanu da zaitun da dabino da kuma cinikin bayi. A kowane gari ana biyan haraji daidai gwargwado a kan kowane gida. Ana biya hayar fili mai suna ishakole ga masu mulki. Maza da mata suna biya owo ode, da tsabar kudi da kuma amfanin gona. Rabin harajin yana tafiya wurin babban sarki, rabi kuma a ajiye shi a hannun mai unguwa.
iv) Masarautar Benin
Benin kafin mulkin mallaka ta kasance masarauta ce ta siyasa wacce ke da tsarin tsarin mulki. A karni na 15, Benin ta zama birni mai ƙarfi da wadata a sakamakon tashar jiragen ruwa ta Ughoton, wadda ake amfani da ita don cinikin bayi. Zanga-zangar da dakarun soja suka yi ta kai ga mamaye yankuna da dama na gabashin Yarbawa inda aka tilasta wa sarakunan garuruwan da aka ci da yaƙi da su miƙa wuya ga Benin. Ƙasar Benin ta samu ɗaukaka da martaba sakamakon wannan mamaya.
A farkon karni na 18 Benin ta samar da kuɗaɗen shiga masu yawa, galibi ta hanyar haraji. Tarin kuɗaɗen kuma ya kasance ginshiƙin samun kuɗi a Benin kafin mulkin mallaka. ‘Yan kasuwar suna biyan kuɗin alawus-alawus daidai da darajar kayayyakin da suka yi jigilar su, yayin da tsarin shari’a na gargajiya yake sanya tara. Ana biyan haraji, bisa ko dai tallafin ƙasa ko al’ada. Sarki yana ƙirƙiro sabbin muƙamai wanda wannan ma wata hanyar samun kuɗin shiga ce. Yankuna da dama sun ci gaba da mubaya’a ga ƙasar Benin, duk da cewa daga baya Benin ta yi amfani da ƙarfin soji.
v) Yankunan Gabas (Inyamurai)
‘Yan ƙabilar Igbo na ɗaya daga cikin manyan ƙabilun Najeriya, sai dai a sakamakon watsi da tsarin sarautarsu da al’adu babu wata masarauta da aka samu. A kowane yankuna uku na ayyukan tattalin arzikin yankin Inyamurai, a fannin noma, kasuwanci da masana’antu masarauta na da muhimmiyar rawar da za ta taka dangane da ci gaban Inyamurai a matsayin wata ƙabila mai tsari.
Duk ɗan kabilar Igbo manomi ne. Sassan ƙasar Igbo na da manyan ma’adinan ƙarfe waɗanda ake amfani da su don ƙera kayan aiki da abubuwan al’ada. Duk da babu wata masarauta ko tsarin shugabanci, al’ummar Igbo kafin mulkin mallaka na da tsarin haraji. Tsarin harajinsu ya ƙunshi ba da gudummawa ga ayyukan gama-gari kamar ginawa ko gyaran hanyoyin al’umma.
(B) Lokacin mulkin mallaka
Turawan mulkin mallakar Biritaniya sun yi ta ƙoƙarin mamaye tattalin arzikin Najeriya. Su ma, a lokacin mulkinsu suna da nasu tsarin harajin, sun yi ƙoƙarin aiwatar da wannan tsari a kan ‘yan kasuwa. An fara gudanar da mulkin mallaka a Najeriya tun a shekarar 1861. A lokacin, Legas ce fadar mulki a Najeriya. Duk da kasancewar wanzuwar hukumomin daban-daban, tsarin harajin ya kasance hukuma ɗaya ce ke da ikon karɓa.
Sir Lord Lugard shi ne shugaban mulkin mallaka na Burtaniya a Najeriya, a wancan lokacin. Ya yi kokarin daidaita tsarin haraji a Najeriya. A sakamakon haka, ya aiwatar da dokar haraji ta Stamp Duties Proclamation a shekarar 1903. An kuma maye gurbin wannan doka da wata dokar wato Native Revenue Proclamation a shekarar 1906. An ƙirƙiri wannan doka ne don daidaita tsarin harajin ƙasa. Wannan doka har wayau ta ƙunshi mahimman ƙa’idojin biyan kuɗi guda huɗu. Don haka, a duk lokacin da mutum yake son biyan haraji, sai ya bin waɗannan ƙa’idoji:
- Me za a biya?
- Wa zai biya?
- A ina zan biya?
- Yaushe za a biya?
Wannan hanya ta sauƙaƙa kuma ta fayyace manufofin haraji a Najeriya.
(C) Bayan samun ‘yancin kai
A Najeriya alhakin kula da haraji ya rataya ne a wuyan gwamnatin tarayya, jihohi da kuma ƙananan hukumomi. Kowane daga cikin matakan nan uku na gwamnati na da dokokin haraji da dokokin tarayya suka kafa. An tsara harajin Najeriya a matsayin hanyar samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati, kuma an gina shi ne a kan dokokin haraji na shekarar 1948, na gwamnatin mulkin mallakar Burtaniya, wanda aka samar kafin samun yancin kai. Kuma tun lokacin tsarin harajin Najeriya yake tafiya da gyare-gyare da sauye-sauye iri-iri. An gudanar da gyare-gyare a tsarin harajin Najeriya da dama. An yi gyare-gyaren ne don sauƙaƙa tsauraran dokokin haraji. Duk da waɗannan gyare-gyaren sake fasalin tsarin harajin Najeriya, tsarin har yanzu yana fuskantar ƙalubale da dama. Wato har yanzu akwai sauran batutuwan da ake jayayya da su da ke buƙatar kulawa cikin gaggawa.
Tsarin harajin Najeriya
Babbar manufar tsarin tsarin haraji a Najeriya ita ce samar da kuɗaɗen shiga ga gwamnati. An tsara wannan tsari ne bisa tanade-tanaden dokar ƙasa, kuma zai iya kasancewa haraji na kai tsaye ko kuma na kaikaice. Akwai nau’ikan haraji guda 61, waɗanda suka haɗa da harajin kuɗaɗe da caje-caje da ke ƙunshe cikin jadawalin dokar haraji wadda ta haifar da ƙarin haraji 22 daga na asali guda 39 a cikin shekarar 2014.
Akwai hanyoyin samar da kuɗaɗen shiga da yawa a Najeriya kamar harajin kwastam da harajin haƙo ma’adinai da harajin hayar gidaje da ƙari a kan farashin man-fetur da dai sauransu, ana tanadar su a ƙarƙashin dokoki daban-daban da kuma ɗimbin harajin da ƙananan hukumomi ke karɓa. Tsarin da gudanar da haraji a Najeriya yana da nau’i-nau’i daban-daban.
Akwai manyan matakai uku na gwamnati da ke da alhakin kula da haraji a Najeriya, wato tarayya, jihohi da kananan hukumomi. Dukkansu suna da iko a kan harajinsu, wanda dokokin tarayya suka tanada haɗe da manufofinsu. Hukumomin haraji na matakai ukun na gwamnati su ne; Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS), Hukumar Harajin Cikin Gida ta Jiha (SBIR) da kuma Kwamitin Harajin Karamar Hukuma.
Hukumar FIRS tana tantancewa da tattarawa da lissafin haraji da sauran kuɗaɗen shiga da ake tara wa gwamnatin tarayya, a yayin da hukumomin kula da harajin cikin gida na jihohi da na ƙananan hukumomi ke gudanar da irin waɗannan ayyuka a jihohi da ƙananan hukumominsu.
Tsarin rabon kuɗin haraji a tsawon shekaru a Najeriya ya nuna cewa a mafi yawan lokuta jihohi da ƙananan hukumomi na karɓar harajin ɗaiɗaikun mutane yayin da gwamnatin tarayya takan karbi harajin kamfanoni. Mafi yawan sabbin haraji irin su harajin fasahar sadarwa, (NITDA), harajin ilimi na manyan makarantu da harajin (VAT), gwamnatin tarayya ce da hurumin su.
Abubuwan da tsarin harajin Najeriya ya ƙunsa
Tsarin haraji a Najeriya yana da bangarori uku, waɗanda suka ƙunshi manufofin haraji, dokokin harajin da kuma shugabancin hukumar haraji.
1. Manufar haraji
Manufar haraji ta ƙunshi ka’idoji da tsare-tsare da manufofin da ake son cimmawa ta hanyar tsarin harajin. Manufar ta ƙayyade harajin da gwamnati za ta sanya wa kamfanoni da kadarori da ɗaiɗaikun mutane domin samar da kuɗaɗen shiga. Hakazalika, manufar ta ƙunshi batun harajin da gwamnati ke sawa a matsayin ƙananan caje-caje, nawa za a caja, sannan kuma wa za a caja. Har wayau dai manufar ta shafi nawa ne harajin da gwamnati za ta karɓa domin biyan kuɗaɗen da take kashewa da kuma tasirin harajin ga ayyukan tattalin arzikin ƙasa gabaɗaya. A taƙaice, manufar haraji ta shafi batun adalci, waye zai biya haraji kuma nawa ya kamata ya biya?
2. Dokokin haraji
Dokar haraji ta fayyace nau’ikan haraji da caje-caje da bayar da shawarar hukunci ga waɗanda suka karya doka da kuma yin tanadin tsarin dokokin haraji gabaɗaya. Hukumar (FIRS) ta ayyana dokar haraji a matsayin doka ko tsarin aiwatarwa ga dokokin haraji da ire-iren dokokin da ke yin tanadin haraji da caje-cajen gudanarwa. Hukumar ta FIRS ta lissafa dokokin haraji da ake aiki da su Najeriya kamar haka;
- Associated Gas Re-Injection
- Capital Gains Tax
- Companies Income Tax
- Deep Offshore and Inland Basin Production Sharing Contracts
- Tertiary Education Trust Fund
- Federal Inland Revenue Service (Establishment)
- Income Tax (Authorised Communications)
- Industrial Development (Income Tax Relief)
- Industrial Inspectorate
- National Information Technology Development
- Nigerian Export Processing Zones
- Nigerian LNG (Fiscal Incentive Guarantees and Assurances)
- Oil and Gas Export Free Zones
- Personal Income Tax
- Petroleum Profits Tax
- Value Added Tax
- Stamp Duties
- Taxes and Levies (Approved List for Collection)
- Casino Act
3. Shugabancin hukumar haraji
Wannan ɓangare ya ƙunshi aiwatar da dokokin haraji ta hanyar ayyukan hukumomin da aka ɗorawa nauyin hakan tare da wajibcin tantancewa, tattarawa da lissafin kuɗaɗen shigar da aka samu. Haka nan wannan sashe yana da alaƙa da gudanar da manufofin haraji wanda suka haɗa da bin ƙa’idojin haraji ga masu biyan harajin.
Hukumomin harajin Najeriya
Akwai hukumomin haraji guda uku (3) da ke wakiltar matakan gwamnati guda uku;
- Hukumar Harajin Cikin Gida ta Tarayya (FIRS): ƙarƙashin gwamnatin tarayya.
- Hukumar Harajin Cikin Gida ta Jiha (SIRS): ƙarƙashin gwamnatin jiha.
- Kwamitin Harajin Ƙaramar Hukuma: ƙarƙashin ikon ƙaramar hukuma.
Hukumar haraji ta tarayya (FIRS)
Federal Inland Revenue Services (FIRS) ita ce hukumar haraji ta tarayya kuma dokar harajin kuɗi ta kamfanoni wato (CITA) ta shekarar 1979 ce ta ƙirƙire ta kuma a yanzu tana ƙarƙashin dokar FIRS, ta shekarar 2007. Ma’aikatar da ke da alhakin lura da ita ita ce Ma’aikatar Kula da Harajin Cikin Gida ta Tarayya wato, Federal Inland Revenue Services Board (FIRSB).
Dokokin hukumar (FIRSB)
Dokokin wannan hukuma sun tanadi ƙa’idojin zama mamba na ma’aikatar FIRSB kamar haka:
1) An kafa hukumar don kula da ayyukan hukumar kula da harajin cikin gida ta tarayya (FIRS) wacce za ta sami cikakkiyar kulawa kamar yadda aka bayyana a ƙarƙashin dokar.
2) Hukumar za ta kunshi:
- Shugaban zartarwa wanda zai kasance mai gogewa a fagen haraji a matsayin shugaban ma’aikata, wanda shugaban ƙasa zai naɗa, kana kuma ya samu tabbatarwa daga majalisar dattawa;
- Mambobi shida masu cancanta da ƙwarewa waɗanda shugaban ƙasa zai naɗa don wakiltar kowace shiyya cikin shiyyoyin mulki guda 6;
- Wakilin babban lauyan gwamnatin tarayya
- Gwamnan babban bankin Najeriya ko wakilinsa.
- Wakilin ministan kuɗi wanda bai gaza matsayin darakta ba;
- Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen da kasafi ko wakilinsa wanda zai iya kasancewa kowane daga cikin kwamishinoni masu wakiltar jihohi 36 na tarayyar;
- Manajan darakta na kamfanin man-fetur na Najeriya ko wakilinsa wanda bai yi ƙasa da matsayin babban darakta na kamfanin ba ko makamancinsa;
- Kwanturola-janar na hukumar harkokin kasuwanci ko wakilinsa da bai gaza matsayin darakta ba;
- Babban jami’in hukumar tsare-tsare ta ƙasa ko wakilinsa wanda bai gaza matsayin darakta ba;
3) Membobin kwamiti, ban da shugaban zartarwa, za su kasance mambobin wucin-gadi.
Ayyukan hukumar FIRSB
Hukumar FIRSB tana da ikon tantancewa da aiwatar ayyuka kamar haka:
1) Hukumar za ta aiwatar da;
- Samar da dukkan tsare-tsaren gudanarwa waɗanda suka shafi ayyukan hukumar;
- Sarrafawa tare da kula da manufofin aikace-aikace ga al’amuran da suka shafi gudanar da kuɗaɗen shiga, caje-caje, tattarawa da tsarin lissafin kuɗi a ƙarƙashin wannan dokar ko duk wani tsari;
- Bita da kuma yarda da tsare-tsaren dabarun aikace-aikacen hukumar;
- Samarwa tare da ƙayyade sharuɗɗan aikace-aikace da suka haɗa da matakan ladaftarwa ga ma’aikatan hukumar;
- Kayyade albashi, alawus-alawus, hakkoki da fansho na ma’aikata tare da tuntubar ma’aikatar albashi da kuɗin shiga ta ƙasa;
- Aiwatar da dukkan abubuwa bisa ra’ayin hukumar waɗanda suke da mahimmanci don tabbatar da ingantattun ayyukan hukumar ƙarƙashin wannan dokar.
Kwamitin ayyuka na hukumar FIRSB
Wannan wani ɓangare ne ko kwamiti wanda dokar harajin ta kamfanoni ta ƙirƙira, wato Companies Income Tax Act, kamar yadda aka gyara dokar a shekarar 2007. Wannan kwamiti ya ƙunshi;
- Shugaban hukumar wanda kuma shi ne shugaban kwamitin
- Daraktoci da shugabannin ɓangarorin hukumar
- Mashawarci kan al’amuran Shari’a na hukumar
- Sakataren hukumar
Kwamitin yana da ikon ƙara yawan mambobin idan buƙatar hakan ta taso don gudanar da ayyukansa. Yana da ikon ƙarawa don:
- Yin la’akari da al’amuran haraji da ke buƙatar ƙwararru da fasaha da ba da shawarwari ga hukumar.
- Ba wa hukumar shawara a kan iko da ayyukanta
- Gudanar da duk wani aikin da hukumar ta dora wa kwamitin.
Hukumar Haraji ta Jiha (SIRS)
An kafa hukumar harajin cikin gida ta jiha bisa dokar harajin kuɗi ta 1993 a matsayin hukumar kula da haraji ta jiha. Bangaren aiki na hukumar shi ne ma’aikatar kula da kudaden shiga ta jiha (SIRSB). Sashe na 85A (1) PITD na shekarar (1993) ya ayyana tsari na bai-ɗaya ga dukkan jihohin tarayya. Abubuwan da aka tsara su ne kamar haka:
- Shugaban hukumar kula da kuɗaɗen shiga na cikin gida na jiha wanda za a naɗa a matsayin shugaban hukumar, zai zama mutum mai gogewa a harkokin haraji kuma gwamnatin jiha za ta zaɓo shi daga cikin ma’aikatan jihar.
- Mutane uku da kwamishinan kuɗi na jihar zai gabatar da sunayensu bisa cancantarsu.
- Dukkan daraktoci da shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga na jiha.
- Darakta daga ma’aikatar kuɗi ta jiha.
- Mashawarcin kan al’amuran shari’a na hukumar.
- Sakataren hukumar wanda zai kasance tsohon mamba ne na kwamiti daga cikin hukumar SIRSB.
Ayyukan hukumar (SIRSB)
- Tabbatar da inganci da kyakkyawan tsarin tattara dukkan haraji da hukunce-hukuncen da suka shafi gwamnati a ƙarƙashin dokokin da suka dace.
- Aiwatar duk wasu abubuwan da za a iya ganin sun dace don tantancewa da tattara haraji da lissafinn duk adadin kuɗin da aka tattara ta hanyar da kwamishinan ya tsara.
- Ba da shawarwari, inda ya dace da hukumar haraji ta yi haɗin-gwiwa game da manufofin haraji, gyare-gyaren haraji, dokokin haraji, yarjejeniyar haraji yadda zai yiwu kuma ake bukata daga lokaci zuwa lokaci.
- Kula da dukkan harkokin gudanarwa na aikace-aikace da tsare-tsare ƙarƙashin tanadin dokar ta kafa hukumar.
- Naɗawa, ciyarwa gaba, canja wurin aiki da kuma ladaftarwa ga ma’aikatan hukumar.
Kwamitin ayyuka na hukumar SIRSB
Haka nan an kafa wannan kwamiti ne na hukumar tattara kudaden shiga ta jiha bisa dokar harajin ɗaiɗaikun mutane ta shekarar (1993). Kwamitin ya ƙunshi waɗannan mutane a matsayin membobi:
- Shugaban hukumar tattara kuɗaɗen shiga na jihar wanda kuma shi ne
- shugaban kwamitin.
- Dukkan daraktocin hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta jiha.
- Mai ba da shawara kan harkokin shari’a ga hukumar.
- Sakataren kwamitin.
Ayyukan kwamitin aiki na SIRS
- Ba da shawara ga hukumar a kan al’amuran da ke buƙatar ƙwararru.
- Gudanar da duk wani aiki da hukumar ta dora wa kwamitin.
Hukumar harajin haɗin-gwiwa ta tarayya (JTB)
An kafa hukumar harajin haɗin-gwiwa ne ƙarƙashin sashi na 85 na dokar harajin ɗaiɗaikun mutane wato Personal Income Tax (PIT), kamar yadda aka yi wa dokar gyaran fuska. Ayyukan wannan hukuma sun haɗa da sasanci tsakanin hukumomin haraji na jihohi da tarayya idan aka samu saɓani kan haraji. Ƙirƙirar hukumar kamar yadda dokar Personal Income Tax ta shekarar 1993 ta bayyana ta kasance kamar haka:
- Shugaban hukumar haraji ta ƙasa shi ne shugaban hukumar harajin haɗin-gwiwar.
- Mamba ɗaya daga kowace jiha ta tarayya, da kwamishinan kuɗi zai zaɓa, zai kasance mutum ne mai gogewa a harkokin haraji.
- Sakataren hukumar wanda zai kasance jami’in da ya ƙware a harkokin haraji, wanda kwamishinan ma’aikatar na tarayya ya naɗa, duk da cewa ba mamba ba ne, amma shi ne ke da alhakin adana bayanan ayyukan hukumar da gudanar da wasu ayyukan shugabanci.
- Mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar kula da harajin cikin gida ta tarayya, shi ne mai halartar taron hukumar kuma shi ne mai ba da shawara kan harkokin shari’a ga hukumar.
Ayyukan hukumar JTB
Dokar harajin kuɗaɗen shiga ta ɗaiɗaikun al’umma ta shekarar 1993 ta fayyace iko da ayyukan hukumar kamar haka:
- Yin amfani da iko ko ayyukan da aka ba ta ta hanyar samar da wannan doka, da duk wani iko, da ayyukan da suka taso a ƙarƙashin wannan doka wandaza a iya amincewa da gwamnatin kowane yanki don aiwatarwa.
- Yin amfani da iko wajen aiwatar da ayyukan da aka ba ta ta kowace doka da gwamnatin tarayya ta sanya haraji kan kuɗaɗen shiga da riba, na kamfanoni, ko wanda hukumar kula da harajin cikin gida ta tarayya za ta iya amincewa.
- Ba da shawara ga buƙatun gwamnatin tarayya, dangane da tsarin biyan haraji ko bisa la’akari da kowace jiha, da kuma ƙimar alawus-alawus na babban birnin tarayya da sauran batutuwan haraji wanda ke da tasiri a duk faɗin Najeriya da kuma duk wani gyara da aka gabatar ga wannan doka.
- Amfani da ƙwazo da ƙwarewa don inganta daidaito a tsakanin ɓangarori biyu a cikin aikace-aikacen dokokin haraji da kuma matsalar haraji ga daidaikun mutane a fadin Najeriya.
- Aiwatar da hukunci a kan al’amura da fassara wannan doka a kan kowace jiha don aiwatar da tsarin da aka amince da shi.
- Aiwatar da shawarwarin amincewa kan tsare-tsaren kuɗaɗen da aka samar, ya kasance an gane su a matsayin alawus ɗin haraji.
- Warware duk wata taƙaddama tsakanin masu biyan haraji da hukumar haraji.
- Amfani da duk wani iko ko ayyuka da suka taso a ƙarƙashin dokar wanda za a iya amincewa da gwamnatin kowace jiha.
Daga madafun iko da ayyukan da aka zayyana a sama za a iya ganin cewa JTB ta daidaita harkokin haraji a ƙasar nan.
Kwamitin Harajin haɗin-gwiwa na J’jiha (SJRC)
An kafa wannan ga kowace jiha ta tarayya, ya kuma kunshi:
- Shugaban hukumar tara haraji ta jiha a matsayin shugaba.
- Shugaban kwamitocin tara kuɗaɗen shiga na ƙananan hukumomi.
- Wakilin ofishin kula da harkokin ƙananan hukumomi da bai gaza matsayin darakta ba.
- Wakilin rabon kuɗaɗen shiga da kasafin kudin hukumar, a matsayin mai sa-ido.
- Kwamandan sashin jihar na hukumar kiyaye haɗɗura ta tarayya, a matsayin mai sa-ido.
- Mashawarcin kan harkokin shari’a na hukumar harajin cikin gida ta jiha.
- Sakataren kwamitin wanda zai kasance ma’aikacin hukumar tattara kuɗaɗen shiga na jiha.
Ayyukan hukumar SJRC
Waɗannan su ne ayyukan SJRC;
i. Aiwatar da shawarwarin hukumar harajin haɗin-gwiwa
ii Ba wa hukumar harajin haɗin-gwiwa da ta jiha da ƙananan hukumomi shawara kan harkokin kuɗaɗen shiga.
iii. Daidaita tsarin kula da haraji a jihar.
iv. Faɗakar da al’umma a kan kuɗaɗen shiga na jiha da ƙananan hukumomi.
Kwamitin harajin karamar hukuma (Local Government Revenue Committee) (LGRC)
Kwamitin kuɗaɗen shiga na ƙananan hukumomi shi ne hukumar haraji ta ƙananan hukumomi. An kafa kwamitin ne bisa sashi na 85 na Personal Income Tax Decree ta shekarar 1993. An ba wa kwamitin ikon karɓar haraji a matakin ƙananan hukumomi. Mambobin kwamitin gudanarwa na kuɗaɗen shigar ƙananan hukumomi su ne kamar haka:
- Shugaba wanda shi ne mai kula da harkokin kuɗi.
- Kansilolin ƙananan hukumomi uku.
- Mutum biyu da shugaban ƙaramar hukumar zai zaɓa.
- Dole ne waɗanda za a zaɓa su kasance masu gogewa a harkokin kuɗaɗen shiga.
Ayyukan hukumar LGRC
Waɗannan su ne ayyukan LGRC:
- Ita ce ke da alhakin tantancewa da karɓar duk haraji, karɓar tara da kuɗaɗen da ke ƙarƙashinta kuma za ta yi lissafin duk kuɗaɗen da aka karɓa ta hanyar da shugaban ƙaramar hukumar ya tsara.
- Za ta kasance mai cin gashin kanta na baitul-malin ƙananan hukumomi, kuma ita ce ke da alhakin gudanar da ayyukan yau da kullum na sashen, wanda ya zama ɓangaren aikinta.
- Nasiha ga ƙaramar hukumar kan harkokin haraji.
Ƙudirin sake fasalin dokar haraji ta Najeriya na 2024
Shugaban Najeriya mai-ci, Bola Ahmad Tinubu, ya gabatar da wasu ƙudorori a gaban majalisar ƙasa da ke neman sauya fasalin dokar haraji. Kudirin sake fasalin dokar harajin wasu kudirori ne daban-daban da ke son yin gyaran fuska ga tsarin haraji a Najeriya karkashin wasu dokoki guda hudu. Kudurorin su ne kamar haka:
1. Kudirin harajin Najeriya
2. Dokar kula da harajin Najeriya
3. Dokar kafa hukumar harajin ta Najeriya
4. Kudirin kafa harajin haɗin-gwiwa 3
Kudirin ya haɗa dukkan dokokin da ake buƙata waɗanda aka tanada don aiwatar da haraji. Idan aka amince da shi, wannan kudiri zai ba da damar soke wasu dokoki 11 da suka ƙunshi tanade-tanade kan sanyawa da karɓar haraji. Wasu daga cikin manyan tanade-tanade da ke kunshe a cikin kudirin dokar harajin Najeriya wanda zai yi tasiri a kan ɗaiɗaikun mutane da kamfanoni sun hada da:
- Cire mutanen da ke samun N800,000 ko ƙasa da haka daga biyan haraji. A halin yanzu, idan mutum yana samun jimillar ₦800,000 a duk shekara, to ana buƙatar ya biya ₦84,000 daga cikin wannan adadin a matsayin haraji. Idan wannan ƙudiri ya tabbata, ba zai biya komai ba.
- Waɗanda suke samun sama da naira miliyan 50 ne za su biya kashi 25% na kuɗaɗen shiga. A karkashin dokar da take a yanzu, da zarar mutum ya samu sama da naira miliyan 3.2 za a caje shi kashi 24% na haraji.
- Ware ƙananan sana’o’i daga biyan haraji. A cikin wannan kudiri an ayyana ƙananan kamfanoni a matsayin waɗanda suke samun kuɗin shiga na shekara-shekara na naira miliyan 50 ko ƙasa da haka. A cikin dokar da take aiki kuwa, an bayyana ƙananan kamfanoni a matsayin waɗanda suke samun kuɗaɗen da suka kai naira miliyan 25 ko ƙasa da haka. Abin da hakan ke nufi shi ne, kusan kashi 90% na ‘yan kasuwa a Najeriya za a cire su su daga biyan haraji.
- Rage biyan haraji daga kashi 30% zuwa 25% a shekarar 2026 ga matsakaita da manyan kamfanoni.
- Janye mafi ƙarancin haraji na kashi 1% da ake ɗorawa kan manyan kuɗaɗen na matsakaita da manyan kamfanonin da ba su bayyana ribarsu ba. A cikin riba kawai za a biya haraji a ƙarƙashin wannan sabon ƙudiri.
- Daidaita harajin ilimi da kashi 2.5%, harajin NITDA da kashi 1%, da harajin NASENI da kashi 0.25% wanda kamfanoni da yawa ke biya baya ga harajin da kamfani ke biya a duk shekara zuwa harajin ci gaba na kashi 2% wanda za a yi amfani da shi don ba da lamunin karatu daga shekarar 2030. Wannan ƙudiri zai ƙara rage yawan nauyin haraji na wasu kamfanoni daga kusan kashi 33.75% na abin da suke samu.
- Nazarin tsarin raba kuɗaɗen shiga na VAT inda a yanzu jihohi ke karɓar kashi 55% na kuɗaɗen shiga maimakon kashi 50% yayin da kason gwamnatin tarayya ya ragu daga kashi 15% zuwa 10%. Kason kananan hukumomin ya kasance iri ɗaya.
- Ci gaba da inganta ƙimar VAT daga kashi 7.5% na yanzu zuwa kashi 10% a cikin shekarar 2025, sai kashi 12.5% a tsakanin shekarun 2026 zuwa 2029 da kuma kashi 15% daga shekarar 2030.
- Cire yawancin kayayyakin amfanin yau da kullun da talakawa ke saya daga harajin VAT kamar kayan abinci, sha’anin kiwon lafiya da magunguna, kuɗin makaranta, wutar lantarki da sauransu.
- Cire haraji don ƙarfafa saka hannun jari a harkokin iskar gas da sauran su.
Tanade-tanaden sabuwar dokar haraji ta Najeriya
Sabuwar dokar hukumar haraji ta Najeriya, ita ce dokar da ta bayyana yadda hukumomin haraji za su gudanar da karɓa tare da sarrafa haraji, waɗanda suka hada da tantancewa, tarawa da kuma kididdigar kuɗaɗen harajin da suke karɓa. Ƙudirin ya kuma zayyana iko da ayyukan hukumomin haraji, harajin da aka keɓe shi kaɗai domin hukumar NRS ta karɓa da kuma wanda aka keɓe wa jahohi a cikin wasu tsare-tsare daban-daban da suka shafi ingantaccen tsarin haraji a Najeriya. Wasu daga cikin manyan tanade-tanaden daftarin dokar kula da haraji ta Najeriya sun hada da:
- Saka masu arziki a cikin haraji. Kudirin ya samar da hanyar da za ta tabbatar da cewa ɗaiɗaikun kwastomomin cibiyoyin hada-hadar kuɗi waɗanda kan yi hada-hada a wata ɗaya da ta kai naira miliyan 25 ko sama da haka, da kamfanoni waɗanda adadin hada-hadarsu ya kai naira miliyan 100 ko sama da haka a wata guda ba sa bijire wa biyan haraji ta hanyar tilasta wa cibiyoyin hada-hadar kuɗin miƙo wa hukumar haraji jerin sunayen irin waɗannan mutane da kamfanoni tare da adiresoshinsu.
- Hukumar NRS ce za ta tattara kuɗaɗen shiga na wasu hukumomi kamar Nigeria Customs Service, Nigeria Upstream Petroleum Regulatory Commission (NUPRC), NPA, NIMASA, da dai sauransu. Wannan tanadin na nufin ba wa waɗannan hukumomin damar mayar da hankali kan ayyukansu na ƙayyadaddewa yayin da NRS wadda aikinta shi ne tattara kuɗaɗen shiga.
- Samar da fasahar zamani wajen tarawa da kuma lissafa kuɗaɗen haraji. Wannan zai inganta tara haraji musamman kan kamfanonin da ke aiki da tsarin dijital kamar kafofin watsa labarai, shafukan sada zumunta, da sauran su.
- Rage kuɗaɗen harajin da ba a biya ba daga hukumar MDAs waɗanda suke aiki a matsayin wakilan hukumomin haraji daga kasafin kuɗinsu.
- Wani sabon tsarin samar da harajin VAT inda kashi 60% na kuɗaɗen shiga na harajin jihohi ana raba su ne bisa la’akari da yadda aka same su, kashi 20% a raba bisa la’akari da yawan al’umma sannan sauran kashi 20% kuma ana raba su daidai a tsakanin jihohi. Abu mafi mahimmanci shi ne, kuɗaɗen harajin VAT a sabon tsarin nan ba za a sake danganta su da muhallin masana’antu ko ayyukan ba, za a danganta su ne da asalin wuraren da ake amfani da kayayyaki ko ayyukan a faɗin jihohin. Hanyar da ake bi a halin yanzu ta fifita jihohi irin su Legas, Ribas da Oyo waɗanda ke da hedikwatar kamfanoni da yawa a cikinsu.
- Damar biyan haraji kashi-kashi, wato da kaɗan-kaɗan
- Samar da kuɗi ga asusun mayar da kuɗaɗen haraji ga waɗanda suka biya ya zarta ƙima ta hanyar cire wani kaso na kuɗaɗe daga cikin harajin da hukumar ta tara kafin rarrabawa. Wannan zai tabbatar da cewa an biya duk wani mai da’awar ya biya harajin sama da ƙima kuma an tabbatar da hakan, za a mayar masa. Kafin wannan ƙudiri ana samar wa asusun kuɗi ne ta abin da kasafin kuɗi ya fitar, wanda kuma ba sa wadata sosai.
- Kafa kwamitin harajin kuɗi na ƙananan hukumomi don kula da tattara haraji, karɓar tara da kuma caje-caje a ƙarƙashin ikon kowace ƙaramar hukuma.
- Daidaita duk laifukan haraji da hukunci don tabbatar da bin doka.
Haka nan akwai ƙudiri na neman sauya sunan hukumar tara haraji ta ƙasa FIRS zuwa hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta Najeriya (NRS) domin ganin yadda take tara kuɗaɗen shiga ba wai gwamnatin tarayya kaɗai ba ke amfana, tunda akasarin kuɗaɗen shigar da take karɓa ana rabawa ne tsakanin matakai uku na gwamnati. Kudirin ya kuma bai wa hukumar ta NRS ikon gudanar da dukkan haraji da suka haɗa da sauran harajin da wasu hukumomin tarayya ke karɓa a yanzu kamar hukumar kwastam ta Najeriya, NUPRC, NPA, NIMASA da dai sauran su.
Kudurin dokar kafa hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta haɗin-gwiwa ya tanadi kafa hukumomi daban-daban har guda uku da suka hada da:
- Hukumar tattara kudaden shiga ta haɗin-gwiwa ta Najeriya (Joint Revenue Board of Nigeria) wacce za ta taimaka wajen daidaita duk wani harajin da ake karɓa a ƙasa tare da soke harajin da bai dace ba da kuma samar da bayanan masu biyan haraji na ƙasa.
- Kotun daukaka kara ta haraji (Tax Appeal Tribunal) wacce za ta yi aiki don warware taƙaddamar haraji tsakanin hukumomin haraji kan batutuwan da suka haɗa da ikon tara harajin da sauransu.
- Ofishin ƙorafe-ƙorafe (Office of the Tax Ombudsman) wanda zai taimaka wa masu biyan haraji su gabatar da ƙorafe-ƙorafensu domin samun adalci idan akwai rashin jituwa da hukumomin haraji.
Manufofin tsarin harajin Najeriya
Manufofin tsarin haraji kamar yadda tsarin harajin Najeriya (The National Tax Policy) ya bayyana su ne kamar haka;
- Don haɓaka kasafin kuɗin ƙasa
- Don ci gaban tattalin arziki
- Don samar da nutsuwa ga gwamnati yayin da take amfani da albarkatun ƙasa don samar da ayyuka ga jama’a
- Don tabbatar da magance matsalar rashin daidaiton rarraba kuɗaɗen shiga
- Don tabbatar da nagartaccen tsarin tattalin arziki
- Don magance matsaloli da kurakurai a fannin haraji.
Matsaloli da kalubalen da tsarin harajin Najeriya
Tsarin harajin Najeriya yana tattare da ƙalubale iri-iri. [Link 7] A cikin watan Oktoba na shekarar 2010, kafar Price Waterhouse Coopers ta lissafa manyan batutuwan haraji guda 50 a Najeriya. Kacokan gwamnatoci sun fi mayar da hankali kan ciniki da harajin man-fetur; an yi watsi ko sakaci da tarin haraji na kai-tsaye waɗanda ke da muhimmanci kamar harajin VAT (Value Added Tax). Bugu da ƙari, tsarin gudanarwa na hukumomin haraji shi ma cike yake maƙil da ƙalubale sakamakon dalilai kamar rashin ilimi da ƙarancin sanin mene ne harajin kansa da kuma rashin samun horo da bita ga jami’an kula da haraji. Ga wasu daga cikin ƙalubalen da ke tattare da tsarin harajin Najeriya;
Karɓar haraji fiye da sau ɗaya
Wannan matsala na da alaƙa da ɗora haraji a kan abu ɗaya, sau biyu ko sama da haka. Wato yanayi ne da ke haifar da karɓar haraji fiye da sau ɗaya. Wannan ba tsari ne da aka sani a fagen haraji ba. Don haka, wannan baƙon tsari ne ga harkar harajin Najeriya, kuma ya saɓa da doka. Masu biyan haraji da kuma kamfanoni duk suna kokawa game da wannan tsari na karɓar haraji fiye da sau ɗaya.
Matsalar shugabanci
Ɗaya daga cikin manyan matsalolin haraji a Najeriya shi ne tsarin kula da harajin, wanda hakan ke haifar da rashin gaskiya wajen tafiyar da kuɗaɗen shiga. Wannan kan haifar da ƙin biyan haraji, wanda shi ma alama ce cikin manyan matsalolin da ke tattare da tsarin haraji a ƙasashe masu tasowa ciki har da Najeriya.
Rashin cikakkun bayanai
Rashin samun gamsassun bayanan duk ɗaiɗaikun mutanen da ke biyan haraji da kayan aikin da ake amfani da su don tantancewa da tattara haraji da kuma rashin ingantattun hanyoyi, suna daga cikin batutuwan da ke raunata ingancin tsarin harajin Najeriya. Babu wani yunƙuri na tattarawa ko bincika ƙayyadaddun bayanai da ake da su. Wannan ya nuna cewa tsarin harajin Najeriya ba shi da inganci.
Ƙarancin ƙwararru
Tauye haraji a ƙananan hukumomi ɗabi’a ce da ta zama ruwan-dare musamman a matakin da mutane waɗanda ba su da ƙwarewa kuma ba a horar da su yadda ake karɓar haraji ba, a riƙa amfani da su wajen tilasta wa mutane ana karbar haraji. A wasu jihohi misali kamar Fatakwal da Kano ana amfani da su wajen karɓar haraji daban-daban.
Tsarin dokar harajin Najeriya
Wani sashe na dokokin harajin Najeriya na da sarƙakiya ta yadda a wasu lokutan sukan yi wahalar fahimta, hatta masu ilimi a cikin al’umma sukan gaza ganewa. Saboda irin sarƙaƙiyar dokokin harajin Najeriya, ba abu ne mai sauƙi ga masu biyan harajin su fahimta.
Ƙayyade kuɗin haraji
Ƙaga wa kamfani mafi ƙarancin haraji matsala ce ita ma. Domin a lokacin da babu riba mai yawa ko ma babu ribar gabaɗaya, kamfani zai kasance ya yi asara a wannan shekarar. Abin da wannan yake nunawa shi ne, kamfanoni ba su da wani zaɓi da ya wuce su biya haraji daga cikin jarinsu, don haka akwai barazanar gazawar kamfanoni lokacin da aka samu ƙarancin riba ko ma babu ribar gabaɗaya. Masana na ganin ƙayyade mafi ƙarancin haraji kamar tilasta wa mutum ne ya ba da gudummawar jini, alhali kuwa yana fama da matsalar buƙatar jinin.
Shawarwari da mafita
Duk da kasancewar tsarin harajin Najeriya yana cike da matsaloli da ƙalubale daban-daban, hakan ba yana nufin matsalolin ba su da magani ba ne, lallai akwai mafita. Ga wasu shawarwari da idan aka bi za a samu sauƙi da sassauci;
1. Samar da ingantacciyar hanyar tattara kuɗin shiga
Ya kamata matakai uku na gwamnati su samar da ingantaccen tsari ga masu biyan haraji; wanda ya haɗa da sake fasalin hanyoyin da ake amfani da su wajen tarawa da kuma kawo ƙarshen yawaitar haraji, wanda hakan ya zama naƙasu ga ɓangaren masana’antu da tattalin arzikin ƙasa gabaɗaya. Haka kuma ya kamata a rage haraji da yawa sannan a daidaita harajin da aka amince da shi a matakai uku na gwamnati.
2. Tabbatar da kyakkyawan tsarin kula da haraji mai inganci
Ya kamata gwamnati ta tabbatar da cewa ƙwararrun ma’aikata masu ilimi su ne ke gudanarwa tare sarrafa haraji. Ya kamata a riƙa horar da ma’aikatan hukumomin haraji na kowane mataki uku na gwamnati a kai-a kai.
3. Samar da fasahar zamani
Haka nan ya kamata a ɓullo da tsarin biyan kuɗin haraji ta hanyar yanar gizo a Najeriya domin hakan zai rage ɓata lokaci da sauƙaƙa wa masu biyan harajin. Wannan na iya taimakawa wajen bincika ayyuka da bayanai nan take da sauƙaƙa harkokin haraji.
4. Hanyoyin wayar da kai
Akwai bukatar wayar da kan jama’a cikin gaggawa. Ya kamata kafofin watsa labarai su kasance ana yin amfani da su don sadarwa da kuma sanar da sababbin dokokin haraji da fahimtar da jama’a buƙatar bin doka da kuma hukunci ga masu karya doka. Wannan zai taimaka saboda yawancin masu biyan haraji ba a sanar da su wasu bayanan ko kuma ba su da masaniya game da wasu dokokin harajin.
5. Sauƙaƙa dokokin haraji
Ɗaya daga cikin mahimman ƙa’idojin kowane tsarin haraji mai kyau shi ne dole ne ya zama mai sauƙi, tabbatacce kuma bayyananne. Ya kamata a fassara tare da yin bayanin dokokin haraji dalla-dalla don tabbatar da cewa masu biyan haraji da jami’an haraji sun fahimce su sosai. Kuma ya kamata a soke wasu daga cikin dokokin kamar dokar ƙayyade mafi karanci haraji.
6. Mayar da kuɗaɗen harajin da suka yi yawa
Ya kamata hukumomin haraji na matakai uku na gwamnati su fara mayar da kuɗaɗen harajin da aka biya suka zarta ƙa’ida. Gwamnati cikin gaggawa ta samar da kuɗaɗen da za a mayar da su ga mutane. Domin hakan zai ƙara ƙwarin gwiwar masu biyan haraji ga amincewa da gwamnati.
7. Damar cin gashin kai
Yakamata a bai wa hukumomin haraji a ƙananan hukumomi, jiha da tarayya matsayi masu zaman kansu. Hakan zai bai wa hukumomin damar ɗaukar nauyin ayyukansu da yadda suke gudanar da harkokin gudanar da haraji.
8. Magance matsalar cin hanci
Karancin albashin jami’an kula da haraji ya sanya da yawa daga cikinsu yin sulhu da masu laifin biyan haraji. Don haka akwai bukatar a magance matsalar cin hanci da ayyukan rashawa a tsakanin jami’an haraji. Kamata ya yi a tuhumi jami’an da ke karɓar cin hanci da rashawa, kuma kada wani babban jami’in gwamnati ya yi katsalandan game da hukuncin da doka ta tanada. Gwamnati ya kamata ta biya ma’aikatan haraji albashi mai gwaɓi ko kuma ta bayar da kwangilar ɓangaren haraji ga hukumomi masu zaman kansu.
9. Ƙarfafa binciken haraji
Wannan aiki ne da aka yi watsi da shi a Najeriya. Jami’an haraji suna zama a ofisoshinsu ba tare da tantance kamfanoni ba. Ya kamata jami’in haraji ya kasance mai himma don gano kamfanoni da ɗaiɗaikun mutanen da suka daina cika kuɗaɗen shekara-shekara, kamfanonin da ke bayyana ribar da ake zargin su da kuma kamfanonin da ke ba da rahoton asarar da suka yi. Inganta binciken ƙididdiga zai rage guje wa biyan haraji, ƙara yunƙurin kiyaye bayanan da ya dace na masu biyan haraji.
10. Ƙaddamar da kotuna na musamman don harkokin haraji
Ya kamata gwamnati ta kafa ko sanya wasu kotuna a matsayin kotunan haraji don magance matsalolin haraji da batutuwan da suka shafi masu kin biyan haraji da jami’an haraji masu cin hanci da rashawa da. Ya kamata a kula da fassarar dokokin haraji a wannan kotu ta musamman. Ya kamata a bai wa lauyoyi horo na musamman game harkokin haraji, domin hakan zai taimaka matuka wajen magance ɗimbin matsalolin haraji da ke tattare da tsarin harajin Najeriya.
11. Hukunci mai tsauri kan ƙin biyan haraji da sauran laifuka
Hukunce-hukuncen da dokokin haraji da ake da su a Najeriya a halin yanzu ba sa iya hana masu laifi aikata laifin. Hukunce-hukunce masu tsauri, kamar ƙwace kadarori, ɗaurin kurkuku ba tare da wani zaɓi na tara ba, ƙwace lasisi a inda ya dace da sauran su za su bunƙasa tafiyar da tsarin haraji.
Manazarta
Babajide, O. (2020, August 10). Nigerian tax system structure and administration. PML
Olarinde, O. M. (2024, June 3). Overview of fiscal and tax reforms in Nigeria. LinkedIn
Olusegun, D. (2024, November 21). Tinubu’s Tax Reforms Explained in Layman’s Language. PM News Nigeria
San, O. M. A., & San, O. M. A. (2024, December 12). The Nigerian Tax Bill 2024 At a glance: Highlights and key provisions. Omaplex Law Firm