Noma a lokacin damina sanannen abu ne, amma yaya ake yin noman rani?
Hausawa na cewa “Noma na ɗauke da tsohon ciniki, noma tushen arziki, kowa ya zo duniya kai ya taras”
Menene Noma?
Noma yana da kuma ma’anoni da dama kasancewar irin amfaninsa a fannoni daban-daban. To, amma dai a fassara mafi sauki, za mu ce, Noma wata hanyar sana’a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika, noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin Da arzikin al’ummai suka raja’a a kan ta. A kasar hausa ko kuwa, noma shi ne babbar hanya ta samun haɓakar tattalin arziki. Da noma ne Hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci da ma kayayyakin da ake sarrafawa a masana’anta kamar tufafi da sauransu. A wajen hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen Kuma kowanne Bahaushe, musamman ma magidanci.
Kusan mu ce ma kowanne Bahaushe ya iya noma, ya kuma san yadda ake yin shi. Noma da Kiwo duk suna nufin abu daya ne a ma’anar da ilimin zamani ya samari.
shi noman damina ana yin sa ne a lokacin damina.
ga yadda ake yin noman damina.Da zarar an samu ruwan sama wato (damina ta fadi), manoma za su bazama gonakinsu domin yin huda da shuka. Akasari an fi shuka kayan abinci a wajen noman damina, to, amma akan shuka kayan sayarwa jefi-jefi.
Kayan Abinci kamar,
Masara
Gyaɗa
Gurjiya
rogo
Doya
Dankalin Hausa
Danja turawa
Makani
Dawa
Gero
Alkama
Shinkafa
Wake
Ridi
Auduga
Waken soya da sauransu.
Haka zalika ana shuka kayan miya da na marmari kamar haka,
Tattasai
Tumatir
Albasa
Attaruhu
Barkono
Kubewa
Alayyahu
Yakuwa
Lalo
Ayoyo
Karkashi
Salak
cabbage
Lansir da sauransu.
Kayan marmari kuma kamar haka,
Gauta
Yalo
gulli
Ɗata da sauransu.
Saɓanin Noman rani, noma ne da ake yin shi a lokacin rani ba da damina ba.
ga yarda ake noman rani.
Shi noman rani ana yin sa ne a wuraren da ruwa yake wadatacce kamar rafi
Korama , da madatsun ruwa wato (dam). Da zarar ruwan sama ya dauke wato kaka ta yi, manoman rani za su fara ne da share gonakinsu, daga nan kuma sai su yi kaftu, su ja kwamame, sai su shuka abin da za su shuka a cikin kwamame. Suna yin amfani da injinan ban ruwa wajen bai wa shukokinsu ruwa, har su girma, su isa girbi.
Akasarin abubuwan da ake nomawa a noman rani ana shuka su ne saboda sayarwa domin samun kudin shiga.
Ga irin abubuwan da ake nomawa da rani.
Kubewa
Albasa
Yalo
Tumatir
Karas
Tattasai
Rogo
Madalla.