Yi bayanin yadda ake haɗa miyar ɗanyar kuɓewa.
MIYAR KUƁEWA ƊANYA
Kamar yadda kowa ya sani girki ya kasu kashi-kashi, domin kowace mace da kalar yadda take girkinta.
Da a ce za’a kawo komai iri ɗaya, a bawa mata ace su girka, toh kowace zata yi irin salonta ne, misali, wata tana sanya maggi farkon girki, wata sai a ƙarshen girki take sanyawa, toh haka salon ya banbanta, don haka nima zan yi salona wurin koyar da miyar kuɓewa ɗanya.
Da farko dai uwargida zata tanaji abubuwa kamar haka.
Kuɓewa Ɗanya
Cefane
Nama
Spices
Mai (Man gyaɗa)
Maggi.
Da farko uwar gida zata wanke namanta tas, sannan ta ɗora shi a wuta, sai ta yanka mashi albasa, haɗe da ƴar dakakkiyar citta, da kuma maggi kaɗan, sai ta tafasa shi har naman ya tsotse ƴan ruwan da aka sa mashi.
Idan kuma da ruwa a jikinsa, toh ana iya sauke shi a haka, a kwashe shi daban.
Daganan uwargida zata ɗauko cefanen da ta jajjaga, wanda ya haɗa da tattasai, tarugu albasa da ƴar tafarnuwa, za a sa cefanen ba da yawa ba, domin kuɓewa bata son cefane sosai.
Sai a soya shi haɗe da mai, idan ya soyu sai uwar gida ta ɗauko naman nan da ta tafasa, idan da ruwa jikin naman sai ta juye shi cikin cefanen ta ɗan ƙara jujjuya shi, sannan ta ƙara da ƴan ruwa kaɗan, idan kuma ruwan naman ma sun isa shikenan.
Idan kuma naman bai da ruwa, sai ta tsaida ruwan miyan, sannan ta sa maggi irin wanda take so haɗe da spices. (Kada a manta kuma da daudawa ta gida ko ta kanti, don tana gyara miya)
Ɓangare ɗaya kuma ga kuɓewarta nan wadda ta gurza ta, ruwan na tafasa sai ta zuba kuɓewar ta jujjuya ta, sannan ta rufe, lokaci bayan lokaci ana buɗewa a juya har ta warware.
Yadda ake miyar kuɓewa kenan. Sannan wannan wadda ake cin tuwo ce.
Insha Allahu zan kawo yadda ke miyar kuɓewa ta cin shinkafa, ko kuma taliya.
Wani ɗan ƙarin haske, idan uwargida bata da nama ko kifi, toh zata iya sanya wake, shi ma yana ƙara zaƙin miya sosai.
Ma sha Allah!