Sabaya na ɗaya daga cikin Magungunan musulunci da ke gyara jikin mace, da kuma ƙara mata lafiya.
Toh ya ake yin wannan haɗi (Ingredients) na Sabaya?
Cikakken Bayanin Yadda Ake Haɗa Sabaya.
Abubuwan da za a nema don haɗa sabaya sun haɗa da:
1- Alkama
2- Waken Soya
3- Ɗanyar Shinkafa
4- Gyaɗa (kamfala)
5- Riɗi
6- Hulba
7- Madara
8- Zuma/Suga.
Measurements;
Alkama,
ɗanyar shinkafa,
waken suya,
dukkansu kwano ɗai-ɗai.
Riɗi,
gyaɗa,
hulba,
kowanne rabin kwano.
Yadda ake haɗawa:
Za a jiƙa alkama da ɗanyar shinkafa a waje ɗaya na tsawon awa biyar.
Ita kuma gyaɗa da riɗi a haɗe su waje ɗaya a soya sama-sama a bushe ɓawon gyaɗar.
Sai a tsame shinkafa da alkamar nan idan sun tsane sai a haɗe su da wannan soyayyen riɗi da gyaɗa da waken suya da hulba a kai inji a niko su.
Idan an kawo garin sai a dinga dama cokali uku kullum safe da yamma ana sha. Wajen damawar za a dama ne kamar za a yi talge.
Idan an sauke sai a saka madara da zuma ko suga a dinga sha.
Wannan hadi yana tayar da brest sosai ko shayarwa ake yi babu abin da nono zai yi, zai tsaya kyam In sha Allah.
Sannan yana gyara jiki ya yi sumul-sumul kamar jikin kulɓa, ya yi fresh sosai, sannan jiki ya murje duk wata rama In sha Allah.
A taƙaice wannan shi ne yadda ake haɗa garin sabaya.