Akwai wasu alamomi da ake gane soyayya ta hanyar su.a duk lokacin da mace ko na miji suka ga wannan alamun yana nufin tana son shi ko yana sonta.
wane alamomi ne waɗannan?
Soyayya guda biyu ce, wato soyayyar gaskiya, da kuma soyayyar ƙarya, sannan kowace akwai manufar da ta sa ake yin ta.
Soyayyar gaskiya ana gina ta ne domin Allah, tare da manufar kasancewa da juna har abada (Aure), sai dai idan Allah bai nufa ba. Soyayyar ƙarya kuma ana gina ta ne da wata manufa, wadda da zaran an cimma manufar za a rabu.
Sai dai alamomin duka waɗannan soyayya iri ɗaya ne, bambancin shi ne aiwatuwar manufar da ta sa aka gina soyayyar. Ga kaɗan daga cikin waɗannan alamomi:
Alamar farko ita ce ka ji kana son mutum a ranka, duk lokacin da ka ganshi ko kuma ka ji labarinsa zaka yi farinciki a ranka, har ma ka na ware lokaci na musamman don yi tunanin wannan mutum. Da zaran ka ji haka, to tabbas ka kamu da so. Yadda zaka fara gane wani na son ka kuma shi ne zai riƙa kulawa da kai, wanda shi ne alama ta biyu.
Kulawa na cikin alamomin da suke sa a gane soyayya. Babban burin wanda ya kamu da soyayya shi ne ya kula wanda yake so, daga cikin hanyoyin kulawar: shiga cikin lamarin wanda kake so, sannan a kwai yawan kyauta d.s, waɗannan na daga cikin hanyoyin kulawa, waɗanda suna faruwa ne tun kafin a furta soyayyar da baki.
Alama ta uku ita ce furtawa, wanda ya kamu da so baya samun nutsuwar zuciya har sai ya furta, domin furtawar ita ce cikamakin soyayya. Kuma ita ce babbar alamar da take bayyana soyayya. Don ka ƙi faɗa ma wanda kake so, ba lallai ne ya gane ba, amma da zaran ka furta, za a gane inda ka dosa, kuma furtawar ce zata sa a tuna irin kulawar da ka bada a baya, daga nan ne kuma idan da rabo sai ka ga ka samu karɓuwa.
Waɗannan su ne alamomin gane soyayya. Shin kai ake so, ko kai ne son wata. Waɗannan su ne alamomin. Da fatan Allah ya haɗa mu da masoya na gari Amii
iiin.