Funkaso yana daya daga cikin nau’in abincin da za mu kira shi da na gargajiya. Haka nan abinci ne mai daɗin dandano a baki, kuma mai kyawu a idanu. Funkaso yana da farin jini musamman a yi shi a wurin taro, ko biki, ko suna, ko abin da ya danganci haka.
YADDA AKE FUNKASO:
KAYAN HADI:
Alkama (kamar gwangwani hudu)
Filawa (gwangwani daya ko biyu)
Ruwan tsamiya (kamar Rabin gwangwani)
Yeast (cokalin shayi)
Sikari (cokali daya) Idan ana bukata
Ruwan kanwa (cokali daya)
Man suya (kwalba daya ko fiye da haka)
YADDA AKE HADAWA:
Ki samu robarki mai murfi ki zuba sikarinki da yeast da ruwan tsamiya da kanwa, kamar
yadda na fada a sama. Ki dauki filawarki ki hada ta da garin alkamarki, idan yeast ya narke ki juye filawarki ki kwaba sosai ki tabbatar babu gudaji kuma kar kwabin ya yi ruwa kar kuma ya yi tauri tikiki. Sai ki rufe ya samu kamar awa daya za ki ga ya tashi.
Ki dora manki a wuta ya yi zafis sosai, ki samu kwabin ki kara juya shi sosai za ki ga ya koma ya kwanta, kuma za ki ga a yayin da kika dada juya shi kwabin ya ake sakin jikinsa. Sai ki samu dan farantinki ki shafe shi da ruwa ki dinga gutsurar kullun funkason kina saka wa a kan dan farantin, ki huda tsakiya sai ki saka a cikin mai. Za ki ga yana dagowa yana fada wa cikin mai a hankali.
Abin lura a nan shi ne; funkaso ba ya son yawan juyawa, idan kin ga kasan ya soyu sai ki juya saman shi ma ya soyu, kuma funkaso ba ya son mai kadan wajan suya ya fi son mai wadatacce ya sakata ya wala, amfanin tsamiya a funkaso shi ne ba zai taba sha miki mai ba, kuma zai miki suya ta yi ja ta yi kyau.
Adadin awon da na yi a haka za ki yi shi, idan da yawa za ki yi shi to haka
za ki dinga aunawa kina kara yawan abin da na lissafo miki.
Wannan shi ne yadda ake yin funkaso mai daɗi. A ci daɗi lafiya.