Waɗanne shirye-shirye ake yi in mai ciki ta kusa haihuwa?
Da zaran mace ta samu juna biyu, toh an fara shiri kenan a al’adance da kuma lafiyance, domin ganin ta rabu da wannan cikin lafiya, ba tare da samun naƙasu a gare ta ko jaririnta ba.
Da zaran kuma ciki ya tsufa, wato lokacin haihuwa ya gabato, za a ci gaba da shiri na musamman har Allah ya sa a haihu lafiya, daga cikin shirin da ake yi ma mai juna biyu akwai:
A lafiyance za a cigaba da bata kulawa, ta hanyar zuwa awon ciki, domin tabbatar da lafiyarta da kuma ta jaririnta. Waɗanda kuma babu tsarin zuwa a asibiti a wurinsu, su kan yi amfani da magungunan gargiya, domin hana mai jego da jaririnta faɗawa cikin lalurarar da ka iya naƙasta su, ko kuma kaiwa ga rasa rayuwarsu. Wannan kulawa kuma za ta fara ne tun daga samun cikin har zuwa haihuwar sa.
Yayin da ciki ya kai matakin haihuwa kuwa, toh a lafiyance za ta riƙa ziyartar asibiti akai-akai, idan a can baya tana zuwa duk bayan mako huɗu, toh za a mayar da shi duk bayan mako biyu, ko kuma ɗaya, duk don a tseratar mata da lafiyarta ita da ɗanta. Sannan a al’adance zata koma gida idan haihuwar fari ce, ko kuma a kawo wata Dattijuwa ta zauna tare da ita, idan kuma ta taɓa haihuwa, zata dasu a akan tsari, na shan magungunan gargiya masu sauƙaƙa haihuwa.
Sannan idan haihuwa ta gabato ne ake tsara shirin hidimar haihuwar, za a nemi kayan wankan mai jego da na jariri, sannan za a daka yajin jego a aje, sannan mai jego zata yi ɗinkuna, da kuma siyen kayan baby.
Maigida zai sayi iccen wanka, tare da ragon suna, sai kuma abincin da za a yi hidimar tarɓar baƙi da shi, da kuma gero na kunu.
Dukkan wannan shirin ana yin shi ne idan haihuwa ta gabato ga wanda yake da iko. Da zaran haihuwar ta zo kuma za a nufi asibiti, idan kuma haihuwar gida ce, toh za a kira unguwar zoma ta gargajiya ta kula da mai cikin, tare da ɗora ta a kan yadda zata haihu cikin sauƙi.