Wane nau’in abinci ne ya kamata mai son rage ƙiba ya riƙa ci?
Mun sani cewa kiba idan ta yi yawa takan zamo cuta ga me ita. Kuma sau da yawa abinciccikan da muke ci ne suke jaza mana kiba. Don haka akwai abincin da ya kamata mu dinga ci wanda zai rage mana wannan kiba ya daidai mana jikinmu. Akwai kuma abincin da ya kamata mu rage ci saboda yana ƙara mana kiba.
Haka nan akwai wasu abubuwa da ya kamata a kiyaye wajen rage kiba, duk da ba su danganci abinci ba.
Abincin da ya kamata mu dinga ci don rage kiba. Da kuma abincin da ya kamata mu rage ci don rage kiba. Da kuma abubuwan da ya kamata a yi su ko a daina yin su domin rage kiba:
1- Rage amfani da abinci mai dauke da sugar da yawa yana taimakawa wajen rage kiba sosai.
2- motsa jiki (exercise) na daga cikin hanyoyin da za a bi domin rage kiba.
3- Amfani da kayan lambu (ganyayyaki) irin su salad, da cabbage yana taimakawa sosai wajen rage kiba.
4- Rage amfani da abinci mai kitse yakan taimaka sosai wajen rage kiba.
5- Amfani da ‘ya’yan itatuwa fiye da abinci yakan rage kiba sosai. Musamman irin su; apple, lemo, strawberry, gwanda, cucumber, carrot, kankana, yalo, da sauran su.
6- A samu isasshen barci saboda sabon bincike ya nuna cewa rashin barci sosai yakan taimaka wajen kara kiba.
7- Amfani da ruwan shayi (tea) da lemun tsami yakan taimaka wajen rage kiba sosai.
8- A dinga yin break fast da kwai (egg) yakan taimaka wajen rage kiba domin zai sa kusan a wuni ba a nemi abinci ba.
9- A dinga shan ruwa sosai, idan so samu ne kafin cin abinci a sha ruwa kamar kofi daya zuwa biyu zai taimaka wajen rage kiba.
10- A rage amfani da lemun kwalba ko na roba irin su coke, fanta, da sauransu.
11- A daina cin abincin dare a kurewar lokaci sannan a kwanta. Zai fi kyau a ci abincin dare karfe bakwai domin ya narke kafin a kwanta.
12- A daina kwanciya daga zarar an ci abinci, yana da kyau idan aka ci abinci a bar shi ya narke kafin a kwanta, walau abincin safe, rana, ko kuma dare.
Idan aka bi wadannan shawarwari da hanyoyi, in sha Allah za a rage kiba ta daidaita. Kuma za a samu ingantacciyar lafiya. Ba za a yi ƙiba mai cutarwa ba. Bahaushe ya ce sai an gwada akan san na kwarai.