Wani irin bambancin sinadaran girki ake samu wajen girka miyan yakuwa da rama?
Akwai bambancin sinadaran girki tsakanin miyar YAKUWA da miyar RAMA. Za a fahimci bambancin ne ta hanyar kawo yadda ake yin miyoyin da kuma sinadaran da ake amfani da su a wajen yin su.
MIYAR YAKUWA
Yakuwa tana daga cikin ganyayyakin da akan samu a muhallin Bahaushe, ɗanɗanonta yana da ɗan tsami, baya ga haka tana da ɗan yauƙi-yauƙi musamman idan tana ɗanya. Tana ɗaya daga cikin tsirran da Bahaushe ke shukawa musamman da damina.
Akwai abubuwan da ake buƙata idan za a gudanar da miyar yakuwa. Waɗannan abubuwa su ne kamar haka:
Albasa
Daddawa
Gishiri
Kayan yaji
Mai
Ruwa
Attaruhu
Tattasai
Wake
YADDA AKE YI:
Idan ganyen yakuwar ɗanye ne akan wanke shi ne kai tsaye, idan kuma busasshe ne akan tafasa shi cikin ruwan zafi daga nan sai a wanke shi. Ana iya daka busasshen ma luƙui tamkar garin kuka, a irin wannan yanayi ana kaɗa shi ne kamar yadda ake kaɗa miyar kuka.
Za a samu wake mai ɗan dama gwargwadon yawan miyar da ake so a yi. Za a surfa wannan waken sannan a wanke, a kuma cire hanci da ɓawon. Za a tanadi kayan yaji a dake su, sannan a markaɗa ko a jajjaga kayan miya nau’o’in da aka ambata.
Za a saka mai a cikin tukunya tare da albasa, da zarar ya so yi za a zuba kayan miya waɗanda aka markaɗa ko aka jajjaga, idan suka soyu sai a zuba kayan yaji da wadatacciyqr daddawa. Daga nan sai a motsa sosai har sai daddawar da aka sanya ta haɗe, sai a zuba ruwa gwargwadon miyar da ake son samarwa.
Bayan haka, za a saka gishiri. Daga nan za a bar miyar tai ta tafasa. Idan da nama za a yi ko kifi a wannan gaɓar ne za a sanya, idan nama ne da ma tuni an silala shi, idan ɗanyen kifi ne tuni an tafasa shi ko kuma an soya shi.
Idan miya ta ɓararraka za a ɗauko dakakken ganyen yakuwar a dinga kaɗawa a ruwan miyar. Sai kuma a rufe tukunyar a bar ta ta yi minti talatin ko sama da haka tana dahuwa, saboda ana so a bar ta sosai ta yi dahuwa mai kyau.
Da zarar ta yi sai ci.
Haka nan akwai wata hanyar da ake bi domin sarrafa miyar yakuwa, ga ta kamar haka:
MIYAR YAKUWA.
Kayan haɗi:
Kifi(ɗanye)
Yakuwa
Maggi
Attarugu
Tattasai
Albasa
Ganyen albasa
Tafarnuwa
Daddawa
Kayan kamshi
Kuli kuli
Manja
Da farko za a yi jajjagen kayan miya, a ɗora tukunya a wuta a zuba manja da albasa a zuba jajjagen a soya sosai.
Bayan jajjagen ya soyu za a zuba ruwa (mai ɗan dama) a zuba su maggi da gishi, za a zuba kayan ƙamshi da daddawar da aka daka.
Bayan an saka komai za a zuba ɗanyen kifin a rufe tukunya, a bar miyar ta yi ta dahuwa.
Idan miyar ta daɗe tana dahuwa, za a buɗe a ga idan ruwan miyar ya kai yadda ake son yawan miyar.
A wannan lokacin za a cire kifin da ke cikin miyar a ajiye gefe, za a zuba ƙulin da aka daka a cikin miyar, a nan kuma za a zuba yakuwar da aka wanke aka gyara haɗe da ganyen albasa sai a rufe miyar.
Bayan kamar minti talatin haka za a buɗe tukunyar a sa whisker a yi whisking sosai da sosai, a nan za a mayar da kifin a miya a juya sannan a rage wuta sosai.
Bayan mintuna uku zuwa huɗu za a ga mai ya taso saman tukunya, miyar ta yi kenan, sai a sauke.
MIYAR RAMA.
Dangane da miyar rama kuwa ga yadda take:
Kayan haɗi.
Rama
Danyen barkono
Attarugu
Tumatur
Albasa mai yawa
Man ja
Daddawa
Gishiri
Dandano
Shambo
leaf Water
Citta/tafarnuwa
YADDA AKE YI:
Ki yanka rama sai ki sa ɗan ruwa a wuta ki tafasa ganyen ramar kamar na minti 3, ki juye ki matse ruwan da ke jikin ramar. (Ki yi amfani da hannunki wajen matse ruwan da ke jikin ramar sai ki sake warware ganye)
Ki yanka water leaf and set a set.
Ki jajjaga attarugu, tumatur kaɗan, ɗanyen barkono da shambo sama-sama. Ki yayyanka albasa mai yawa. Ki sa manja a wuta idan ya yi zafi sai ki sa ‘yar albasa da citta da tafarnuwa ki ɗan soya su, idan albasar ta yi laushi sai ki zuba ragowar albasa da jajjagen kayan miyarki ki sake soyawa kamar na minti 2, sai ki tsayar da ruwa ki sa gishiri, ɗanɗano, da daddawa, sai ganyen rama da kika tafasa. Ki sa ruwan da yawa saboda rama tana da tauri, ki rufe tukunya ki bar ta ta dahu har sai ta shanye ruwan.
Idan ta shanye ruwan sai ki zuba water leaf ki juya sosai ki sake ba ta minti biyu ta ƙarasa.
Da fatan an gane bambancin sinadaran haɗa wannan miyoyin.