Wane shiri ya kamata Mumini ya yi ma Azumin Ramadan da ke gabatowa?
Shirin da ya kamata mumini ya yi wa watan Ramadana da ke gabatowa shi ne:
Tun da fari ya kamata mu sani cewa. Watan Ramadana wata ne mai girma, cikinsa ne ake bude kofofin Aljanna, kuma ake rufe kofofin wuta, wani irin wata ne da Allah ya fifita shi a kan sauran watanni, cikinsa ne Allah yake yi wa mutane falala iri-iri domin ya bude musu kofofin fata da sa ran ‘yanta su daga wuta. Allah yakan ‘yanta wasu daga cikin bayinsa daga wuta , a kowane dare daga cikin dararensa. Don haka ya dace ga kowane musulmi ya yi kyakkyawan tanadi ga wannan wata mai alfarma kafin zuwansa, domin shi bako ne mai daraja, baya zuwa sai sau daya a shekara.
Allah Ta’ala Yana cewa:
( شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآَنُ هُدًى لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ يُرِيدُ اللَّهُ بِكُمُ الْيُسْرَ وَلَا يُرِيدُ بِكُمُ الْعُسْرَ وَلِتُكْمِلُوا الْعِدَّةَ وَلِتُكَبِّرُوا اللَّهَ عَلَى مَا هَدَاكُمْ وَلَعَلَّكُمْ تَشْكُرُونَ 185 ) [البقرة: 185]
(Watan Ramadan wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa a matsayin shiriya ga mutane da bayyanannun ayoyi daga shiriya, da mai rarrabewa tsakanin gaskiya da qarya, duk wanda azumi ya riske shi a halin zaman gida to ya azumce shi, wnda kuwa ya kasance mara lafiya ko a bisa tafiya, to ya rama a wasu kwanakin na daban, Allah yana nufin sauqi ne da ku ba ya nufin qunci da ku ba, sannan kuma domin ku cika adadin (kwanakin azumin), kuma ku girmama Allah a bisa shiriyar ku da ya yi, kuma tsammaninku za ku gode).
Ya wanda fakuwarsa ta tsawaita ga barin mu! Kwanakin sulhu sun gabato. Ya wanda asararsa ta dawwama! Hakika kwanakin kasuwanci mai riba sun gabato. Ya wanda bai ci riba ba a cikin wannan wata! To a cikin wane wata ne zai ci riba? Duk wanda bai kusanci Ubangijinsa a cikin wannan watan ba, to har abada ma ba zai kusance shi ba.
Hakika mun fuskanci wani wata mai girma, da yanayi mai cike da riba mai girma ga wanda Allah Ya datar da shi ga aikata aiki na kwarai. Mun fuskanci watan Ramadana, wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa. Wata ne da ake ninka kyawawan ayyuka a cikinsa. Kuma ake girmama munanan ayyuka a cikinsa. Allah Ya sanya azumtar yininsa farilla ce daga rukunan musulunci, kuma tsayawa a dararensa nafila ce don kammala farillanku. Duk wanda ya azumce shi don ba da gaskiya da neman ladan Allah, Allah zai gafarta abin da ya gabata daga zunubansa. Wanda kuma ya tsaya darensa, yana mai imani da neman lada, Allah zai gafarta masa abin da ya gabata daga zunubansa. Wanda ya yi Umara a cikinsa, kamar wanda ya yi hajji ne. A ciki ne ake bude kofofin Aljanna, ayyukan biyayya kan yawaita daga ma’abota imani. Ana kulle kofofin wuta, sai sabo ya yi karanci daga ma’abota imani. Ana daure shaidanu, ba za su sami damar isowa zuwa ga masu imani ba, irin yadda suke isa zuwa gare su a wasu lokutan.
Bukhari ya rawaito hadisi daga Abu Huraira, ya ce, Manzon Allah tsira da amincin Allah ya ce, Allah ya ce, “Duk wani aikin dan’adam nasa ne, ban da azumi, domin shi nawa ne, kuma ni ne nake sakawa a kansa. Kuma azumi garkuwa ne, idan ranar azumin dayanku ta kasance, kada ya yi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya zage shi ko ya neme shi da fada, to ya ce, ni ina azumi. Na rantse da wanda ran Muhammadu ke hannunsa, hakika rihin bakin mai azumi ya fi kamshi a wajen Allah fiye da kamshin almiski. Mai azumi yana da farin ciki biyu, da yake yinsu. Idan ya yi buda-baki zai yi farin ciki da shan ruwansa, idan kuma ya gamu da Ubangijinsa, zai yi farin ciki da azuminsa”.
Ya zo a cikin Sahihil Bukhari, daga hadisin Abdullahi dan Amru (R.A), cewa Annabi (ﷺ) ya ce, “Kada ku yi azumi har sai kun gan shi, idan an muku lullumi, to ku cika lissafin talatin.”
Haka nan ya ruwaito daga Abu Huraira daga Annabi S.A.W, ya ce “Idan ya buya a gare ku, to ku cika lissafin Sha’aban talatin.” Kuma Ammar bin Yasir ya ce: ” Duk wanda ya azumci ranar da ake kokwanto a cikinta to, hakika ya sabi Baban Qasim (ﷺ)”
Duk wanda ya ga jinjirin wata to, ya sanar da shugaba, kada ya boye. Idan aka sanar a rediyo cewa an ga wata, to a yi azumi. Idan kuma aka sanar cewa an ga watan Shawwal to a sauke. Domin sanarwar shuwagabanni kamar hukunci ne a kan hakan.
Abu ne sananne ga kowane musulmi cewa, azumin Ramadan daya ne daga cikin rukunan musulunci da Allah ya wajabta shi a bisa bayinsa. Saboda haka duk wanda ya musa wajabcinsa to shi kafiri ne. Domin ya karyata Allah da Manzonsa da haduwar Musulmi. Allah Ta’ala ya ce:
( يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آَمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ 183 ) [البقرة: 183]
(Ya ku wadanda suka yi imani, an wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabatawa wadanda suka gabace ku, lalle za ku samu taqawa).
Kuma ya ce:
( شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآَنُ هُدًى لِلنَّاسِ وَبَيِّنَاتٍ مِنَ الْهُدَى وَالْفُرْقَانِ فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ وَمَنْ كَانَ مَرِيضًا أَوْ عَلَى سَفَرٍ فَعِدَّةٌ مِنْ أَيَّامٍ أُخَرَ ) [البقرة: 185] .
(Watan Ramadana wanda a cikinsa aka saukar da Alqur’ani domin shiriya ga mutane da bayyanannun ayoyi daga shiriya, kuma mai rarrabewa tsakanin karya da gaskiya, duk wanda ya zama mazaunin gida a kwanakin watan to ya azumce shi…).
Don haka azumi wajibi ne a kan kowane musulmi, baligi, mai hankali, mai iko, mazaunin gida, namiji ne ko macen da ba ta jinin haila, ko na biqi (a lokacin) azumin. Ba ya wajaba a kan kafiri, amma da zarar ya musulunta a tsakiyar rana to ya kame bakinsa a ragowar yininsa, amma ba zai rama wannan ranar ba.
Hakika Annabi (ﷺ) ya kwadaitar a bisa tsayuwar dare a wannan wata ya ce: “Duk wanda ya tsaya a Ramadana yana mai imani, da kuma neman lada, to za a gafarta masa abin da ya gabata na zunubinsa.” Haka nan sallar Asham ko Tarawihi, tana daga kiyamu Ramadana. Ya kamata ku tsai da wadannan salloli ku kyautata su, ku tsaya tare da limaminku har sai ya idar, domin duk wanda ya tsaya tare da limaminsa har ya kare, to za a rubuta masa ladan tsayuwar dare cikakke, ko da kuwa ya yi barci.
Bukhari da Muslim sun ruwaito daga Annabi (ﷺ), ya ce: “Lallai a cikin aljanna akwai wata kofa da ake ce mata Rayyan. Masu azumi ne kawai za su shiga ta cikinta, babu mai shiga cikinta ban da su.” A wata ruwayar kuma, “Wanda ya shiga zai sha abin shan da ba zai yi kishi ba har abada.”
Hakika wata azumi yana da kebance-kebancensa saboda Alqur’ani, kamar yadda Allah Ta’ala Ya fada:
( شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآَنُ ) [البقرة: 185]
“Watan Ramadana wanda aka saukar da Alqur’ani a cikinsa.”
Haka nan dan Abbas ya ce: “Hakika an saukar da shi jimilla guda daga Lauhil Mahfuz zuwa Baitul Izzah a daren Lailatul Qadari, shaidar haka, fadin Allah Ta’ala:
( إِنَّا أَنْزَلْنَاهُ فِي لَيْلَةِ الْقَدْرِ 1 ) [القدر: 1]
“Hakika mun saukar da shi a daren Lailatul Qadri”.
Zuhri ya kasance idan Ramadana ya shigo sai ya ce, “Ramadan wata ne kawai na karanta Alqur’ani da ciyar da abinci.”
Ibnul Hakam ya ce: “Maliku ya kasance idan Ramadana ya shiga yana kaurace wa karatun hadisi, da zama da daliban ilimi. Ya mai da hankalinsa a kan karantun Alqur’ani daga Mus’hafi.”
Watan Ramadana watan horarwa ne a kan ciyarwa da yawan kyauta, domin ya zo a cikin Bukhari da Muslim daga dan Abbas Allah ya yarda da shi ya ce: Annabi (ﷺ), ya kasance mafi kyautar mutane da alheri. Kuma lokacin da ya fi kyauta shi ne da Ramadana, yayin da Jibrilu ya gamu da shi. Jibrilu ya kasance yana gamuwa da shi a kowane Ramadana. Sai ya yi karatun Alqur’ani tare da shi. Lallai Manzon Allah (ﷺ) ya fi sakakkiyar iska kyauta, yayin da Jibrilu yake gamuwa da shi.
WALLAHU TA’ALA A’ALAM.