Wane shiri ya kamata mace ta yi kafin ta shiga gidan aure a matsayinta na sabuwar Amarya? Tun daga fannin kula da lafiyarta da kuma ƙawata jikinta, ta yadda zata zama tauraruwa a wurin mijinta.?
Shirin Da Ya Kamata Mace Ta Yi Kafin Ta Shiga Gidan Aure.
‘Yan mata da dama suna aure ne ba tare da sun yi wani shiri ko sun nemi sanin wasu abubuwan da ya kamata su san su ba domin inganta zaman aurensu.
Hakan ya sa wasu mazan da ke tsammanin sun auri macen da ta san mahimman abubuwan da ke inganta aure sai su ga ba haka ba. Wasu mazan su kasa hakuri su karo wani auren ko kuma su hakura da zama da wacce suka auro.
Yana da kyau tun kafin mace ta shiga gidan aure ya kasance ta sha maganin sanyi domin tsarkake mararta daga dukkan wani infection da zai dame ta ita da mijinta, haka nan ta koyi yadda za ta dinga gyara jikinta domin janyo hankalin mijinta gare ta, ta hanyar kwalliya da ƙamshi da kuma wasu abubuwa da za su biyo bayan auren, wadanda suka kasance na halayya kamar haka:
1. Tsafa- Dole ne duk wata ‘ya mace ta koyi tsaftace jikinta da kuma muhallinta.
Wasu matan musamman wadanda suka fito daga gidajen alfarma ana samun su da rashin iya tsaftace jiki da muhalli saboda yadda suka saba da a yi musu hidima, wanda hakan ba daidai ba ne a tarbiyya ta ‘ya mace.
Duk gatan ‘ya mace yana da kyau ta zama mai kokarin tsaftace jikinta da kuma na muhallinta domin idan za a iya kular mata da muhalinta ba za a kula da jikinta ba. Ko muhallin nata ba ko ina ba ne za ta ba da damar a shiga ba ko a gani.
2. Ilimi- Yana kan gaba ga kowace mace ta samu ilimi kafin ta yi aure.
Illimi na addini ya wajaba a kan iyaye su koyar da ‘yarsu kafin ta shiga gidan miji. Haka shi ma illimi na zamani yana da amfani matuka a wannan lokacin da wasu mazan ba su da hakuri da jimirin rike aure.
Duk macen da ba ta da illimi zai yi wuya ta iya mu’amala da mijinta ballantana sauran mutane. Haka kuma abin da za ta haifa suna cikin matsala na yadda uwarsu ba ta da illimin da za ta koyar da su ballantana ta ba su tarbiyya.
3. Abin Yi- Lokaci na dogaro ga miji ko iyaye ya wuce. Hakan ya sa kafin mace ta yi aure ta tabbatar da cewa tana da wani abin da ta iya a rayuwarta da zai samar mata da kudaden shiga.
Dogaro da mata suke yi karankatakaf a kan miji na wasu bukatun da ba wajibi ba ne a kan mazansu shi yake jawo rashin fahimta tsakanin ma’aurata wani lokacin.
Wannan yasa duk namijin da kika san ba zai bar ki ki yi aiki ko sana’a ba ki hakura da shi kawai domin Allah bai hana mace neman kudi ba.
4. Hakuri- Duk macen da ba za ta koyi hakuri ba tabbas ba za ta iya zaman aure ba.
Zaman aure gaba dayansa a kan hakuri ake yin shi kowane irin miji kika aura kuwa.
Dole ne wani abun kina gani ke ce da gaskiya amma za ki hakura ki dauki laifin domin a zauna lafiya.
5. Iya Mu’amala – Yana da kyau ki iya mu’amala da mutane kafin ki yi aure.
Idan kina gidan aure duk wanda yazo gidanku tarbar da za ki masa shi ne abin da zai sa ya sake dawowa ko ya ki dawowa.
Ki sani a gidan mijinki ba ke kadai ce za ki yi rayuwa ba. Akwai abokai da ‘yan uwan miji. Akwai makota ko masu yi muku hidima idan masu akwai ne. Dukkanin wadannan mutane dole sai kin iya mu’amalar zama da su kafin ki zauna da kowa lafiya, musamman ma a ce kina da abokan zama.
6. Girki- Duk wanda ya ce miki aikin mace a gidan mijinta babu girki yaudarar ki yake yi. Idan har Matan Manzon Allah (SAW) za su yi masa girki har abokansa su zo su ci, kamar yadda ayar Alkurani ta ba mu labari, ina ga ke?
Haka nan ta wajen girki ake kara shiga zuciyar namiji. Matar da ta iya sarrafa abinci da kayan sha ba daya take da wadda ba ta iya ba a wajen mijinta.
Duk namijin da ya san matarsa ta iya girki da wuya ki same shi yana cin abinci a waje. Koyo da iya girki kala-kala kafin ki yi aure wajibi ne muddin kina burin ganin kin zauna a gidan aure.
7. Kyauta- Yana cikin abin da ake so duk wata mace ta iya kafin ta yi aure.
Kada ki zama mace marowaciya, kuma mai kwauro. Idan kika yi aure da wannan halin ba ma masu ziyartar gidanku ba hatta mijinki da yaranki ba za su ji dadin ki ba.
Ba ana nufin ki yi kyautar shiga daka ki yi kuka ba. Ki bayar da abin da kika fi karfinsa. Haka abinci kada ki zama mai rowar shi ko kwauron shi, duk wanda ya shigo gidanki ya fita a koshe muddin akwai wadatar abincin.
8. Adani- Ko takarda kika gani a kasa ta mijinki samu waje ki adana masa wata rana zai nema.
Haka nan duk wani abinci da kayan da aka bari a karkashin kulawarki ki zama kina kula da su yadda ya dace.
Ba kuma za ki iya wadannan abubuwan ba har sai idan kin koya tun daga gidanku. Don haka kafin ki yi aure Ake so ki yi shiri sosai domin ki samu zaman lafiya da jin daɗin auren.
9. iya Magana- magana da miji ba daya take da yadda za ki yi magana da iyayenki ko kawayenki ba.
Akwai wasu kalmomin da duk irin yadda mijinki yake da sakin fuska da wasa ba za ki furta masa su ba. Haka akwai kalmomin da duk irin dacin ran mijinki ba za ki fada masa su ba. Don haka koyo da sanin kalaman da ake furtawa masoyi neman sanin su ake yi daga lokacin da kike soyayya har zuwa rayuwar aurenki.
10. Jima’i – Wani abu mai matukar mahimmanci da kuma karancin samun damar koya wa ‘ya mace shi kafin aure.
Iyaye musamman mata sukan kasa fitowa fili su nuna wa ‘ya’yansu mata abubuwan ki da wadanda ake so mace ta yi su a lokacin gudanar da Jima’i da mijinta. Duk da ana samun wasu iyayen da suke bai wa wasu tsofi dama wajen illimantar da ‘yan mata Jima’i kafin aure.
Rashin karantar da ‘yarki mahiman abubuwan da suka dace ta sani game da Jima’i kafin aure zai iya cutar da rayuwar aurenta musamman idan mai mata za ta aura, ko wanda ya taba aure. Don haka yana da kyau iyaye mata su cire kunya da tsoro su karantar da ‘ya’yansu abin da ya dace su sani game da Jima’i kafin aure.
Idan har mace ta riki wadannan abubuwa, su ne tsanin da za ta taka ta zama tauraruwa a wurin mijinta.