Shin shan taba sigari da cin goro yana da illa ga lafiyar mutane? Idan yana da ita mece ce illar?
Shan taba sigari ba abu ne mai kyau ba ga lafiyar Ɗan adam, domin illar farko da take da ita shi ne “Masu shan taba suna yawan mutuwa da ƙuruciyarsu”, kamar yadda masu kamfanin tabar suka faɗa da kansu, kuma mutuwa da ƙuruciya ba abu ne da kowa ke so ba, sai wanda Allah ya ƙaddara mawa.
A Addinance kuwa shan taba na cikin nau’in almubazzaranci, domin babu wani amfani da take da shi a jikin Ɗan’adam, sai dai asarar kuɗaɗe, shi kuma almubazzaranci haramun ne a musulunci, domin Allah Maɗaukakin Sarki ya ce “Kada ku yi almubazzaranci, domin masu yin almubazzaranci ƴan uwan shaiɗan ne, shi kuma shaiɗan ya kafirce ma Ubangijinsa.”
Wata uwa da take yi ma ɗanta nasiha ta ce “Shan taba sigari daidai yake da ka ɗauki kuɗinka ka cinna musu wuta”, ta cigaba da cewa “Kai gwara ma ka cinna ma kuɗinka wuta zai fi, domin hakan ba zai cutar maka da lafiya ba, saɓanin shan taba sigari da ke haifar da cutuka masu illah.”
Don haka shan taba sigari a Addinance haramun ne, domin daidai take da almubazzaranci, sannan jefa kai a halaka ne, kuma Allah Maɗaukakin Sarki ya ce “Ka da ku jefa kanku a halaka.”
A lafiyance kuwa shan taba sigari na kawo kansar hunhu (Lung cancer), tana haifar da tarin tibi (Tuberculosis), sannan tana kawo warin baki, da ma Cancer ta baki, wani likitan musulunci ya ce “Matan da mazansu ke shan taba wuya suke sha, musamman a wurin shimfiɗa, saboda bakinsu wari yake.”
Daga ƙarshe kuma tana kawo lalacewar fata, domin mai shan taba jikinsa ya kan yi baƙi, ta yadda da an gansa ake ganewa.
Don haka babu wani alfanu a shan taba sigari, sai ma muguwar illar da take da ita. Da fatan Allah ya tsare mu Amiiiiin.