Wace irin Illa ce yin TikTok yake yi ma rayuwar ƴa mace a addinance da kuma al’adance??
Illar Tiktok Ga ‘Ya Mace.
Manhajar Tiktok wata babbar kafa ce da jama’a ke baje-kolinsu a ciki, wasu sun dauke ta hanyar isar da sakonni na Musulunci da karance-karancen addini. Yayin da wasu suke yada fasadi da aikata munanan abubuwa, musamman bayyana tsiraici da raye-rayen da ba su kamata ba. Mata da yawa da suka kasance matan aure ko ‘yammata suna aikata ba daidai ba duk da cewa suna iƙirarin isar da sako suke yi.
Haba ‘yar’uwa! Yaushe surar jikinki ta zama mahaɗin isar da saƙo? Mene ne amfanin isar da saƙon da zai zama sanadiyar saka wasu su saɓa wa Allah kuma ke ma ki saɓa masa? Mene ne amfanin bayyana tsiraicin da Allah Ya hane ki da bayyana shi idan har ba ga mijinki ba? Kin sani cewa a matsayin ki na ’ya mace surar jikinki ba abar tallatawa ba ce a cikin gidanku ma ballanta shafukan sada zumunta wurin da ba shi da tsafta ko kaɗan‚ ke kuma a wurin ne za ki yada zango ki talla ta surar jikinki domin samun ‘Followers’ a matsayin ki na halitta mai tsafta? Kin sani cewa wannan surar taki fitina ce da take halakar da al’umma in aka talla ta ta a muhallin da bai dace ba? Kin san adadin mutanen da suke yabon surar jikinki a kafar Tiktok in kika saki Video? Kin san adadin mutanen da suke kallon Vedionki domin yana kwantar musu da sha’awa?
Buɗe tsiraicinki babu abin da zai janyo miki sai saurin lalacewa kwatankwacin wayar da ba ta samu tagomashin kangewa ba. Bari na ba mu wani misali da wata ƙaramar hikaya kamar haka:
Wata budurwa ce ta sayi sabuwar waya kirar iPhone, da mahaifinta ya gani, sai ya tambaye ta.
“Shin mene ne abu na farko da kika yi a lokacin da kika sayi wannan wayar?
Sai ta ce, “Na sanya mata ‘Screen guard’ Don ba ta kariya daga tsagewa da kuma rigar waya ‘cover”.
“Wani ne ya tilasta miki yin haka?”
“A’a.”
“Ba kya ganin wannan cin fuska ne ga kamfanin da ya kera wayar?”
“A’a baba! A zance na gaskiya ma su ne ke bada shawarar yin amfani da wadannan ababen don bai wa wayar kariya.”
“Shin kina rufe ta ne saboda tana da arha ko ta yi muni?”
“A’a gaskiya, ina rufe ta ne saboda ba na so ta lalace ko kuma darajarta ta ragu.”
“Lokacin da kika sanya mata riga (cover), shin ya rage kyawun iPhone din?”
“Ina tsammanin ma ta fi kyan gani a haka kuma tana da daraja a wajena ko don kariyar da take bai wa iPhone dita.”
Uban ya kalli diyarsa cikin nuna so da kauna, ya ce, “Duk da haka idan na ce ki rufe jikinki wanda ya fi iPhone daraja, za ki amince.
Ta yi shiru…
Idan muka duba za mu ga cewa a wannan hikayar an nuna mana muhimmancin rufe tsiraici ga ‘ya mace, tun da har za a rufe tsiraicin waya to ina ga na ‘ya mace?
Ki sani cewa sanya tufafin da bai dace ba da bayyanar da surar jikinki yana rage miki kima da daraja a idon mutane.
Duk macen da ta mayar da tsaraicinta abin tallatawa a duniya, domin ta samu abin duniya, ta yi suna a duniya, ta mutu ta bar shi a duniya‚ ta daina alaƙanta kanta da sunan ’ya mace‚ domin wannan ba siffar mata na gari ba ne‚ muddin ta ci gaba da kiran kanta da ’ya mace‚ to ta tanadi abin da za ta faɗa wa Allah gobe ƙiyama‚ amma sam ta daina kiran kanta da sunan ‘ya mace ta san sunan da za ta kira kanta.
Sau da yawa za mu ga cewa illar da mace take samu a yayin yin Tiktok tana sa ta rasa mijin aure ma, domin kuwa su mazan da suke kallon ki a yayin da kike rawa cikin tsiraici ba za su taɓa auren ki ki zamo uwar ‘ya’yansu ba, ko da sun aure ki ɗin ma to auren babu inda yake zuwa ake rabuwa baram-baram cikin rashin arziki, ai ta tona wa juna asiri ana zagin juna da aibata juna, to don Allah me gari ya waya?
A kwanakin nan ma akwai ɗan Tiktok ɗin da ya fito ya yi magana a kan cewa ba zai iya auran yarinyarsa da suke yin comedy tare suna ɗorawa a Tiktok ba, duk da kasancewar yarinyar ta fito ta nuna tana son shi da aure, a cewarsa ba zai iya auren macen da take yin social media ba, ya fi son wadda ba ta social media saboda ko bayan ya aure ta asirinsa ya rufu, domin kuwa idan ya auri ‘yar social media ya sani aurensa zai zama a bankade tamkar babu hijabi, sai duniya ta dinga sanin sirrin gidansa, an yi ba sau ɗaya ba ba sau biyu ba ya gani, don haka ya shafa wa kansa ruwa ba zai iya ba.
Wannan wani babban darasi ne ga matan Tiktok, su gane cewa namiji ko dan iska ne to kamammiya yake so, haka nan shi idan ya yi ado yake zame masa, a yayin da mace idan ta samu tabo yake bibiyar ta har karshen numfashin ta.
Wannan kadan ne daga illolin Tiktok ga ‘ya mace mai raye-raye da bayyana tsiraici.