Ina son sanin muhimmancin sallar shafa’i da wutiri.
Sallar Shafa’i da Wuturi Sallah ce mai matuƙar daraja a cikin jerin Nafilolin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu.
Tana daga cikin sallolin da ake son duk rintsi musulmi ya kasance yana yin su, domin Malamai suna faɗin “Da ace mutum ya rasa sallar Shafa’i da Wuturi, da kuma raka’atanin Fajr, gwara ya rasa Duniya da abin da ke cikinta.”
Ya kuma zo a cikin Hadisi cewar “Watarana Sayyiduna Umar R.A ya makara har alfijir ya keto bai yi shafa’i da Wuturi ba, da gari ya waye sai ya fito waje ya yi shimfida, a nan Sahabbai suka riƙa zuwa yi masa jaje.”, wannan na ƙara nuna mana ɗimbin darajar da wannan nafila take da ita.
Na daga cikin falalar ta ne Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce “Ku yi wutiri ya ku ma’abota Alkur’ani, domin Allah wutiri ne (Guda ɗaya), kuma yana son wutiri”, wannan hadisi ya bayyana mana irin matsayin da masu yin sallar wutiri suke samu, domin yin ta na jawo soyayyar Ubangiji.
Sannan kuma akwai hadisin dake nuna “Wanda baya yin wutiri baya tare da mu”, don haka yana da kyau mu koyar da kanmu yin wannan sallah a kowace rana.
Lokacin Sallar Shafa’i da Wuturi yana farawa ne bayan sallar Isha’i zuwa ɓullowar alfijir, sannan adadinta na farawa ne daga raka’a uku, biyar, bakwai, har zuwa adadin yadda mutum zai iya. Kawai dai ya kasance akwai mara a karshe, sannan mutum ya riƙa yin yadda zai iya.
Sannan a na yin niyya ɗaya ne idan ya kasance raka’a uku mutum zai yi, idan kuma sun wuce uku, toh mutum zai yi ma shafa’i niyyarta, Wuturi ma zai yi mata niyyarta.
Allah ya bamu ikon riƙo da wannan salloli Amiiiiin.🙏