Wace al’ada ake yi in ciki ya yi wata bakwai ga mai haihuwa?
Al’adar Da Ake Yi Idan Ciki Ya kai Wata Bakwai Ga Mace Mai Haihuwa.
Idan ciki ya kai wata bakwai akwai wata al’ada da ake yi ga mai haihuwa, wannan al’ada kuwa ita ce zuwa goyon ciki gida. Kuma ita wannan al’adar a haihuwar fari kaɗai ake yin ta.
Da zarar cikin mace ya kai wata bakwai to za ta tattara daga gidan mijinta ta koma gidansu goyon ciki, saboda a nan ne za a lura da yadda take jin ciwo a yayin da cikinta ya tsufa, za a nuna mata hanyoyin da za ta bi domin jikinta ya yi lafiya, domin hatta yadda za ta shayar da jaririnta ma za a koya mata idan ta haihu. Sannan za ta samu hutu sosai ba za ta dinga aikace-aikacen da za ta jigata ba, idan a gidanta ne kuwa dole za ta yi aiki babu hutu.
Haka nan iyayenta za su tanadar mata abubuwan buƙata kamar su; ƙwaryar wanka wadda ake kira kwatanniya, zanin ɗaukar jariri, rigar jariri, kujerar wanka, garwar wanka, da kuma sabulun salo da sauran su.
Da zarar ta isa gidansu idan cikin ya kai wata bakwai, to za a fara ba ta sassaƙen mangoro ne ta fara sha saboda maganin basir ne. Idan ta shiga wata na takwas kuma za a fara ba ta wani magani mai suna kukuki, saboda yana ƙara wa jaririn cikinta ƙwarin jiki da lafiya. Idan ta shiga wata na tara sai a fara ba ta farin zoɓo tana sha saboda yana maganin zaƙi, sai kuma ganyen inibi da yake wanke hanyar fitowar jariri. Sai kuma hannu wanda yake kamar sheƙar tsuntsu yana maganin naƙuda da ciwon cikin maijego. To idan aka bi waɗannan hanyoyi mace za ta haihu lafiya ta samu jariri mai cike da lafiya in sha Allah.
Haka nan bayan ta haihun za a dinga gasa mata nama da toka tana ci saboda ɗanɗanon bakinta ya dawo daidai. Za a dinga ba ta zuma da yaji wanda za ta dinga sha a tsaye saboda ta wanko mata mahaifarta. Sannan a cimarta ma sai an samu sauyi, za a dinga ba ta cima mai kyau ne kamar kunun kanwa wanda zai saukar mata da ruwan nono, da kuma tuwon dawa wanda zai ƙara mata ƙarfin jiki tun da za ta ci ta ƙoshi, har shi ma jariri ya samu wadataccen ruwan nonon da zai sha ya ƙoshi.
Ba iya nan lamarin ya tsaya ba, akwai wankan jego da za a yi wa maijego, wanda za ta ji daɗin jikinta sosai saboda wannan wankan. Ana samo wata ciyawa mai suna dandana a saka a garwar wanka, wannan ciyawa ta haɗa abubuwa da yawa kamar; nannaɗaɗɗen ɓawon kalgo, duman rafi, sassaƙen aduwa, sassaƙen mangwaro, sai a tafasa ruwa a yi wa maijego wanka da ganyen dalbejiya.
To cikin ikon Allah idan aka gudanar da wannan al’ada ana haifar ɗa mai ido, domin kuwa maijego da jaririnta za su samu ingantacciyar lafiya, kuma ta koma gidan mijinta bayan arba’in cike da ƙoshin lafiya.
Wannan ita ce al’adar da ake gudanarwa ga mace mai ciki idan ya kai wata bakwai.