Wace Addu’a Ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam Yakoyar Yayin Tashin Mutum Daga Baccin Sa?
-
Akwai addu’o’i da Annabi (S.A.W) Ya koyar da mu a yayin tashi daga barci. Wasu daga ciki ma yana karantawa a yayin da ya tashi daga barci. Ga kaɗan daga ciki:
1- الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُورُ.
Alhamdu lillahil-lathee ahyana ba’ada ma amatana wa-ilayhin-nushoor.
“Dukkan Godiya Ta Tabbata Ga Allah Wanda Ya Raya Mu Bayan Mutuwarmu, Kuma Izuwa Gare shi Tashi Yake.
2- لا إله إلا الله وحده لا شريك له، له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير، سبحان الله، والحمد لله، ولا إله إلا الله والله أكبر، ولا حول ولا قوة الا بالله العلي العظيم، رب اغفر لي
La ilaha ilallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wa huwa ala kulli shai’in qadeer. Subhanallahi, walhamdu lillahi, wa la ilaha illallahu wallahu akbar, wa la haula wa la quwwata illa billahil aliyyul azeem. Rabbi Igfir ly.
“Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, mulki da godiya duka nasa ne, kuma Shi mai iko ne a kan dukkan komai, tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah Shi kadai, Allah Shi ne mafi girma, kuma babu tsumi babu dabara sai dai zuwa ga Allah madaukaki mai mai girma, ya Allah ka gafarta min.”
3- الحمد لله الذي عافاني في جسدي، ورد علي روحي، وأذن لي بذكره
Alhamdu Lillahil lazy aafaani fi jasady, wa radda alayya ruhy, wa azin ly bi zikirihi.
“Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya ba ni lafiya a cikin jikina, kuma Ya dawo mini da raina bayan mutuwar ran nawa, kuma Ya umarce ni da ambaton sa.”
Waɗannan addu’o’i guda uku suna daga cikin manya-manyan addu’o’i waɗanda ake karanta su yayin tashi daga barci. Domin yabo da kirari da jinjina da kuma godiya ga Allah (S.W.A.) Allah Ya sa mu dace.