Waɗanne irin hanyoyi ake bi don kama zukatan masu sauraro a yayin wa’azi?
Da farko dai WA’AZI shi ne yin kira a kan tafarkin Muslunci, wanda ya ƙunshi umurni ko kuma hani. Sannan wa’azi na tafiya ne a kan Jigo guda biyu, wanda bayan su, babu wani jigo.
1. Jigo na farko shi ne Umurni da kyakkyawa.
2. Na biyu kuma shi ne hani da Mummunan aiki.
Shi ya sa Allah ya aiko Manzanninsa domin su zama masu bushara da gargarɗi. Ma’ana masu umurni da a bauta ma Allah shi kaɗai, tare da umurnin wasu nau’aukan Ibadu, a cikin wannan umurnin ne kuma ake yin kyakkyawar bushara ta wannan aikin, kamar yadda Allah ya yi ta yi ma muminai bushara da gidan Aljanna, idan har sun kyautata aikinsu.
Sannan har ila yau a cikin wannan hanin ne ake gargaɗar mutane, tare da tsoratar da su da mummunan sakamako, don haka a taƙaice, wa’azi na nufin umurni da kuma hani.
WAYE YA KAMATA YA ZAMO MAI YIN WA’AZI?
Mutanen da ya kamata su yi wa’azi, su ne masu Ilimi, shi ya sa Allah ya fifita Annabawa da Manzanninsa da ilimi, domin da shi ne ake fahimtar me Allah yake so, menene baya so.
A cikin Suratu Yusufa A.S, Allah Maɗaukakin Sarki ya ce “Ka ce ‘wannan hanyata ce; ina kira zuwa ga Allah a kan Basira, ni da waɗanda suka bi ni, ni kuma ban zama daga masu yin shirka ba.”
Wannan ayar mai girma ta bamu cikakkiyar siffar wanda ya kamata ya yi wa’azi. Ta nuna mana mai wa’azi mutum ne mai Basira (Wato ilimi).
Sannan mai wa’azi dole ne ya siffantu da siffar da yake son yi ma mutane wa’azi da ita. Misalin dai waccan Ayar, inda ya ce “Ni ban kasance daga masu yin shirka ba.”, A nan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana kira ne da a bauta ma Allah shi kaɗai, don haka siffar farko da yake da ita ita ce tsarkake Ubangiji, baya shirka, shi yasa kai tsaye yake kira da kada a yi shirka.
Don haka in dai mutum zai yi wa’azi, toh ya zama mutumin kirki gwargwadon iyawarsa, da haka ne zai ɗauki hankalin mutane har su karɓi abin da yake so ya wa’azantar da su.
Ba zai yiwu mutum na shan giya, ko zina ko sata ba, kuma ya zo yana yi ma mutane wa’azi a kan su guji waɗannan munanan ayyukan ba, duk da gaskiya ce ya faɗa, amma kasantuwar yana aikata laifin, wani ba zai saurare sa ba, asali ma mutane zasu ga kamar ya raina musu hankali, don haka duk wanda zai yi wa’azi, yake wajibi a kansa ya kyautata aikinsa.
Allah maɗaukakin Sarki ya gargaɗi Muminai a littafinsa ta hanyar faɗin “Ya ku waɗanda suka Imani, saboda me kuke faɗin abin da baku aikatawa? Ya girma ga zama abin ƙyama a wurin Allah, ku faɗi abinda baku aikatawa.”
Don haka idan har zaka yi ma mutane wa’azi a kan su yi sadaka, toh kaima a ga kana yin sadakar, ba don riya ba, sai don mutanen da kake yi ma wa’azi su yi koyi da kai.
SALON YIN WA’AZI
Wa’azi tafe yake da salonsa, domin da shi ne ake jan ra’ayin mutane, sannan ko wane salo yana aiki ne a kan irin mutanen da aka taras kuma ake son yi masu wa’azi.
Misali, an samu waɗanda ba musulmai ba, kuma ana son kiran su zuwa ga Musulunci, toh waɗannan salon da za a yi masu wa’azi daban ne da waɗanda su suna cikin musuluncin.
Su waɗanda ba Musulmai ba za a yi masu gargaɗi ne cike da tausasawa, tare da kwaɗaitar da su musuluncin da kuma irin Alkhairin da ke cikin kasancewa musulmi.
Duk da wasu sai da aka yaƙe su, wasu kuma da kyauta aka ci galabarsu har suka zama musulmai. Kawai dai ya danganta da wa ake son yi ma wa’azin, don wani bai bukatar a kira shi a ce ya zama musulmi, kyakkyawar mu’amalar da aka nuna masa kaɗai ta isa ta sa ya zama musulmi, shi ya sa ake son mai wa’azi ya zama mutumin kirki.
Sannan tausasawa, ko kuma yin amfani da lafuzza waɗanda babu cin fuska, zagi ko aibatawa a cikinsu.
Allah Maɗaukakin Sarki ya ce ma Annabi Musa da Ɗan uwansa Harun “Ku faɗa ma Fir’auna magana mai taushi, wataƙila ya tuna, ko kuma ma ya ji tsoron Allah.”
Ku duba girman kafircin Fir’auna, amma Allah ya ce a faɗa masa magana mai taushi, ma’ana a bashi girman da ya ke jin yana da shi, ta haka ne zai ji an girmama shi, idan an yi sa a sai ya tuba.
Kuma tunda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama yake yin wa’azi, ba a taɓa jin ya kama sunan wani ba, sai dai ya ce “Ɗayanku”, da mutum ya ji sauran zancen zai gane da shi ake.
Don haka wa’azi na bukatar azanci da ingantaccen salon sarrafa harshe.
Sannan yana da kyau mai wa’azi ya kalli zamanin da yake ciki, sai ya riƙa yin wa’azi da irin abinda mutanen zamanin suka fi karkata a ciki, kamar yanzu da muka ritso zamanin social media, da yawan Malamanmu sun koma kamar comedians, toh wannan salo ne mai zaman kansa na isar da saƙo, idan basu bi wannan salon ba, ba kowa ne ma zai san da zamansu ba.
Duk ba a so mai wa’azi ya zama mai yawan wasa, toh amma kuma kada ya yi tsauri da yawa.
Allah shi ne masani.