Ya ake yin Alwala? Sannan waɗanne abubuwa ne suke ɓata alwala?
YADDA AKE YIN ALWALA.
Sallah ba ta yiwuwa sai da alwala, kuma tilas alwalar ta zamanto an yi ta da ruwa mai tsarki wanda shi ne ruwan da bai canja daga asalin kamanninsa na ruwa ba,kamar ruwan kogi ko na rijiya ko na idaniyar ruwa ko na korama.
A KULA DA KYAU: Komai kankantar najasa takan lalata ruwan da yake dan kadan,amma idan yana da yawa to najasa ba ta lalata shi har sai idan ta canja masa kala ko dandano ko kuma kamshi.
1. Ana fara alwala da sunan Allah (Bisimillah) kuma an so a fara da wanke tafukan hannu a kuma tabbatar sun fita,za ayi hakan sau uku,musamman ga wanda ya farka daga barci.
A KULA DA KYAU:Ba a son a wanke wata gaba sama da sau uku wannan makaruhi ne.
2. Sannan sai kuskurar baki,tilas ne a yi kuskura na farko, amma idan aka yi sau uku to shi ya fi soyuwa kuma ya fi falala.
A KULA DA KYAU: Zuba ruwa a baki kadai ba ya wadatarwa, dole ne sai an kurkura shi a cikin bakin. Kuma an so mutum ya yi asuwaki yayin kuskure bakin.
3. Sannan sai shaka ruwa a hanci,tilas ne a yi sau daya a kalla, amma idan an yi sau uku shi ya fi falala.
A KULA DA KYAU: Ita ma shakar hanci ba wai kawai za a shigar da ruwa hanci ba ne, dole ne ya zamo ta hanyar shakar ruwa tare da numfashi, kuma ya shigar har cikin hancin sannan ya fyato shi ya fito tare da numfashi.
4. Sannan sai wanke fuska, ita ma tilas ne a yi sau daya a kalla, amma idan anyi sau 3 shi ya fi. Za a wanke ta ne tun daga kunnen dama zuwa na hagu, wannan a kwance kenan, a tsaye kuma tun daga karshen haba har yazuwa mabubbugar gashin kai.
A KULA DA KYAU: Idan gemun mutum yana da yawa to an so ya tsefe shi, amma idan ba shi da yawa to tilas ne ya tsefe shi ta yadda ruwa zai ratsa shi.
5. Sannan sai wanke hannaye tun daga ‘yan yatsu har zuwa guiwar hannu, tilas a yi na farko amma idan an kara zuwa sau uku wannan shi ya fi.
A KULA DA KYAU: Ana so a fara da hannun dama kafin na hagu, da kuma cuccuda su.
6. Sannan sai shafar kai baki dayansa, mutum zai shigar da yan yatsunsa guda biyu manuniya (sabbaba) cikin kofofin kunnuwansa, sannan ya shafi fatun kunnuwansa da manyan yan yatsun nasa (ibham)
A KULA DA KYAU: Inda ya wajaba a shafa a kai shi ne; daga mafarin fuska zuwa kewayowa da juyo da shi daga keya zuwa mafarin fuska. Kuma idan gashi yana da yawa ba lallai ne sai an shafi wanda ya sauko ba.Idan kuma babu gashin kwata-kwata to sai a shafi fatar kai kuma tilas ne a shafi fatun kunnuwa.
7. Sannan sai mutum ya wanke kafafuwansa shi ma sau daya ne ya wajaba, amma idan aka yi sau uku ya fi falala.
An so mutum idan ya kammala alwalarsa ya ce: “ASH-HADU AN LA’ILAHA ILLALLAHU WA ANNA MUHAMMADAN ABDUHU WA RASULUHU.”
ABUBUWAN DA KE BATA ALWALA.
Abubuwan da suke bata alwala sun kasu kashi biyu; Hadasi da Sababinsa. Abin nufi a nan shi ne, akwai abin da shi karan kansa yake bata alwala to wannan shi ake kira Hadasi. Akwai kuma wanda shi karan kansa ba ya warware alwala amma zai kai ka ga abin da yake warware alwalar, to wannan shi ake kira, Sabuban Hadasi**.** To shi hadasin wato abin da yake karya alwala da karan kansa, abubuwa ne guda shida, hudu daga cikinsu suna fita ne ta gaba, su ne; fitsari, maziyyi, wadiyyi da kuma maniyyi. Wadannan idan suka faru ko dayansu ya faru to tsarki kawai za a yi a sake alwala in ban da maniyyi, Wanda shi maniyyi bayan ya bata alwala sai kuma an yi wanka. Sai kuma guda biyu da suke fita daga dubura, su ne; Bayan-gida da kuma tusa. Amma shi bayan-gida tsarki za a yi sai a sake alwala, sabanin tusa wacce take ita ba a yi mata tsarki alwala kawai za a sake. Sai kuma abubuwan da suke sabuba ne na hadasin wadanda yake suna da wasu bayanai, amma su wadancan da zarar ya diga komai kankantarsa to ya karya alwala in ban da mai fama da cutar yoyon-fitsari, wadannan abubuwa sune;
Barci: Shi barci a nan ya kasu kashi hudu;
(a) Dogon barci mai nauyi, kai tsaye wannan ya karya alwala.
(b) Takaitaccan barci mai nauyi, shi ma ya karya alwala.
(c) Takaitaccan bacci mara nauyi to shi bai karya alwala ba.
(e) Dogon bacci mara nauyi, bai karya alwala amma an so a sake ta.
Ma’aunin da ake auna barci da shi domin a gane yana da nauyi ko ba shi da nauyi shi ne; idan ka san wanda ya zo da wanda ya tashi to barcinka bai yi nauyi ba, amma idan ba ka san wanda ya zo ba ko wanda ya tashi ba to barcin ya yi nauyi.
Gushewar Hankali: Idan hankalin mutum ya gushe ta hanyar hauka ko farfadiya ko suma ko maye to mu sani alwalarsa ta karye. Kenan idan mutum ya yi alwala sai ya hau iska ko kuma suka yi hadari kawai sai ganinsa ya yi a asbiti ko kuma ya sha ta yi Marisa ta sha kafso to alwalar kowannen su ta karye.
Shafar Azzakari: Idan mutum ya shafi al’aurarsa kai tsaye tafin hannunsa ya taba al’aurarsa ba wai ta saman riga ko wando ba ko kuma wani kyalle ba to malamai sun kara wa juna sani kan makomar al’walarsa, wadansu suka ce kawai alwalarsa ta karye, wasu kuma suka ce idan ya taba ne domin ya ji dadi to ta karye amma idan ba wai ya yi hakan ne domin ya ji dadi ba alwalarsa tana nan, wannan maganar kuwa tana da karfi. Amma dukkanin malamai sun yi ittifaki kan cewa idan ya taba al’aurarsa ba kai tsaye ba ko dai ta saman wando ko saman riga ko saman wani kyalle to alwalarsa tana nan daram.
Shafar Mace/Namiji: Idan namiji ya shafi mace domin ya ji dadi to ko ya ji dadin ko bai ji ba alwalarsa ta karye, haka kuma al’amarin yake idan mace ta taba namiji domin ta ji dadi to ta ji dadin ko bata ji ba alwalarta ta karye, malamai sun kasa shafar zuwa gida hudu;
(a) Idan ya taba domin ya ji dadi kuma ya ji dadin to alwalar ta karye.(b) Idan ya taba ba don ya ji dadi ba sai kuma ya ji dadin to ta karye.(c) Idan ya taba domin ya ji dadi sai bai ji dadin ba to alwalar ta karye.
(d) Idan ya taba ba domin ya ji dadi ba kuma bai ji dadin ba to alwalarsa tana nan daram.
Wadannan bayanai haka mai Ashmawi ya kawo su.
Akwai wadansu da malamai suka kara wa juna sani a kan suna karya alwala ko ba sa karyawa? Wadannan kuma su ne:
Shakka A kan Hadasi: Idan mutum ya tabbatar da alwalarsa sai kuma yake kokonto ya yi hadasi ko bai yi ba? Kenan ba shi da tabbas? Wasu malamai suka ce: Ai da ya yi kokwanto alwalarsa ta karye domin ba a sallah da wani abu na shakku. Wasu malaman kuma suka ce: Idan ya tabbatar da yana da alwala sai daga baya ne yake shakka to ai shakka ba ta ture abin da yake dahir, saboda haka suka ce alwalar tana nan, Allah shi ne masani.
Ridda: Shi ne mutum musulmi ya kafirta (Allah Ya tsare mu). Wadansu malamai suka ce da zarar ya bar musulunci to alwalar ta karye, wasu malaman kuma suka ce; a’a, ai ayyukansa da ya yi ba za su baci ba sai in ya mutu bai dawo musulunci ba, wadda alwala na cikin wadannan ayyukan. Mafi kyawu ga wadannan abubuwa mutum ya sake alwalar shi ya fi. Alwala ba ta baci idan mutum ya yanke farce (Kumba), ko ya taba marenansa ko duburarsa ko an yi masa kaho ko ya yi dariya ko amai ko kuma tuntube har jini ya fita duk alwala ba taba ci saboda wadannan, ko mace ta shafi gabanta amma idan ta sa yatsa a ciki to wasu sun ce alwalar ta karye. Idan mutum yana jin fitsari ko tusa ko bayan gida abin da musulunci ya karantar shi ne mutum ya je ya biya wannan bukatar tasa tukunna, maimakon ya matse. Alwala tana da muhimmanci matuka saboda haka a kiyaye ta a san kuma abin da yake warware ta, kuma wannan yake nuna mana cewa tun da har alwala za a ce akwai abubuwan da suke warware ta duk da ga laima a jikin mutum amma a ce alwalarsa ta warware to lallai yana da kyau mu san abubuwan da suke warware ta din.
Allah Ya sa mu dace. Amin.