Cutar Olsa, maganin gargajiya ko na asibiti, wanne ya fi?
Maganin Gargajiya da Maganin asibiti dukkansu abin yarda ne a wurin neman lafiya, madamar an yi amfani da su yadda ya kamata, toh amma kuma dole a samu wanda ya fi amfani a cikinsu a kan nau’aukan cutuka.
Misali: Akwai cutukan da maganin asibiti ne ya fi dacewa da su, kamar cutar cancer, diabetes da sauransu, sannan akwai cutukan da maganin gargajiya ne ya fi dacewa da su, kamar ciwon iska d.s.
Toh haka a wurin ciwon olsa, ita kowane magani aka haɗa mata yana warkar da ita, ko kuma ya sanya ta yi sauƙi, a magungunan gargajiya a kan haɗa garin bagaruwa da madara ana damawa ana sha, wannan yana maganin olsa, sannan a kan daka gero da ganyen aduwa a riƙa sha da madara ko nono, shi ma yana maganin olsa. Sai dai babbar illar ta ce, ya yakama mutum ya sha wannan magani na gargajiya? Nan ake samun matsala, don masu bada shi ba sa ƙayyade adadin yadda za a sha, toh a nan ne ake samun matsala, ƙarshe daga neman lafiya kuma a samo cuta.
Maganin asibiti irinsu Gestid, magnesium, Gaviscon da sauransu kuwa likita ne zai rubuta ma marar lafiya su, tare da ƙa’idar yadda zai sha su, sannan an yi ittifaƙin waɗannan magunguna suna warkarwa, ko kuma kwantar da cutar olsa, sannan basu cika illa ba in dai an yi amfani da su yadda ya dace.
A don haka ne ma nake ganin maganin asibiti ya fi warkar da cutar olsa fiye da maganin gargajiya, in dai an yi amfani da shi yadda ya dace, sannan ra’ayina baya nuna gazawar maganin gargajiya a wurin cutar olsa, shi ma yana magani sosai, toh amma dai ni na fi gamsuwa da maganin asibiti. Sai mu yi fatan Allah ya bamu lafiya Amiiiin.