A lokacin da mutum ke yin wanki, shin kumfa ne ke fitar da datti ko kuma sabulu ko omon da ake wankin da shi?
Alaƙar da ke tsakanin Sabulu da kumfa, kamar alaƙar da ke tsakanin Ruhi da gangar jiki ne, ɗaya baya da wani tasiri ko amfani idan babu ɗayan. Sai dai duk da haka, akwai wanda ya fi bada gudunmawa mai ƙarfi a cikin tafiyar. Sai dai kafin nan bari mu ga matsayin kowanne:
Sabulu: Shi ne uban tafiyar, wanda idan babu shi wankin ba zai yiwu ba.
Kumfa: shi ne mataimaki wurin tafiyar, wanda shi kuma idan babu shi wankin ba zai kasance yadda ya kamata ba.
Don haka a nawa ra’ayin, Sabulu shi ne ke fidda datti yayin da ake gudanar da wanki, domin shi ne ke ɗauke da chemicals ɗin da ke fitar da datti, sannan shi ne jigon wankin, wanda idan babu shi wankin ma ba zai yiwu ba, domin ba a wanki da ruwa zalla. Kumfa kuma mataimaki ne na musamman ga sabulu, domin yana sanya kaya su yi daɗin wanki kuma su fita tas.
Na san wasu zasu ce Omo fa? Shi kumfa ne ai ba Sabulu ba, kuma ana wanki da shi har kaya su fita.
Tabbas Hakane, shi ɗin kumfa ne, amma ba kuma kumfa irin na sabulu ba, shi kumfansa ɗauke yake da chemicals ɗin da sun fi na kumfan sabulu ƙarfi, sannan su kansu chemicals ɗin ma ba za a rasa bambanci a tsakanin na sabulu da na omo ba. Tunda idan da zaka damtse omo a hannunka, zaka ji shi da zafi, sabulu kuwa ba ta yadda zaka ji zafi don ka taɓa shi.
Don haka idan na koma batun tsakanin kumfa da sabulu wane ya ke fidda datti? Toh sabulu ne ke fidda datti, shi kumfa babban mataimakinsa ne.
Amma fa wannan ra’ayina ne na faɗa, na san ba lallai ne ya zama haka ba, ko kuma ba lallai a gamsu da shi ba. Ko ma dai mene ne, sabulu ne ke fidda datti ba kumfa ba!
Da kyau, sannu da ƙoƙari.