Ta yaya mutane za su iya gwada ingancin tsaftan ruwan sha a cikin gidan su? Sannan mai ne ne mahimmancin shan lafiyayyen ruwa mai tsafta?
Ruwa mai inganci yana nufin ruwa wanda ya cika ka’idoji na lafiya da tsafta, wanda zai iya zama lafiya ga jikin mutum.
Mutane za su iya gwada ingancin tsaftan ruwan sha a cikin gidansu ta hanyoyi da dama, kamar haka:
1. DUBAN LAUNIN RUWAN: Idan ruwa yana da launi ko kuma yana da wani abu mai launi, wannan na iya nuna cewa akwai gurbatacce a cikin ruwan.
2. DUBA ƘAMSHIN RUWAN: Idan ruwa yana da wari mai kyau ko kuma wari mai tsanani, wannan na iya zama alamar gurbatawa.
3. GWAJIN pH: Ana iya amfani da na’urorin gwaji na pH don tantance ko ruwan yana da acidic ko alkaline. Ruwan sha mai kyau yawanci yana da pH tsakanin 6.5 zuwa 8.5.
4. GWAJIN KWAYOYIN CUTUTTUKAN: Akwai kayan gwaji da za a iya amfani da su don tantance kwayoyin cuta kamar E. coli da sauran kwayoyin cuta a cikin ruwa.
5. TUNTUBI MASANA: Hakanan, zaka iya tuntubar masana ko hukumomi don gudanar da gwaje-gwaje na ingancin ruwa.
Mahimmancin shan lafiyayyen ruwa mai tsafta yana da yawa, ciki har da:
– KARE LAFIYA: Shan ruwa mai tsafta yana rage hadarin kamuwa da cututtuka da sauran matsalolin lafiya.
– INGANTA AIKI: Ruwan da ya dace yana taimakawa wajen inganta aikin jiki da kwakwalwa.
– KARE JIKI: Ruwan mai tsafta yana taimakawa wajen tsarkake jiki daga gurbataccen abinci da sinadarai.
Saboda haka, yana da matukar muhimmanci a tabbatar da cewa ruwan da ake sha yana da inganci da tsafta.
Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Allah mai tsarki ne kuma yana son tsarkakka, mai tsafta ne shi kuma yana son mai tsafta[1]. Haka nan yana cewa: Tir da kazamin bawa[2].
Shin mece ce tsafta?
Tsafta ita ce; tsarkaka daga dauda, wani lokaci dauda tana kasancewa a jiki, a tufafi, a gida, a hanya kamar titi, a magudanar ruwa, a iska, a ruwa, da sauransu. Wadannan abubuwa ne da Allah da manzon (s.a.w) suka yi gargadin nisantar kazanta su, domin Allah yana da tsarki kuma yana son bayinsa masu tsarki (tsafta). Idan mun duba zamu ga addini kansa asasinsa ya ginu ne kan tsafta, manzon rahama yana cewa: An gina musulunci kan tsafta, kuma ba mai shiga aljanna sai mai tsafta[3]. Da fadinsa (s.a.w): Allah yana son mai ibada mai tsafta[4]. Da fadinsa (s.a.w): Wanda ya riki wani tufafi to ya tsaftace shi[5].
Hadisai ne masu yawa suka zo suna masu bayani kan tsafta da muhimmancin ta, kuma sun yi nuni da kyamar da Allah (s.w.t) ya ke yi wa mai rashin kula da tsafta. Idan kuwa Allah ya kyamaci mutum ko wata al’umma to fushinsa ke nan yana fada wa wannan mutumin ko wannan al’ummar, don haka babu yadda lamarinta zai gyaru.
Mene ne ruwa?
Ruwa shi ne yalwataccen sinadari mafi muhimmanci a rayuwa, a don haka yake da amfani daban-daban. Kuma shi ne sinadarin da aka halicci kowanne abu da shi.
Allah Madaukakin Sarki yana cewa :
بسم الله الرحمن الرحيم
ﻭَﺟَﻌَﻠْﻨَﺎ ﻣِﻦَ ﺍﻟْﻤَﺎﺀ ﻛُﻞَّ ﺷَﻲْﺀٍ ﺣَﻲٍّ ﺃَﻓَﻼ ﻳُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ
(ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻷﻧﺒﻴﺎﺀ 30)
Ma’ana
“Kuma daga ruwa muka sanya kowane abu ya rayu, shin ba za su yarda ba ne?”
(Aya ta 30, suratul Anbiya’i).
Wannan ayah tana nuna mana cewa asalin kowane abu daga ruwa ne Allah Ya halicce shi.
A gaskiya kamata ya yi a ce ruwa shi ne mafi soyuwa cikin abubuwan da ake sha, saboda a yayin da dan adam ka iya kwashe sati uku ba tare da cin abinci ba, to ba zai iya kwashe kwana uku ba tare da shan ruwa ba.
Da akwai bukatar adadin yawan ruwa da ake so kowanne mutum ya sha a rana. Masana sun gudanar da bincike da dama da ya nuna cewar, kwakwalwar mutum na da bukatar adadin yawan ruwa a rana don samun gudanar da aiki yadda ya kamata.
A cewar wani babban likita Dr. Robert A. Huggins, na asibitin koyarwa a jami’ar Connecticut, ta kasar Amurka, ya ce.
“Kwakwalwar mutum na bukatar akalla yawan ruwa da ya kai “8*8” wanda yayi dai-dai da yawan ledar fiyowata 5 a rana.”
Ya kara da cewa, “Kwakwalwar mutum na da nauyin kashi 3.5% na nauyin mutum, amma ita ke cin fiye da kashi 20% na duk wani abu da mutum yake ci.”
Hakan na nuna cewar kwakwalwa tafi kaso mai yawa da sauran sassan jikin mutum.
Hakan ya sa tana bukatar ruwa mai tsafta da yawa don gudanar da aiki yadda ya kamata a cikin lokaci.
To sai dai duk da wannan muhimmanci da ruwa yake da shi a jikin dan adam, akan samu waɗanda ba sa kula da tsaftarsa, wanda kuma hakan yakan janyo kalubale mai yawa ga lafiyar mutum.
Ta yaya mutane za su iya gwada ingancin tsaftace ruwan sha a gidajensu?
Tsaftar ruwa shi ne kashin bayan tafiyar tsafta a cikin al’umma, al’ummar da ta rasa tsaftacaccen ruwa tana cikin karancin lafiya da miyagun cututtukan da za su mamaye ta da addaba. Al’ummar da ta zama haka za ta kasance al’umma ce da babu wani magani da zai amfanar da ita domin ta rasa asasin farko na samun lafiya. Musulunci ya yi hani mai tsanani kan lalata ruwan shan mutane da gurbata shi, don haka ne zamu ga ya haramta yin bayan gida a wurin da yake matattarar shan ruwan al’umma sakamakon hadarin da yake cikin yin hakan na cutar da al’umma da haifar mata da kwalara. Lamarin ya sanya duniya ta tayar da jijiyar wuya kan maganar ruwa mai tsafta ga dan adam. Ana samun yawaitar rashin lafiya da cututtuka a gidaje sakamakon rashin tsaftace ruwan sha. Rashin tsaftace ruwan sha yana taka muhimmiyar rawa wajen yada kwayoyin cutar Typhoid. Ruwa yakan gurbata da kwayoyin cutar saboda rashin tsaftace ce, idan ya gurbata kuma za a iya kamuwa da cutar, don haka ya zamana dole mu kiyaye da tsaftace ruwan shanmu domin guje wa cutar. Saboda masana sun ce muhimmiyar hanyar daukar cutar Typhoid ruwan da ne.
Samar da ruwan sha mai tsafta a gidajenmu babban abu ne, za a iya samar da shi ta hanyar kulawa da shi, da tafasa shi domin kashe kwayoyin cutar da ke ciki. Da kawwame shi a wuri guda cikin rufaffen mazubi saboda kada kwayoyin cuta su shiga ciki.