Ayi mana ƙarin haske game da wannan:Ta wace hanya yarinya ko saurayi suke sanar da iyayen su wanda suke so da aure?
Hanyoyin da mace ko namiji zasu faɗa ma mahaifansu sun samu wanda zasu aura suna da yawa. Sannan ya danganta da yadda kowa zaɓi hanyar bayyanarwa. Ta bangaren namiji, yana da hanyoyin bayyana ma mahaifansa ya samu matar aure masu yawa, kaɗan daga cikin hanyoyin akwai:
Akwai yawan magana: wani da zaran ya samu matar da yake so ya aura, toh zai riƙa yawan maganarta a cikin gidansu, da wurin abokansa, ba tare da ya sani ba zai riƙa bayyana musu irin son da yake mata da kuma manufarsa akan ta, su kuma ta haka ne zasu gane da aure yake son wannan macen da yake maganarta.
Hanya ta biyu: ita ce da zaran ya samu karɓuwa a wurin macen, da kuma iyayenta, toh zai zo wurin mahaifansa ko kuma waliyyansa ya sanar da su ya samu mata, don haka su je su nema mashi aurenta.
Hanyar sanar ma waliyyan yawa gare su, wani yana jin nauyin mahaifansa, ko kuma a tsarin gidansu ba a tunkarar mahaifa da maganar kai tsaye, sai dai a samu ƴan uwan mahaifan a faɗa masu, kamar ƙane ko wan Uba, su kuma sai su je su nemar mashi auren.
Mace kuma saboda kunya sai dai a gane da ta samu mijin aure, don wata ko ƙawayenta ba ta iya faɗa mawa ba, sai dai su ji, batun sanar da mahaifa kuwa, mijin da zata aura ne idan ya shirya, toh zai nemi ta faɗa musu yana son a ba shi dama, domin wuƙa da naman neman auren na hannunshi, don kuwa duk yadda mace ta so ga yin aure, don ta samu mai son ta ba zata ce ta samu miji ba a zo a yi aure, har sai idan shi ya buƙaci haka.
Waɗannan su ne kaɗan daga cikin hanyoyin da mace ko namiji suke bayyana ma mahaifansu sun samu wanda zasu aura, sai mu ce Allah ya haɗa kowa da zaɓinsa na gari Ami
iiiin.
Amin ya rabb! Sannu da ƙoƙarin.