Akan ce wai asalin bil’adama ya samu daga birai ne. Shin ina gaskiyar wannan magana take?
Tabbas biri ya yi kama da mutum, tun daga kaɗan na wasu siffofinsu da kuma kaɗan daga wasu ɗabi’insu. Sai dai hakan ba shi ne ke nuna mutum ya samo asali daga biri ba, ko kuma a ce biri ya samo asali daga mutum ba, duk da Al-qur’ani mai girma ya zo mana da labarin wasu mutane da ake kira As’habu Ssabt, da aka yi su a zamanin Annabi Dawuda A.S, waɗannan mutane sun yi ma Allah laifi, inda Shi kuma ya hukuta su ta hanyar mayar da su birrai.
Sai dai a yadda tarihi ya nuna, su waɗannan mutanen da aka maida birrai, ba su ne na farko ba a halittar biri, kafin su, da ma can akwai birrai a doron duniya, kawai Allah ya zaɓi ya maida su birrai ne, domin tsananta hukunci a kansu, bisa ga bijire ma dokarsa ta hana su kamun kifi da ya yi a ranar Asabar. Sannan da aka maida su birran, tarihi ya nuna ɗimuwa ta same su, har ta kai ga basa iya gane yan’uwansu da aka hukunta su a tare, sai suka riƙa zuwa wurin birran asali suna shinshina su suna kuka, yayin da birran na asali suka riƙa faɗa musu ba fa su ne ƴan’uwansu da suka saɓa ma Allah a tare ba, don haka su rabu da su.
Sannan har ila yau, su waɗannan mutane da ka azabtar da su ta hanyar mayar da su birrai, gabaɗanysu sun mutu ne bayan kwana uku, sannan aka aiko ruwa da iska suka watsa su a kogi. Kun ga hakan na nufin su basu yi dogon zangon da za a samu wata zuri’a ta birrai a tare da su ba, don haka biri asalinsa biri ne, kamar yadda Mutum ya samo asali ne daga Annabi Adamu, kamar yadda tarihin Musulunci ya nuna.
Allah ne mafi sani.
Dakyau. Sannu da ƙoƙari.