Mutane nawa ya hallatta su ciyar idan basa iya yin Azumi?
Azumi babbar ibada ce da Ubangiji Ya wajabta wa bayinsa. Bukhari ya rawaito hadisi daga Abu Huraira ya ce, “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, Allah Ya ce, “Duk wani aikin ɗan’adam nasa ne, ban da azumi, domin shi nawa ne, kuma Ni nake sakawa a kansa. Kuma azumi garkuwa ne, idan ranar azumin ɗayanku ta kasance, kada ya yi batsa, kada ya yi hayaniya, idan wani ya zarge shi ko ya neme shi da faɗa, to ya ce; ni ina azumi. Na rantse da wanda ran Muhammadu ke hannunsa, haƙiƙa rihin bakin mai azumi ya fi ƙamshi a wajen Allah fiye da ƙamshin almiski. Mai azumi yana da farinciki biyu da yake yin su, idan ya yi buɗa baki zai yi farinciki da shan ruwansa, idan kuma ya gamu da UbangijinSa zai yi farinciki da azuminsa.”
Don haka azumi wajibi ne a kan kowane Musulmi, baligi, mai hankali mai iko, mazaunin gida, namiji ne ko macen da ba ta jinin haila ko na biƙi (a lokacin) azumin. Ba ya wajaba a kan kafiri, amma da zarar ya musulunta a tsakiyar rana to ya kame bakinsa a ragowar yininsa, amma ba zai rama wannan ranar ba.
Akwai nau’in mutane waɗanda azumi bai wajaba a kansu ba, su ne kamar haka:
Azumi ba ya wajaba a kan yaron da bai balaga ba, sai dai idan azumin ba ya ba shi wahala za a iya umartar dhi da ya yi don ya saba.
Azumi ba ya wajaba a kan wanda ba shi da hankali, kamar mahaukaci, ko wawa, ko makamantansu, ko babba wanda yake sambatu.
Azumi ba ya wajaba a kan wanda ya kasa, kamar mai shekaru da yawa wato tsoho tukuf.
Akwai waɗanda azumi yake wajaba a kansu, sai wata lalura ta sa su sha azumin, to za su rama ne. Misali kamar,
Mara lafiya da ake sa ran warkewarsa, idan ya warke ya samu lafiya dole zai rama azumin da ya sha, idan kuma a lokacin rashin lafiyar tasa ma zai iya azumin ba tare da ya wahala ba to ya wajaba ya yi.
Mace mai ciki wadda azumi yake yi mata wahala saboda rauninta ko nauyin cikinta, ya halatta ta sha, sannan ta rama idan ta samu sarari kafin ta haihu ko idan ta samu tsarki daga jinin nifasi.
Mai shayarwa ko nononta kan yi ƙaranci saboda yin azumin, kuma wannan ƙarancin zai cutar da shayarwar, to ya halatta ta sha sannan ta rama a lokutan da babu wahala ko tawaya.
Matafiyi da tafiyar za ta wahalar da shi idan ya yi azumi, to ya halatta ya sha azumi daga baya sai ya rama a lokacin da ba ya cikin halin tafiya.
Sai dai kuma akwai waɗanda ya wajaba a kansu, amma ba za su iya ba saboda wani babban dalili. To wadannan an halatta musu ciyarwa a maimakon ramuwar azumin. Misali kamar;
Marar lafiya da ba a tsammanin warkewarsa, zai ciyar da miskinai a madadin azumin. Ga kowane miskinai rubu’in Sa’i (Mudu ɗaya) Amma an fi so idan ya haɗa da mahaɗin abincin, kamar nama da mai, ko kayan miya.
Da kuma masu irin cutar Olsa babba wadda ba za a iya yin azumi ba, su ma za su yi ciyarwa a maimakon azumi.
Sai kuma matan da suka kasance cikin ciki da goyo a koyaushe, wato (kwanika) kuma ya kasance saboda wannan wahala ta ciki da goyo ba za su iya yin azumi ba, to su ma za su yi ciyarwa ne a maimakon azumi.
Sai kuma tsohon da ya kasance saboda tsufa ba zai iya yin azumi ba, to shi ma zai yi ciyarwa ne a maimakon azumi.
WALLAHU TA’ALA A’ALAM.