Abu ne sananne addu’a tana da muhimmanci kuma tana da sharuɗa. Ina son sanin su.
Muhimmancin da addu’a take da shi baya misaltuwa ga kowane bawa, domin ita kanta Ibada ce mai zaman kanta, wadda ba’a haɗa Allah da wani acikin aiwatar da ita. Sannan matsayin da addu’a take da shi a cikin ibada kamar matsayin ɓargo ne a cikin ƙashi, wanda idan aka rasa ta to da wahala rayuwar ta yi ƙarko da inganci ga bawa.
Shi ya sa Allah maɗaukakin Sarki ya ƙarfafa mana guiwa ta hanyar yi mana alƙawarin amsa addu’ar a cikin littafinsa mai tsarki, inda ya ce “Kuma Ubangijinku ya ce ku roƙe ni zan amsa musu, sannan duk wanda ya yi girman kai a cikin bautata, da sannu zai shiga wutar jahannama yana ƙasƙantacce.”
Wannan aya ɗauke take da umurni na ayi addu’a, sannan albishir ne na amsawar addu’ar, daga ƙarshe kuma gargaɗi ne ga wanda ya wofintar da addu’ar, domin Kalamar “Bauta”, da ta zo a cikin ayar tana nufin addu’a. Don haka yin addu’a wajibi ne ga kowane bawa mai son tsira a rayuwarshi ta duniya da lahira.
Sannan a cikin ƙarfafa mana guiwar yin Addu’a Allah maɗaukakin Sarki ya cigaba da cewa a cikin littafinsa mai tsarki “Idan bayina suka tambaye ka, ka ce musu ina kusa, kuma ina amsa roƙon mai roƙo idan ya roƙe ni, don haka su yi imani da da ni inbiya masu buƙatun da suka roƙe ni.”
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kuma ya ce “Lallai Allah Rayayye mai girma da ɗaukaka yana jin kunya bawansa ya ɗaga hannu ya roƙe shi, kuma bawan ya dawo da hannunsa ba tare da an amsa mashi ba.”
Wannan Aya da kuma Hadisi suna ƙara nuna mana muhimmancin addu’a, da kuma yadda ya kamata mu yi ta da Ikhlasin cewa Allah ne kaɗai ake roƙo, kuma wurinshi kaɗai ake neman biyan buƙatu, inda Shi kuma ya yi alƙawarin amsa mana.
Sannan Addu’a na da sharuɗɗa ko ladubba kamar haka:
Kada a roƙi kowa idan ba Allah ba, duk lokacin da ka tashi yin addu’a ka kaɗaita addu’ar a wurin Allah, domin shi ne kaɗai mai biyan buƙatu.
Yaƙini da cewa Allah ne mai biyan buƙatun da aka roƙe shi, da ma wanda ba a roƙe shi ba.
Fara yin addu’ar da godiya ga Allah da tsarkake shi, da kuma yin salati ga Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
Naci a cikin addu’ar, duk lokacin da mutum ya so biyan wata buƙata a wurin Allah, toh ya nace sosai, har sai ya samu biyan buƙatar ko kuma madadinta a wurin Allah.
Sannan ba wai buƙatun duniya kaɗai ba, hada na lahira, kullum idan mutum ya tashi yin addu’a ya haɗa da buƙatun lahira, domin can ne ma dawwama. Kuma ya riƙa sanya iyayensa, da sauran duk mai haƙƙi a kansa na musulmai, wannan zai sa addu’arsa saurin karɓuwa a wurin Allah, domin duk Alkhairin da ka roƙa ma wani, toh kamar kanka ka roƙa mawa.
Waɗannan na daga cikin sharuddan addu’a, duk da akwai wasu, da fatan Allah ya karɓi addu’oinmu Amiiiiin.