Tushe na nufin asalin yadda abu ya faro, kamar Mutum, dabba, shuka, labari da sauransu.
Bari mu ɗauki wadancan misalan mu yi sharhi a kansu.
Mutum: idan aka ce tushen mutum, ana nufin Asalin ƙabilarsa, yarensa, addininsa, da kuma su waye mahaifansa, muddin kana son sanin waye mutum, toh wadannan abubuwan da na lissafa zaka bincika, da ka same su, toh ka san cikakken tushensa.
Dabba: Dabba ma ana sanin asalin tushenta, domin su ma akwai nau’ukansu. Misali kaji kaɗai zai tabbatar maka da su ma suna da tushe, tunda akwai kajin Hausa, akwai na turawa, wannan banbancin nasu ne zai bayyana ma mutum asalin tushen su.
Shuka: Idan aka ce tushen shuka, ita kuma nufin matsirarta ko kuma jijiyarta, ma’ana daga inda ta fara tsurowa, kun ga dai a nan ma tushe na nufin asali, kuma daga inda tushen shuka ya samu matsala, toh wannan shuka ta samu matsala.
Labari: Idan aka ce tushen labari, ana nufin asalin samuwar labarin, ma’ana farkonsa ko kuma in ce silarsa.
A takaice dai tushe na nufin asali, ko kuma farkon faruwar wani abu. Sannan ingantuwar kowane abu tana faruwa ne daga ingancin tushensa, haka naƙasar wasu abubuwan tana faruwa ne daga naƙasar tushen abin.
Misali, idan ana neman aure, na daga cikin abin da ake bincike a kansa shi ne asalin mutum, idan an samu iyayensa da Kakanninsa suna da nagarta, toh a kan auri wannan mutum, da an same su da naƙasu kuwa, a kan guje ma wannan mutum, domin asalinsa baya da kyau.
Wani misalin, idan mutum na son kiwo, zaku ga yana neman iri mai kyau, mai asali, domin samun yaɗo na dabbobin mai kyau.
Mu sani, tushe abu ne mai matuƙar muhimmanci ga rayuwarmu, kuma shi ne ginshikin ingantuwarmu, saboda mutane suna girmama tushe ko kuma in ce asali, don haka mu gyara rayuwarmu, ta yadda zuri’armu zasu samu tushe mai kyau.
Jazakumullahu khairan!
Wannan shine cikakken ma’anar kalmarda ake nufi da tushe.
Muna godiya 🙏