MA’ANAR AURE A MUSULUNCI:
Aure shi ne hada wata irin alaka
tsakanin mace da namiji, wannan
yana nufin hade rayuwarsu ta zama
daya; haka nan kuma makomarsu ta
kasance guda daya.
Haka nan kowace irin al’umma akwai irin
matsayin da ta ba wa aure .
Aure a musulunci wani dauri ne da
yake halatta wa ma’aurata. ( mace da
miji ) jin dadi da junansu ta hanyar
saduwa irin ta
Jima’i da sauran mu’amaloli.
Allah ( S.W.T) Ya
halicci mace daga hakarkarin namiji
ya kuma sanya soyayya da tausayi a
tsakaninsu. Kamar yadda ya fada
mana a cikin Alkur’ani mai tsarki.
Wannan yana nuna mana cewa alaka
tsakanin mace da namiji Allah ne ya
kulla ta tun fil azal.
Abin da kuwa Allah Ya hada babu wanda ya isa ya raba shi
Wannan shi ne ya sa a dabi’ance
kowane namiji yana bukatar mace,
haka kuma kowace mace tana bukatar
namiji. Wato kowane daya ba zai iya
wadatuwa da kansa ba, ya rayu shi
kadai, dole sai dai hade da waninsa.
Sannan kuma aure yana tabbata ne idan aka cika sharudda guda shida. Sharuddan kuwa su ne;
1- A samu ma’aurata biyu, namiji da mace, wadanda ya halatta a daura masu aure a shari`ar musulunci.
2- Waliyin mace: Wanda zai bayar da ita.
3- Wakilin ango: Wanda zai karba masa aure ko kuma shi ango da kansa.
4- Akalla shaidu guda biyu wadanda za su yi shaidar aure a tsakanin ma’auratan.
5- Sadaki: Za a iya bayar da shi, ko wani abu daga cikinsa, kafin daurin auren, ko a lokacin da za a daura, ko kuma bayan an daura.
6- Sigar bayarwa da karba. Waliyyin mace ya ce: Ya aurar da ita ga wane. Shi kuma ango ya ce: Ya karba ko kuma wakilinsa ya karba masa a madadinsa.
Sigar daurin aure takan zo da lafazi kamar haka: Na aura maka ko kuma na halatta maka ita. Dukkan wadannan lafazai sun tabbata daga bakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yayin da ya ce da wani daga cikin sahabbai (Alhali yana daura masa aure da wata mata), “Na mallaka maka ita.” Kuma wannan lafazin bai tsaya ga Larabci ba kawai, duk lafazin da zai iya nuna bayarwa da karba ya halatta a yi amfani da shi, ko da wane irin yare ne kuwa. Wannan shi ne abin da Ibn Taimiyya ya fada a cikin fatawarsa. Wannan zancen kuma, shi ne mafi rinjaye a wurin mafi yawan malamai.
Misali a harshen Hausa, za a iya cewa: “Na mallaka maka ita, ko na aura maka ita, ko kuma daga yau ta zama halal a gare ka”. Da sauransu. Haka kuma mai karba zai iya amfani da lafazi kamar haka: Na karba, Na amince ko kuma na yarda da sauran lafuzzan da al’adar gari ta saba amfani da su wadanda suke nuna cewa an mallaka maka ita kuma ka karbi auren. Saboda haka kada a tilasta wa waliyyai (na ango ko na amarya) cewa dole ne su fada da Larabci. Kuma ya kamata a fahimci cewa auren ba zai taba kulluwa ba, face an yi amfani da sigar aurarwa da kuma ta karba.
Akwai tambayoyi guda biyu dangane da waliyyi kamar haka;
TAMBAYA:
Wane ne ya kamata ya zama waliyyin matar da ta musulunta?
AMSA:
Waliyyinta shi ne shugaban Musulmin da take zaune tare da su, ko liman ko na’ibinsa ko waninsu.
Domin ya tabbata a cikin wani hadisi mai tsawo, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana cewa:
…فَالسُّلْطَانُ وَلِىُّ مَنْ لاَ وَلِىَّ لَه.
Ma’ana:
… Shugaba shi ne waliyyin macen da ba ta da waliyyi.
Wannan yana nuna cewa kafiri ba zai taba zama waliyyin mace Musulma ba, ko da kuwa `yarsa ce ko kanwarsa ko `yar’uwarsa.
TAMBAYA
Mene ne hukuncin matar da ta aurar da kanta ba tare da waliyyi ba?
AMSA:
A shari`ar Musulunci mace ba za ta iya aurar da kanta ba, sai dai waliyyinta. Domin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
لاَ نِكَاحَ إِلاَّ بِوَلِى
Ma’ana:
Aure ba ya tabbata sai da Waliyyi…
Waliyyi a nan shi ne mahaifinta, ko kane ko wan mahaifinta, ko kaninta namiji, ko yayanta namiji, ko kuma `ya`ya mazan da ta haifa da sauransu. Kuma hadisi ya tabbata, Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
أيما امرأة نكحت بغير إذن وليها فنكاحها باطل فنكاحها باطل فنكاحها باطل…
Ma’ana:
Duk macen da ta yi aure ba tare da izinin waliyyinta ba, to, auren ta batacce ne, auren ta batacce ne, auren ta batacce ne (ya fadi haka har sau uku)…
A wani hadisin kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce:
لا تزوج المرأة المرأة . ولا تزوج المرأة نفسها…
Ma’ana:
Mace ba ta aurar da mace kuma mace ba ta aurar da kanta…
Wannan hadisin yana nuna mana cewa mace ba za ta zama waliyyiyar wata ba, ko da `yarta ce ko kanwarta ko `yar’uwarta. Haka kuma ba za ta aurar da kanta ba.
Bayan tabbatuwar aure akwai wasu hakkoki da suka wajaba a kan miji da mata wadanda dole ne dukkansu su kula da wadannan hakkoki.
Miji yana da hakkoki a kan matarsa,
wadanda ya wajaba ta kiyaye da su,
kuma ta sauke nauyinsu, Allah
Madaukakin Sarki ya ce :
“Su ma (mata) suna da
kwatankwancin abin da yake kansu
da adalci, maza kuma suna daraja a
kansu, Allah Mabuwayi ne Mai
Hikima”. (Al-baqara : 228).
Imam Ibnu Kasir – Allah Ya jikansa
da rahama – ya ce :
“Fadin Allah cewa “Su ma (mata)
suna da kwatankwacin abin da yake
kansu da adalci” ma’ana su ma
(mata suna da hakki a kan maza, irin
hakkin da maza suke da shi a kansu,
don haka kowa ya ba wa dan’uwansa
hakkinsa da adalci.”
Hakkokin miji a kan matarsa suna da
yawa, kuma suna da girma, saboda
haka Manzon Allah (S.A.W) yake
cewa :
“Hakika ni da zan umarci wani ya yi
sujjada ga wanin Allah, da na umarci
mace ta yi wa mijinta sujjada. Na
rantse da wanda ran Muhammad
yake hannunsa, mace ba za ta biya
hakkin Ubangijinta ba, har sai ta
bayar da hakkin mijinta, kuma da zai
tambaye ta kanta, alhali tana kan
siddin raqumi da ba za ta hana shi
ba.” Imam Ahmad da Ibnu Majah da
Ibnu Hibban ne suka raiwaito shi.
Daga cikin hakkokin miji a kan
matarsa, wadanda ya wajaba ta
kiyaye su, kuma ta sauke su, akwai :
1- Yi masa biyayya : Musulunci ya
umarci mace ta yi wa mijinta
biyayya cikin abin da bai saba wa
Allah Madaukakin Sarki da Manzon
Allah (S.A.W) ba.
Ya inganta a cikin hadisin Abu
Hurairata (R.A) Manzon Allah (S.A.W)
ya ce:
“Idan Mace ta sallaci biyar dinta, ta
azumci watanta (wato Ramadan) ta
kiyaye farjinta, ta yi wa mijinta
biyayya, za ta shiga Aljannah daga
kofar da taga dama daga cikin
kofofin Aljannah.”
Biyayyar mace ga mijinta wajibi ce,
kuma idan mace ta saba wa mijinta,
ta ki yi masa biyayya, to za ta wayi
gari a cikin fushin Allah, har sai
mijinta ya yarda da ita, ya daina
fushi da ita.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa wata
mata :
“Ki duba, meye matsayinki a wurin
(mijinki), domin shi ne Aljannarki ko
wutarki.” Nisa’i da Hakim da
Dabarani da waninsu suka rawaito
shi.
2- Biya Masa Bukatar Aure : Wajibi
ne a kan mace ta biya wa mijinta
bukatarsa ta aure, ta amsa masa a
duk lokacin da ya bukace ta.
Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Idan mutum ya kira matarsa zuwa
ga shimfidarsa, ba ta zo ba, ya
kwana yana mai fushi da ita, to
Mala’iku za su la’ance ta, har sai ta
wayi gari.” Bukhari da Muslim ne
suka rawaito.
Sai dai ba ya halatta mace ta yi wa
mijinta biyayya wajen kwanciyar
aure in tana tare da wani uzuri da
shari’a ta yarda da shi, kamar idan
tana cikin jinin al’ada ko biki, ko
kuma ida tana azumin farilla, ko idan
ya neme ta dubura, ko yayin da take
cikin aikin hajji ko umara, da
sauransu, saboda yarda da haka
saba wa Allah Madaukakin Sarki ne,
kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce,
“Babu da’a ga wanin abin halitta
cikin saba wa mahalicci”.
Hakkokin mace a kan mijinta:
Wadannan hakkokin kiyaye su shi ne kashin-bayan tabbatuwar aure da ni’imarsa, rashin kiyaye su kuwa babbar matsala ce. Ga hakkokin kamar haka:
1- Samar mata da wurin zaman da ya dace don kare mutuncinta, kamar yadda Allah (SWT) Ya ce: “Ku zaunar da su a inda kuke zaune gwargwadon samunku” (dalak 6).
2- Dole ne ya sama mata abinci gwargwadon karfinsa, kamar yadda Allah (SWT) Ya ce: “Mai wadata ya ciyar daga wadatarsa, wanda kuma aka kuntata masa arzikinsa, to ya ciyar daga abin da Allah Ya ba shi” (dalak 7).
3- Ya tufatar da ita a lokacin da ya dace, gwargwadon halinsa, Manzon Allah SAW ya ce: “Ka tufatar da ita, idan ka tufatar da kanka.” (Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850).
4- Biya mata bukatarta ta ‘ya mace wannan dole ne, gwargwadon yadda Allah (SWT) Ya halicce su, haka zai taimaka wajen tsare mata mutuncinta, kuma hakki ne babba, kamar yadda Manzon Allah (SAW) yake cewa: “Lallai ga iyalinka akwai hakkinta a kanta” (Bukhari 1977, Muslim 1159). Duk wanda yake tare da matarsa, har ya kaurace mata tsawon wata 4 babu saduwa, sai ta yi kararsa wajen magabata, ko ya sake ta, ko ya dawo ya gyara hali, wannan ai cutarwa ce babba.
5- Dole ya karantar da ita yadda za ta bauta wa Allah (SWT), ko dai ya yi da kansa ko ya roki wani, ko ya dauki nauyin hakan. Rashin koya mata addini hadari ne babba, don kusan duk tarbiyyar gidan a hannunsu take, idan ba su san addini ba, ’ya’yansu za su tashi a lalace, sai dai wani ikon Allah. Koya mata addini shi ne kare kai da iyalai daga shiga wuta, kamar yadda Allah Ya yi umurni inda yake cewa: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku tsare kanku da iyalanku daga wutar da makamashinta mutane ne da kuma duwatsu.” (Tahrim 6) Amma koya mata wani ilimi ko sana’a wannan ci gaba ne da samun saukin taimako a rayuwa.
6- Kada ya cutar da ita, da duka, zagi, musgunawa da kaskantarwa, don mace tana da daraja a wajen Allah (SWT), duk abin da ya faru sai a bi dokokin da Allah Ya gindaya, kada a bi son zuciya. Hakuri da danne zuciya suna da muhimmanci a cikin al’amuran duniya, ba ma ana aure kawai ba, don haka abin da bai taka kara ya karya ba, bai kamata ya zama bala’i ba.
Idan mace ta yi laifi har ga Allah, akwai mataki guda 3 kamar haka:-
WA’AZI: Za a yi mata wa’azi na bayanin muhimmancin biyayya da illar saba wa miji ko bala’in saki .
KAURACEWA: Idan wa’azi bai yi ba sai a kaurace mata a wajen kwanciya, a ki kulawa da ita a cikin dakinta, amma dole ne a ba ta abinci don Annabi SAW ya ce: “Kada ka kaurace mata sai a cikin daki.” (Abu Dawud 2142, Ibnu Majah 1850 da Ahmad 4/447).
DUKA: Daga nan kuma sai dukan ladabtarwa, ba mai cutarwa ba, ban da dukan fuska, ban da zagi ko bakaken maganganu, ba kuma a gaban yara ko a waje ba. Idan abu ya faskara kuma sai a je wajen magabata don su warware matsalar. Wadannan matakai 3 Alkur’ani ne ya ambace su. Duba (Suratul Nisa’I, aya ta 34).
Wannan shi ne tsari, daga nan kuma, ko a yi sulhu ko a rabu.
7- Rashin bayyana sirrinta: Haramun ne ya bayyana sirrinta, kamar yadda ita ma aka haramta mata bayyana nasa. Annabi (SAW) ya yi gargadi a kan bayyana sirrin juna, tun da an hadu dole ne kowa ya san asirin kowa.
8- Lallai ne a ba ta izinin fita idan ya zama dole ko ya kama, don zuwa asibiti, makaranta, gidan iyaye ko na ‘yan uwa, da sharadin rashin aukuwar fitina, idan akwai matsala sai a dauki matakin gyarawa.
9- Dole ne ya yi wa matarsa kyakkyawan zato, ban da tuhuma, zargi da dari-dari, idan har akwai shakku to sai ya dauki matakin gyara a zahirance ba a munafurce ba. Allah (SWT) Ya ce: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku nisanci da yawa daga zato, lallai wani sashin zato laifi ne, kada ku yi leken asiri…” (Hujrat 12).
Shi ya sa Manzon Allah ya ce: “Idan mutum ya yi tafiya kada ya dawo gida da daddare kwatsam, ba tare da ya sanar da iyalansa ba.” (Bukhari 5244).
Kuma idan mijin mace ba ya nan, idan ya kama a shiga wurinta, to duk wanda zai shiga kada ya je shi kadai, ya nemi wani muharraminta, ko wasu mata, don kauce wa mummunan zargi.