Shin sakacin iyaye ne ke janyo shaye-shaye ko rashin aikin yi?
Farkon abinda ke kawo shaye-shaye a tsakanin matasa a wannan zamanin yana tasiri ne ta hanyar zama da mutane masu ɗabi’u daban-daban, zamantakewa, muhalli, da talauci. Wasu dalilai na yau da kullun da yasa matasa na iya fara shan sigari ko wiwi sun haɗa da,
1. Tasirin ’yan’uwa
Matsi na ’yan’uwa na sa yaro sha’awar shiga cikin jama’ar da ke shaye-shaye, hakan na iya taka muhimmiyar rawa wajen sa yaro shan taba ko wiwi a tsakanin matasa. Ganin abokai, abokan karatu, ko ’yan’uwa suna shan sigari na iya daidaita ɗabi’ar yaro da tasu ya sa masa sha’awar shaye-shsye shima.
2. Rayuwar ko in kula a zamantakewa da abubuwan al’adu,
Halayen al’umma game da shan shaye-shaye, al’adu, da hotunan shaye-shsye a kafofin watsa labaru na iya yin tasiri ga tunanin matasa game da shaye-shaye a matsayin al’ada ko dabi’a. Kallon shaye-shaye a cikin fina-finai, nunin talbijin, bidiyon rawa wato (music), da tallace-tallace na iya ɗaukaka shaye-shsye kuma ya sa ya zama kamar abin burge wa ga matasa.
3. Hanyoyin magance damuwa
Wasu matasan na iya komawa shaye-shaye a matsayin hanyar magance damuwa, tsarguwa, rikice-rikice na tsara, matsin karatu, ko ƙalubalen yawan tunani. Wasu na ganin shaye-shsye a matsayin nau’i na magani ko samun annashuwa, yana ba da taimako na wucin gadi daga yawan tunani ko al’amuran lafiyar kwakwalwa.
4. Sha’awar fara gwada shaye-shaye
Matasa na iya sha’awar shaye-shaye da sha’awar sanin abubuwan da ke tattare da shaye-shaye (misali, ɗanɗano, kamshi, da sha’awar busa ta), ko kuma ya motsa su ta hanyar sha’awar su watsar da sanin illar ta su yi amfani da son zuciyar su. Gwaji akan yarda taba ko wiwi take, na iya haifar da jarabar shanta akai-akai.
5. Yanayin gidan da aka taso
Halin shaye-shaye na ’yan uwa, iyaye, ko masu kula da su na iya ba da gudummawa ga yuwuwar shaye-shaye ga matasa. Yaran da suka girma a gidajen da ake yawan shaye-shaye na iya yuwuwa su fara shaye-shaye da kansu saboda sun taso sun ga ana sha a gabansu, shaye-shaye zai zame musu wani abu ne mai muhimmanci ba mai illa ba,domin duk abinda yaro ya taso ya gani anayi a gidan su shi yake ɗauka.
6. Samun dama da sauƙin samun samun kayan shaye-shaye a kusa
Sauƙin samun sigari ko wiwi, samfuran taba, ta hanyar shagunan sayar da kayayyaki, injinan siyarwa, tallace-tallacen kan layi, da hanyoyin zamantakewa na iya sauƙaƙe wa matasa samun ta cikin sauki da ci gaba da shan ta. Rashin ƙayyadaddun shekaru, aiwatar da manufofin sarrafa taba, da sa ido kan tallace-tallace ga ƙananan yara na iya ba da gudummawa ga shan taba ga matasa.
7. Dabarun kasuwanci da tallace-tallace
Kamfanonin taba ko wiwi sukan kai hari ga matasa ta hanyar kamfen tallan tallace-tallace, marufi kala-kala, ɗanɗano mai ban sha’awa, da sako shahararrun jarumai wajen yin tallar sa don jawo sabbin abokan cinikayya. Dabarun talla ga matasa na iya haifar da hasashe cewa shan taba bashi da illa, gayanci ne, jarumta ce ko kuma abin sha’awa ne a cikin al’umma, yana haifar da ƙarin yawan matasa wajen fara shaye-shaye a tsakanin matasa.
Hana shaye-shaye ga matasa yana buƙatar cikakkiyar hanyar da za ta magance ta ta waɗannan abubuwan da ke da tushe ta hanyar shigar da shaida, kamar aiwatar da manufofin sarrafa taba ko wiwi, haɓaka yaƙin hana shaye-shaye na jama’a, haɓaka wuraren da babu hayaki, ba da shirye-shiryen daina shan taba ko wiwi, da shigar da matasa cikin ƙoƙarin bayar da shawarwari. Ta hanyar ɗaukaka manyan matakan tasiri da yawa da kuma bayar da tallafi ga matasan ta hanar da ya dace, al’ummomi da masu ruwa da tsaki na iya kawo hanyoyi ko sharuɗan da da ke hana matasa shaye-shaye da inganta halaye masu kyau a tsakanin matasa.