Wasu irin illoli ne ke farwa soyayya yayin da ƙarya ta shiga tsakanin masoya biyu?
Hauwasa suka ce “Ƙarya fure take, amma bata ƴaƴa”, duk kuwa iccen da aka ce baya ƴa’ƴa toh amfaninsa kaɗan ne. Hakan na nufin ƙarya ko da tana da amfani a soyayya, toh amfanin kaɗan ne, bare kuma bata da wata rana, sai ma manyan illoli da take haifar wa.
Sai dai kafin mu je ga illolin, bari mu je ga abubuwan da suke haifar da ita kanta ƙaryar a cikin soyayya.
Abu na farko, kuma ja gaba shi ne SO, duk wanda kake so, kuma kake gudun samun matsala a tare da soyayyarshi, toh akwai yiyuwar ƙarya ta shigo, wadda zata zama garkuwa ga wannan soyayyar, domin kada ta samu illah, sai dai wannan ba zai zama hujja ba da zata sa a riƙa yin ƙarya.
Abu na biyu kuma shi ne, kwaɗayi, kowa ya sani muna cikin zamanin da idanun mutane ya rufe a kan son abun duniya, har ta kai ga mai kuɗi ko wata nasaba shi ne wanda kowa ya fi so, idan mutum bai aje komai ba, toh da wahala ya samu karɓuwa a wurin wanda ya gani yana so, shi ya sa mutane ke tsirar ƙarya domin samun shiga a wurin masoyansu, wanda wannan ma illah ce gare su.
Sai kuma raunin mace, na ɗaya daga cikin abin da ke kawo ƙarya a soyayya, domin lokuta da dama idan aka bayyana ma mace wata gaskiyar, toh kamar an kawo karshen soyayya ko kuma tarayya da ita, shi ya sa wasu mazan suke rufe wata gaskiyar domin cimma manufarsu ta soyayya.
A iya fahimtata waɗannan su ne silar da ake yin ƙarya a soyayya, sai dai na san ba su kenan ba, wani zai iya kawo wasu dalilan na daban.
Batun illah kuwa, zan ƙara koma wa maganar Hausawa a batun ƙarya, inda suka ce “Ramin ƙarya ƙurararre ne”, tabbas duk abin da aka ƙure, toh ƙarshensa ya zo, kenan duk soyayyar da aka gina a kan ƙarya, to karshen ta ya zo yayin da aka gane wannan ƙaryar, idan kuma har ta ɗore, toh da wahala idan bata samu rauni ba, don haka ribar ƙarya a soyayya kaɗan ce, amfanin ta, tamkar amfanin romo ne a zunubi, kawai mutum ya je a yadda yake, da kuma zuciya ɗaya, idan wani ya ƙi ka saboda gaskiyarka, wani na can irin wannan gaskiyar taka yake nema!
Madalla