Marayu bayin Allah da ya kamata a tausaya mawa, saboda sun yi rashin iyayen da ya zame ma wajibi su jiɓinsu lamarinsu, don haka idan har ba a taimaka musu ba, toh kuma bai kamata a ci musu dukiya ba.
Shi ya sa Allah Subhanahu wata’ala ya tsawatar mana, tare da yin mummunar bushara ga wanda yake cin dukiyar Marayu.
A cikin Alkur’ani mai girma, Allah Subhanahu wata’ala ya ce “Kada ku kusanci dukiyar marayu, sai ga wanda yake kyakkyawa…”, ma’ana kada a taɓa dukiyar marayu sai da wani ƙwaƙƙwaran dalili, wanda Shari’a ta yarda da shi, kamar rashin lafiya, hidimar makaranta, ko abinci, da sauransu, wannan ma sai idan marayan ne za a yi ma amfani da su, ko kuma fita haƙƙin masu kula da dukiyar marayan, ko kuma za a fitar da zakka.
Sannan Allah Maɗaukakin Sarki ya ce “Lallai waɗanda ke cikin dukiyar marayu da zalunci, lallai ne suna ci ma cikinsu wuta, kuma da sannu zasu shiga wutar sa’ira”
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ma ya gargaɗe mu da cin dukiyar marayu, inda ya lissafa wasu manyan zunubai masu halakarwa guda bakwai, a ciki sai da ya sako cin dukiyar marayu.
Don haka cin dukiyar marayu zunubi ne mai girman gaske, wanda ya kamata dukkanmu mu nisanta. Sannan wannan na nuna mana halaccin taimakon marayun, domin duk abin da aka gargaɗe ka akan ɓata shi, toh da za ka kula da shi, haƙiƙa zaka samu sakamako mai kyau.
Don haka mu kula da marayu, don wasu basu ma da dukiyar da har wani zai ci, yin hakan akwai kyakkyawan sakamako a wurin Allah.
Allah ya bamu ikon kiyayewa Amiiiiin .