BAMBANCI TSAKANIN SO DA ƘAUNA.
Bambancin da yake tsakanin so da ƙauna a bayyane yake, sau da yawa mukan yi kuskuren haɗa so da ƙauna a ma’auni ko sikeli ɗaya, sai dai hakan ba daidai ba ne domin kuwa akwai tazara mai nisan zango a tsakanin su ta yadda ɗaya ya ɗaramma ɗaya da nagarta ta ƙololuwa.
DANGANE DA SO:
Shi so a zuciya yake! Ita kuma zuciya kamar yadda muka sani an halicce ta ne da son mai kyautata mata da kuma ƙin mai munana mata, kenan dai idan mutum yana son wani da zarar ya munana masa zai iya daina son shi. Haka nan; ana iya son wani saboda wani abu da yake da shi ko ake sha’awarsa saboda yana da shi, kamar kyau ko wani abu da ya danganci haka, to da zarar wannan abu da ake so saboda sha’awa ya gushe ko kuma kyawun shi kenan sai son ya gushe. Ko kuma budurwa ta so saurayi saboda yana da kuɗi, to da zarar ya talauce shi kenan za ta daina son shi.
DANGANE DA ƘAUNA:
Ƙauna saɓanin so ce! Ba ta gushewa ko misƙala zarratin, domin ita a cikin jini da rai take yawo ba a zuciya ba, babu yaudara a cikin ƙauna kwata-kwata. Shi ya sa za a ga iyaye ba sa taɓa daina ƙaunar ‘ya’yansu ko da kuwa suna aikata wani abu na rashin kyautawa to ƙaunar nan ba za ta gushe ba, saboda hannunka ba ya ruɓewa ka yanke ka yar. Haka nan; ko a tsakanin miji da mata idan har ƙaunar da suke yi wa juna ta rinjayi so to ana samun zaman lafiya dawwamamme a tsakanin su, saboda uzuri yana ɗamfare da ƙauna. Shi ya sa ban yarda da karin maganar da ke cewa SO HANA GANIN LAIFI ba, sai dai a ce ƘAUNA HANA GANIN LAIFI. Saboda a bayyane yake ƙauna tana da rinjaye fiye da so ta kowane fanni.
Madalla. Sannu da ƙoƙari. Mun gode sosai da wannan amsa taki.