Banbancin da ke tsakanin so da ƙauna ba wani mai yawa bane, sai dai kuma banbanci ne mai matuƙar tasirin da mafi rinjayen mutane suka gamsu da shi, banbancin ga shi kamar haka:
So, yana da takaitaccen lokacin da yake kaiwa, duk kuwa da yadda ya kai ga ƙarfi, da zaran lokacinsa ya yi za a iya neman sa a rasa, bisa wani dalili mai ƙarfi ko marar ƙarfi da ya faru, shi ya sa har a hausa aka ce “So tsuntsu ne”, duk kuwa abin da aka siffanta shi da tsuntsu toh an san ba maganar zama a wuri ɗaya, zai sauka a inda ya yi masa daɗi ne, sannan idan ya gaji da wurin, ko wani dalili na daban na iya sanya shi ya chanja muhalli, duk kuwa da ana cewa “So hana ganin laifi.”
Ƙauna: ita kuma ƙauna wani abu ce dake zaman dindindin a muhallin da ta sauka, duk wuya ko rintsi bata chanja muhallin da aka santa, har sai idan an mata tilas ko abin ya fi ƙarfin haƙurinta, saboda ita ana yinta ne har ƙarshen rayuwa, don haka ta fi so ƙarko. Duk da ita ma akan yi kuskure wurin yinta, don an sha samun mutum ya ƙaunaci abin da bai kamata ba, wanda daga ƙarshe ya yi ta wahala a kansa.
Don haka, banbancin da ke tsakanin so da ƙauna shi ne: So yana da lokaci, ƙauna kuma bata yankewa. Sannan ta wani ɓangaren, ƙauna tana farawa ne daga soyayya, sai ka fara son abu ne kafin ka ƙaunace shi, suna tafiya ne a tare, sai dai kuma shi so yana taka rawar sa shi kaɗai, anan ne kuma yake da raunin gaske.
Shi ya sa gwara ka samu mai ƙaunar ka, shi ne wanda zai iya jure duk wata wauta taka, saboda baya son rabuwa da kai, wanda yake maka so kaɗai kuwa, wata rana za a iya ganinku a rana.
Madalla.