Faɗa mana;Mene ne bambanci tsakanin auren budurwa da na bazawara?
Banbancin da ke tsakanin auren budurwa da bazawara yana da yawa, sai dai kafin mu je gare su dole sai mun san wacece budurwa, sannan wacece bazawara, ta haka ne zamu fahimci banbancin da ke tsakanin su.
Budurwa: ita ce macen da bata taɓa aure ba, ko kuma bata taɓa sanin wanene namiji ba duk kuwa tsawon shekarunta.
Bazawara: ita ce wadda ta taɓa aure, daga baya auren ya rabu, ko ta hanyar saki, ko kuma ta hanyar mutuwar miji.
Da wannan ne zamu iya fahimtar bambancin da ke tsakaninsu. Wannan bambanci kuwa ya fi yin tasiri matuƙa yayin da aka zo aurensu, tasirin kuwa a al’adance da kuma addininan ce:
A addinance idan budurwa ta isa aure, toh mahaifanta na da ikon zaɓa mata wanda ya dace ta aura, bazawara kuwa addini ya bata damar ta zaɓar ma kanta miji. Sannan idan mai mata ne ya auri budurwa, toh addini ya ba shi damar ya yi kwana bakwai a ɗakinta kafin ya koma ma ɗayar matarsa, bazawara kuwa kwana uku ne addini ya ce a yi a ɗakinta, kun ga anan banbanci ya fito ƙarara a tsakanin budurwa da bazawara a addinance.
A al’adance kuwa a wurin hidimar aure ba a cika kauɗi idan bazawara zata yi aure kamar yadda ake kauɗi idan budurwa zata yi aure ba, wata bazawarar ma ba kowa zai san ta yi aure ba, amma budurwa duk mai haƙƙi sai ya ji labarin zata yi aure, ko kuɗin da ake kashe ma budurwa, ba a cika kashe ma bazawara ba, sai idan ta taki sa’ar gaske.
Sai dai a wurin buɗewar idon zaman gidan aure, bazawara ta fi budurwa, saboda ita ta taɓa yi, ta san daɗi da rashin daɗinsa, saɓanin budurwa da ita kallo ɗaya take yi ma aure, sai ta je ta ga saɓanin haka.
Daga karshe kuma kowace akwai falalar da take da ita in dai an yi sa’a da ta gari ce. Sai mu yi fatan Allah ya sa mu zama cikin bayinsa na gari Amiiiiin.
Madalallah Da wannan ƙayatacciyar amsa.