Kawo bambance-bambancen da ke tsakanin waɗannan ƙungiyoyin addini.
Kungiyoyin Izala, Ɗariƙa da kuma shi’a sun yi matuƙar tasirin a Nigeria, kusan zan iya cewa sun ne kungiyoyin da suke jan ragamar musulman Nigeria, har ma da wasu maƙwabtan ƙasashe na yankin Afirica.
Kuma dukkan waɗannan kungiyoyi suna tafiya ne karkashin kalma guda ɗaya, wadda dukkan musulmi ya ke riƙo da ita, domin sai da ita ne musulunci ya ke tabbata, wato (Kalmar Shahada)
Sai dai akwai abubuwan da suka bambanta waɗannan kungiyoyi, wanda da an ga mutum za a iya gane shi ɗan Izala ne, ko ɗan Ɗariƙa ko ɗan shi’a:
1. Izala: ƙungiya ce mai rajin tsayuwa a kan koyarwar Alkur’ani da kuma Sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ba tare da ragi ko ƙari ba a cikin addini, sannan wannan ƙungiya tana rajin yaƙar duk wani sabon abu da za a ƙirƙira a cikin addini, wanda Manzon Allah bai yi ba, sannan Sahabbansa basu yi ba, shi ya sa ma aka kira kungiyar da Izalatul bidi’a wa iƙamatu Ssunah, ma’ana, za a yaƙi bidi’a, sannan za a tsaida Sunnah.
Bidi’a a wurin Ɗan izala ta haɗa da Maulidi, wazifa, taron suna d.s.
Sannan Salatil Fatihi, shi ma a wurin ɗan izala duk bidi’a ne, saboda ba shi ne Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar ba, wanda ya koyar shi ne Salatil Ibrahimiyya da wasunsu.
Akwai ire-iren waɗansu sababbin abubuwa da suka zama addini, amma Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama bai aikata su ba, kuma bai gani an aikata su ba ya ƙyale, toh irin waɗannan duk bidi’a ce a wurin ɗan izala, kuma shirye yake da ya ga an kawar da su a cikin addini, tare da tsayuwa a kan koyarwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.
2. Ɗariƙa: Kungiya ce mai matukar girman gaske a cikin kungiyoyin addinin Musulunci, sannan manufarsu ita ce bin koyarwar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, tare da nuna tsantsar ƙaunarsu ga Manzon Allah, da kuma Salihan bayi. Hakan ne ya sa kungiyar ɗariƙa take yin Maulidin Manzon Allah, da na wasu Shehunnan ma, domin nuna tsantsar ƙaunarsu a gare su, sannan a wurinsu wannan ba laifi bane, asali ma kamar wani aiki ne na lada, saɓanin yadda Izala take kallon Maulidi a matsayin ƙirƙirarre a cikin addini.
3. Shi’a: kusan tafiyarsu ɗaya da ɗariƙa, saboda suna yin kusan duk abin da ɗariƙa ke yi, kawai banbancinsu shi ne, su kuma sun fifita soyayyarsu ga Alhalul Baiti, wato iyalan gidan Manzon Allah, da suka haɗa da ƴaƴansa da jikokinsa. Sannan suka tsananta ƙiyayyarsu ga wasu daga cikin Sahabbai, a ganinsu sun zalunci Ahalin gidan Manzon Allah, kamar su Nana A’isha, da Sayyiduna Abubakar da Umar, wanda ko kaɗan ba sa son su, saboda wata fahimta tasu ta daban.
Sayyiduna Ali, shi ne wanda suka fi so shi da Matarsa Nana Faɗima R.A, sai ƴaƴansu kamar su Hassan da Hussaini.
Sannan ba wai a manufa ba, hatta a siffa ta zahiri waɗannan kungiyoyi suna da banbanci, ɗan izala yana ɗage wando, yayin da ɗan ɗariƙa yana yawan riƙe charbi, shi kuma ɗan shi’a a tufafinsa ma za a iya gane shi, domin sun fi sanya baƙaken kaya mazansu da matansu.
Wannan shi ne kaɗan daga cikin bambancin da ke tsakanin waɗannan kungiyoyi.
Madalla